Sashe 49
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yi ta nufi part ɗinta, bayan ta shiga ta nufi toilet tare da yin wanka ta ɗaura alwala wata jallabiya ruwan toka ta saka mai yafin farin duwarwatsu bayan ta idar da sallar Asr tayi azkar idanunta rufe ta shiga tilawar Alkur'ani ta yi hakan ne sbd rashin abin yi kuma bata son yin baccin Asr, tana nan zaune Mami ta murɗa handle ɗin bedroom ɗin Majeederh ta shigo daga tsaye ta ce "Zaki mana dinner" A sanyaye Majeederh ta ce "Mami kai na ciwo yake, tunda na dawo ban yi bacci ba, can ma ba bacci nake ba" Mami ta saki ƙofar ta shigo tare da zama saman gado ta kalli Majeederh ta ce "Kenan Raihana ko Ruma zan kira daga gidan mazajen su suyi mana ko?" "Sun tafi ne?" Cewar Majeederh, Mami ta ce "Da ke zasu tsaya su taya zaman gida bayan su Allah yaye musu wannan ƙaddarar? Majeederh shekarunki nawa yanzu ne?" Kanta a ƙasa zuciyarta na bugawa ta ce "28" Mami ta ce "To da kyau tunda har kina lissafe, Sahar a gabanki aka haifeta yanzu yaranta huɗu cif, Widad a gabanki aka haifeta haihuwa ta uku ta biyu za tayi a hakan ma don Allah bai bata da wuri bane, Raihana, Ruma duk akan idanunki aka haife su ita Ruma cikin ne baya zama, ita Raihana Allah ne bai bata ba, duk wannan ba zai sanya kiwa kanki karatun tanatsu ba Hawwa'u? Me kike nema a duniya, kina da kyau, kina da iliminki, kina da kuɗi mene ya yi saura?" Majeederh ta kalli Mami jin ta ce tana da kuɗi, bayan ko ƙwandala bata da shi da sunan mallakinta, komai data mallaka a Misira ta sallamawa Abbu. Mami ta gyara zama ta ce "To na fara gajiya nikam, gashi nan jama'ar gari sun fara zagina da ƙana nan gulmace-gulmace akan wai an tura ki neman kuɗi ba wani karatu da kike, wasu ma cewa suke neman maza kike gashi nan baki aure ba, kuma bama ta kuraki akan aure kina neman tsofe mana a gida" Tunda ta fara magana Majeederh ta kafe Mami da manyan idanunta wanda gefe ɗaya ya yi ja sbd ciwo Kallon nata kawai take amma tunaninta yana wani waje guda, kalmar neman maza ta girgiza Majeederh ta kasa fahimtar wake neman mazan? "Kina jina?" "Wake neman maza?" Majeederh ta faɗa muryarta na rawa Mami ta bata amsa da "Ke mana, kuma dai bani da shaida akan ki ɗana ne ka haifa baka haifi halinsa ba, tunda gashi sam baki damu da rashin auren naki ba" Kalma “Zina†babbar kalma ce wacce a duniya ta tsaneta balle mai aikata yinta amma ita ake ƙoƙarin laƙabawa wannan muguwar kalmar? Bayan data aikata zini gwara ta kashe kanta kawai ta huta, da zina zatai ko yawan bin maza ai tun kafin tabar ƙasar zata fara sbd abinda ke damunta, sai yanzu ne da Allah ya ye mata dukkan wani abu da take ji zata fara zina? Bayan shi isn't interested at all! Ɗigon sha'awa yanzu babu a tare da ita, ta wannan ɓangaren har mancewa take ita ɗiya macace?... Kai ta ɗago ta ce "Allah ne shaidata" "To Allah ya rufa asiri, kin tabbatar kafin shekarar nan ta ƙare kin kawo mijin aure, idan ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci kinfiso muna jerawa a gida muna haɗa kafaɗa? Kuma daga yau duk wani aiki na gidan nan ke zaki nama sallami ƴar aiki, Aaliyah makaranta take zuwa" Tana faɗin hakan ta miƙe tare da ficewa daga ɗakin tana zuba kumfar baki... Majeederh ta bi bayanta da kallo, to ita yanzu za ta yi da ranta? Tallan kanta za tayi kenan? Ko kuma dai photo nanta zata raba masallatai? Wata zuriyar ta ce mata. "Kin manta kenan