← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 93

Sashe 4

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Hospital
A hankali aka buɗe Ƙofar room ɗin tare da mayarda ita aka rufe slowly. Tsaye ya yi a kanta ya zuba mata narkakkun idanunsa ya ɗauki almost 5 minutes yana kallonta kafin ya ɗaga ƙafarsa a hankali zuwa gaban bed ɗin, ya ja kujera tare da zama akai, cikin nutsuwa ya sanya hannu ya ɗauki jaririn dake kwance yana motsi cikin tattausan showel ɗin da aka saka shi. Soyayyar Jaririn ya samu gurbi a zuciyarsa musamman da bai taɓa samun ɗan kansa ba, bai taɓa ganin gudan jininsa ba. "Ohh baby, your Dad is here" ya furta can ƙasa gudun kada ya tashe ta.
"His Dad?" Ta furta cikin magagin barcin dake É—aukarta domin allurar bai gama sarkinta ba.
Ya ɗago kai da sauri ya kalleta ba ƙaramin harbawa zuciyarsa tayi ba, this is the first time da yaga fuskarta babu liƙab iya tsayin shekarun daya santa.
Kasa magana ya yi domin duk yadda zuciyarsa ke fasalta masa kyanta abin ya shige haka, musamman da tayi maganar kamar wacce bata hayyacinta idanunta rufe gashin idanunta sun kwanta luf luf gwanin sha'awa fuskarta ta ƙara haske.
"Kin farka? Ya jikin"
Muryarsa ta daki dodon kunnenta yanzu kam allurar ta gama sakinta ta buɗe manyan Idanunta da suka kumbura tare da sauke ganinta akan Aliyu Sufyan Alhassan. Ta runtse idanu yau ƙarya ta ƙare fuskarta available, Allah ya rufa mata asiri jikinta a rufe yake.
"Sorry, In sha Allah komai ya zo ƙarshe zan wankeki wajan Abbu be patient" bata kalle shi ba, domin ƙirjinta ya yi mata nauyi babu wanda ya sake magana har Aliyu ya ce "I love my son, i love both"
"Ka barni" ta furta a kame cikin sanyin harshe. Aliyu ya gyara zama idanunsa akan fuskarta duk da bashi take kallo ba. "You're dreaming, ba zan sake kuskuren baya Jidderh,ba zan sake ba, ina son rayuwa da yarona tare da mother's of the son"
"Ni guba ce, zan iya zama illa ga kowa" ya tari numfashinta ya ce
"Ban dani Aliyu Sufyan Alhassan, ban dani Jeederh" ta juya ta kalle shi kallon daya kusa zautar da shi hannunta ɗaya a ƙirjinta ta riƙe sosai cikin nutsuwarta da kamilalliyyar muryarta ta kame kanta sosai ta ce. "Baka da haɗi da ɗana, kada ka yaudari kan ka ka duba kusancinmu da Latifa ka barni" "Jeederh idan na barki ki ɗauka na bar duniya, Latifa kuma ta bani full opportunity na aurenki" cikin gajiya wa ta ce "ba zaka saman ba"
"Koda na halattawa kai na zama Uba ga danƙi? Wallahi Majeederh na shirya ɗaukan ko wanne ƙalubale akan ki, kuma idan wannan yaron zai sanya ki aureni zan je court ta mallaka mini shi,wanne Irin mallakawa ma? Bayan blood grp ɗina da na shi ɗaya ne, ko DNA text za a yi zai tabbatar da ni ne uban shi" Wayarsa ce ta fara ringing sunan Wife ya fito ya ɗan ja tsaki har kiran ya tsinke aka sake kira lokacin Jaririn ya fara kuka, picking call ɗin ya yi tare da saka wayar a hands free.
Muryar Latifa na rawa ta ce "Sweetheart kana ina? 3days without you ina ka je ina ta kiran number ka a kashe" ba yabo ba fallasa ya ce.
"Ya akai Latifa?"
"Wani abu mai kama da almara ya faru, na kasa sanin babin da zan iya sanya Malama Majeederh"
Aliyu ya ce "Just go to the point Wife" cikin damuwa Latifa ta ce "Majeederh ta haihu,na goya mata baya amma ta bani kunya ta sanya ina yawo da ita har ina kare cikin shege?" Ya tare ta faÉ—in
"Who told you that?"
"Ruma, ta kirani tun a daren da abin ya faru lokacin na tashi naga babu kai babu motarka, kwana uku kenan yanzu haka Majeederh ta gudu da É—an gudun surutun jama'a kuma ta shaida É—an shege ne, Ruma ta ce Majeederh ta bayyana musu cewa daga gidan Abbu ba inda zata sai gidan uban É—an taci gaba da zaman karuwanci da shi"
Duk maganar da suke Majeederh na ji, tuni ta amshe ɗanta daga hannun Aliyu ta rungume shi,tana jin kawo yanzu shi ne kaɗai ya rage mata, shi zata kalla matsayin wani nata kuma zata kula da shi da dukkan iyawarta har kawo lokacin da gaskiya zata kure ƙarya.
"Ke yanzu kin Yarda Malama Majeederh Abdul'aziz Khan zata iya aikata ZINA?"
"Me zai hana Sweetheart? Tunda ga gaskiya ta bayyana kuma Allah ya isa tsakanina da ita, na gode Allah da ya sanya baka aureta ba, balle mu haÉ—a iri da shege" "Ba shege bane"
Da ƙarfi ta ce "Wallahi shege ne" cikin tsawa mai firgitarwa ya ce
"Latifa Omar idan ki ka sake sheganta mini yaro zaki sha mamakina, zan miki hauka zan nuna miki true color na" Majeederh ta dafe kanta a hankali ta miƙe bayan ta zare ƙarin ruwan da ake mata, ganin Aliyu ya juya baya yana masifa jijiyoyin kansa na motsawa ta sulale a hankali ta bar room ɗin rungume da jaririn nata.
Kamar mahaukaciya haka ta zama, Latifa ta hargitse tamkar zata cinnawa kanta wuta ta ce "Aliyu Sufyan Alhassan kasan me ka ke cewa? Mene haɗinka da yaron?" Cikin rashin damuwa kuma daman ya shirya amsar ko wanne ƙalubale ya ce.
"Yes that's my name Aliyu, kuma baki taɓa jin nayi hauka ba sai dai ina dab da shirin manna bikin haukan ke, tunda ba soyayyar gaskiya ki ke nunawa Majeederh ba"
Latifa ta zari key É—in motar ta ce "Don't Tell me kana tare da Majeederh tsayin kwanaki ukun nan?" Ya ware hannu irin he don't care É—in nan ya ce.
"Yhh, Ina tare da ÆŠana da matata, Majeederh is my wife....

08119237616*🌈MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta
*_Arewabooks@Nimcylub_*
Chapter 4 · 0% Book details