← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 93

Sashe 17

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Uncle Isma'il ya ce "Mene ya ja ra'ayinka? Bayan iyayenka basa su" "Shi ne first and simple way da zai mallaka mini Malumana" Uncle ya girgiza kai ya ce "Ka fara tsarkake niyyarka, ba a taɓa musulunta sbd wani dalili ko neman yardar wani, ka musulunta sbd ka yarda addinin Musulunci shi ne addinin na gaskiya, ka musulunta sbd ka yarda da Allah da Manzonsa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka yarda da su babu abokin tarayya, ka mance littafin injila ka ɗauki Alqur'ani da hannu bibbiyu" "Ta zan yarda?" "Ka fara nutsuwa kasan mene ya sa ka ke son Musuluncin yanzu ka je ka shirya, kuma babu kai babu yiwa Majeederh magana, balle uzzura mata ko kai hannu zuwa jikinta yadda ta ce ka barta ta tsaneka to barta, ka ƙaura cewa ganinta, yanzu ne za ka yi faɗa, fight for your love, ka je bata da bazata, bazata ta sabon sauyin da kayi ka zama tsarkake" Abraham ya yi shiru yana tunanin ta ina zai iya all this, ba zai iya haɗa waje da Majeederh ba tare daya taɓa ta ba. Ya miƙe tare da shigewa bedroom. Babban parlourn a cike yake, Uncle Isma'il, Uncle Bello, Abbu, Mami. Gefe guda kuma Bar Aliyu Sufyan Alhassan ne zaune cikin wani lallausan yadi, Sai Hajia da Papa iyayen Zaki. Daga ɗaya barin Masu garin ne bakiɗaya, Governor Abu-turab Alƙasim da Mama sai Haseenatou wacce ta ƙarasu. Abu-turab cikin wata dakakkiyar shadda fara tas sai ɗaukan Idanu take ɗinkin jamper da babbar riga, he was so looking anger na jin meke faruwa. Daga tsakiya Malama Majeederh ce zaune cikin wata blue black ɗin Abaya mai kyau tayi rolling kanta gefen fuskarta a rufe hannunta riƙe da Khalil. A inda take zaune take jiyo ƙamshin perfume ɗin da har abada ba zata mance ba. Abinda bata sani ba dab da ita Oga Abraham Daniel David ne zaune cikin wani milk ɗin voyel mai manyan zane ana iya hango faffaɗan ƙirjinsa mai ɗauke da zanan tattoo kansa kwance luff yana ƙyalli sai sabga ƙamshin Boadicea The Victorious, idanunsa kafe a kanta babu ko ƙiftawa. Uncle Isma'il ya yi sallama kana yasa aka yi addu'a. Ya gyara zama ya ce. "Bincike da result ya tabbatar Khalil jinin Abraham ne" a kusan tare Governor Abu-turab da Bar Aliyu suka ce.. "Ƙarya yake ɗana ne" Abraham ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Babu me zarar yi ma Jee ciki kaf cikin ku, I'm lucky ni me sa a ne" duk suka kalli Abraham Abbu kuma ji ya yi kamar ya shaƙe yaron. "Ba musu za kuyi nan ba, kuna son rusa mini ƴar fahimtar da nayi, His Excellency, Barrister, Abraham na yarda duk kuna son Majeederh, shawara ɗaya zan baku Majeederh ba budurwa ba ce ƙaddara ta faɗa mata" Zaki ya ce "Zan zauna da ita haka" Uncle ya girgiza kai ya ce "Kuyi faɗa, faɗa na samun soyayyar Majeederh zan ga waye MIJIN MALAMA, zanga mai zarrar sace zuciyarta, Ɗa dai na Abraham ne, ban san ya akayi aka samu cikin ba wanda gabaɗaya yanzu Abraham zai bamu labari anan zamu tabbatar da gaskiyar shi". "Idan tana da burin dawowa gidana to ta ɗauki shegen yaron nan mai gadon tsiya, wanda ya zo da ƙazanta zuwa gidan marayu, kuma ki zaɓi Abu-turab matsayin mijinki shi ne ya dace dake" lokacin guda Majeederh da Abraham da Aliyu suka kalli Abbu banda Abu-turab daya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya. "Abbu gidan marayu, ni na haifeshi ina raye kuma zan kai shi gidan marayu?" "Idan kin yarda ni ne ubanki, ni ke da hakƙin zaɓa miki miji" ta runtse Idanunta zuciyarta na bugawa bata san lokacin da ta ce. "Na amince, na amince Abbu albarkar ka nake nema" idanun Abraham kamar za su faɗo. "You're liar, ki auri wani,ni kuma na ci gaba da tarayya dake kina haifar shegu, ba zan barki ki zauna lafiya da wanda kika aura ba" tayi masa banza. Abbu ya kalli Abu-turab ya ce "Idan ka shirya kawo sadaki yanzu a ɗaura auren ka tafi da matarka" Abu-turab ya ce "A shirye nake Abbu" Majeederh na zaune ta ji an ɗagata cak tare da yin sama da ita har jaririn hannunta kafin kowa ya yunƙura Abraham ya yi waje da Majeederh yana zuwa ya saka key ya buɗe ƙofar mota ya cilla Majeederh ciki idanunsa rufe ƙwaƙwalwar taɓin hankalin na motsawa "Kai Mahaukaci ne?" Ya dubeta yana sunkuyawa dab da ita ya zura mata seat blt ya ɗaurawa kansa. A karo na biyu ta sake cewa "Kai Mahaukaci ne?" Ya buɗe ido ya ce "I don't know, amma yau zan iya bamban cewa ni mahaukaci ne or not? Domin a yau zan ƙara baki wani cikin na kwanta take a karo na biyu, daman wancan i have been drug ban san ya ki ke ba, wannan shi ne aikin hankalina, wanda zan yi na hauka ya fi wannan,zan iya tsayawa tsakiyar titi babbar mota tabi ta kanmu, me, you, and our son duk mu mutu" Majeederh ta runtse Idanunta tasan tabbas zai aikata. Da gudu Bar ya fito Abu-turab na mara masa baya, suna fitowa motar Abraham Daniel David na fice daga cikin gidan da gudu...
Chapter 17 · 0% Book details