ko Majeederh? Bayan mazan gudunki suke babu wani wanda zai ce yana son ki balle aure" Zuciyarta tayi mata nauyi da ƙyar ta samu ta ja numfashi kafin ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi part ɗin Abbu. Yana zaune saman ladduma gabansa cike da kayan marmari hannunsa riƙe da jarida ya dubawa ta yi sallama, bai amsa ba sai gyaran murya da ya yi mata alamar ta shiga. Ta zauna a gefe cike da tsoransa ta ce "Ina yini Abbu? Na sameka lafiya?" Ya ce "Lafiya lou" Ya yi shiru ta ɗan ɗago kanta ta saci kallon Mahaifin nata, ba zaka ce shi ne ya haifeta ba, sbd ya samu duniya da abinda yake so wato kuɗi jikinsa ya murje alamun kwanciyar hankali sun bayyana a tare da shi. Ta sauke ajjiyar zuciya a hankali ta furta "Allhamdulillah na cika burin Abbu" Ta ɗauka zai tambayeta kalar rayuwar da tayi a Egypt ba tare da iyaye ko wani nata ba, ta ɗaukan zai sanya mata albarka bisa namijin ƙoƙarin da tayi na zama Gwarzuwa a musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa, ta ɗauka zai albarkaci rayuwarta bisa burinsa data cika sai ta ji ya ce "Na haifi ƴar da bata san girma da ƙimata ba, na haifi ƴar da take son tuna mini asiri a cikin al'umma, na haifi ƴar da take son saka mini ciwon zuciya...," A gigice Majeederh ta dakatar da Abbu da faɗin "Me na yi Abbu, me aka ce nayi idan zuwa gidan Latifa ya ɓata ranka don Allah ka yafe mini" Jikinta duka rawa da ɓari yake sbd tsoran ɓacin ran mahaifin nata. Abbu ya dubeta sosai kana ya jawo laptop ɗinsa ya shiga Gmail ya nuna mata wani saƙo ya ce "Hukumar makarantarku ta ƙasar Egypt take ƙorafin sun nemi alfarmar ki zauna musu domin zama malama amma ki kaƙi bayan sun yaba miki ba za su samu wata ɗaliba data kai ki ba" Majeederh ta ce "Ka yi haƙuri Abbu" Ya ɗaga mata hannu cikin tsawa ya ce "Haƙuri? Kin manta al'ƙawarinmu dake?" Ta ce "Ban manta ba" Cikin zafin rai ya ce "Ok isa ce ban ba? Anya zaki albarka kowa Majeederh? Kina son wanyewa lafiya?" A ruɗe ta ce "Ka yi haƙuri Abbu, rayuwata a wata ƙasar da bani da kowa akwai hatsari ba zan iya zama ba, na yi ƙoƙarin cika al'ƙawarin amma na kasa ka yafe mini, bana da kowa a Misira bana da mai mini faɗa, bana da wanda zai kalla a matsayin wani nawa, bana da wanda zan zauna nayi fira da shi" Abbu ya dinga kallon Majeederh cikin tarin tsana da ƙonar rai ya ce "Shi ɗan uwanki Alpha ba mutum bane? Da yake tafiya cikin jeji sai ya yi shekara bamu sa shi a idanun ba, ba kuma mu san halin da yake ciki ba, gwara ke mun san inda kike...," Ta ce "Abbu taya zaka haɗa ɗiyarka mace da namiji? Namijin daya kusa tun karar shekaru arba'in? Kuma zai iya kula da kansa?" Ta ƙare maganar tana sakin kuka sosai. Abbu ya ce "Ok ke yarinyar goye ce kenan ba zaki iya kula da kanki ba? Kinga tashi maza ki bar mini parlour idan na ci-gaba da ganinki zuciyata bugawa zatai mu zauna mu cinye ƴan kuɗaɗen da suka rage kinga ma dawo gidan jiya talakawa" Zatai magana ya ƙara daka mata tsawa kamar ba Mahaifinta da take mutuwar so kamar rai ba ta miƙe jiki na ƙyarma da ɓari ko kallon gabanta ba tayi ta nufi waje ga idanunta da suke mata wani masifaffan ƙaiƙayi nan da nan sukai jajir ta shiga susawa tana yin main parlour kuka na cin ƙarfinta, karo tayi da mutum tsaye wanda shigowarsa kenan cikin garin Kano tana ƙoƙarin yin compound a tunaninta main parlour ne sbd idanunta rufe yake caraf ya sa hannu ya riƙo nata hannun....