← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 93

Sashe 44

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ALLAH ya nuna mana ranar Monday Monday Lafiya.... Have a nice weekend👑🍷29 Da sauri Aliyu ya juya tare da fita daga hall ɗin, Alpha ya harɗe hannu a ƙirji zuciyarsa na harbawa, Ajlaal Sultaan kowa numfashi ya sauke yana mai lafewa a bayan matarsa tunani fal a zuciyarsa, kyakkyawan matashin dake zaune kusa da Gwamna ya runtse idanunsa. Tsoro da fargaba ya cika zuciyar ko wanne haifaffen ɗan Nijeriya dake zaune a hall ɗin. Idanun dubban jama'ar wajan ya sauka akan Majeederh da jikinta ya fara rawa ƙwaƙwalwarta ta tsaya cak kamar wacce akaiwa formatting. Malaman da suke lura da musabaƙar suka dinga kallon Majeederh cike da mamaki da tu'ajujji tunda ta fara babu gyaran da akai mata, babu shakka mu'ujizarsa Alkur'ani ce ta sauka akanta, hakan ya sa ta mancewa komai. A hankali ta kifa kanta cikin rauni ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangiji ka taimakeni kada na kunyata a idanun ƴan ƙasata" Da sauri wani malami ya yi mata alama data ɗauki ruwa ta sha, kasa yin musu ta yi ta ɗauki ruwan ta sha ta cikin liƙab ɗin fuskarta, a daidai lokacin kuma computer ta Kaɗa wanda yake alamanta mata cewa ta fita daga cikin lokacinta. Jikinta jama'ar wajan duk ya yi sanyi domin kowa ya ƙaddara Majeederh matsayin wacce za ta yi nasara ganin har zuwa zagaye na biyar ɗin ba a cita gyara ba, makinta ya fi na kowa saɓanin sauran da duk zagaye aci su gyara wajan biyu ko uku. Akai sanarwar tafiya break bayan an dawo za ayi Finally round wanda shi ne zagaye mafi wahala aka umarci gabaɗaya ɗaliban da suje su sha ruwa su huta. A sanyaye Majeederh ta tashi juwa na ɗaukanta Ƙhulud na ganin haka ta miƙe cikin sauri ta ƙarasa ta ce "Mu je ki huta" Majeederh ta tsorawa Ƙhulud Arzaan idanu kasa magana tayi sai jikin Ƙhulud data faɗa ta ƙanƙame tana sauke numfashi, da ace taga idanun wani ahhali nata da babu shakka ta ji sauƙin abinda take ji a zuciya, amma ƙaddara ce haka babu kowa nata a wajan da zata iya raɓar shi ta ji sanyi. "Ba zan iya fa, I alrdy told them" Ƙhulud ta ce "Zaki iya, kina da cikakken lokaci" Ta faɗa tana rungume Majeederh. Daga gefe suka ji an ce "Daman dai Nijeriya ai ta saba samun failing, bata taɓa winning ba ko sau ɗaya, babbar matsalar sun ɗauki daƙiƙiya matsayin wacce zata wakilce su" Ya taɓe baki ya ce "Goodness, please Maa step down for Juwaira ki barwa Qatar domin baki da ilimin cin gasar Alkur'ani ta duniya, actually baki da shi, baki cancanta ba" Ba Majeederh ba, hatta Ƙhulud ta girgiza da jin maganar kai tsaye ta fahimci mamallakin muryar ta juya suka haɗa idanu da Ajlaal ta ce "Kalb, Majeederh ce fa? Ita ce Daƙiƙiya?? Duk ciki ita kaɗai ce ba aiwa gyara ba, me ya sa?" Ajlaal idanunsa akan Majeederh da kanta ke ƙasa ya fahimci yadda maganarsa ta yi tasiri a zuciyarsa musamman da yaga jikinta na rawa "Ita fa, ni muryarta ce ma ta firgitar dani wallahi, karatu sakaka kamar zubar ruwan sama, Asstagafirullah gaskiya Nijeriya akwai saura gashi sun saka hope kuma za su yi failing" Ajlaal Sultaan ya sake faɗa yana lumshe idanu. Ƙhulud ta kafe shi da idanu ta kasa fahimta yanayinsa, bata taɓa jin ya yi magana mai tsayin haka ba, a rarrabe yake yinta. "Me ta yi maka da zaka jefe ta da wannan maganar Ajlaal Sultaan? Da zaka wulaƙanta ta?" Ya watsa hannu irin ko a jikinsa ya ce "I don't know what comes over me, amma na ji kamar bata yi mini ba, ina bala'in son mace mai tsayawa akan nasara wacce bata yarda da faɗuwa ba, Sorry Nigeria" Ya yi gaba "Meke damun Ajlaal?" Ƙhulud ta furta tana binsa da kallo ganin yadda yake tafiya kamar bai so. Majeederh kasa motsi ta yi maganganun Ajlaal suka zauna daram a zuciyarta tare da yi mata amsa kuwwa! Ta ji jarumta ya zo mata, komai na kanta ya dawo fresh, Ƙhulud za ta yi magana Majeederh ta girgiza kai tana ɗan yi murmushi "Babu komai" Majeederh ta faɗa a taushashe tana nufar wani corridor, duk abinda yake faruwa akan idanun Captain Alpha daya jingina yana kuma jin komai deep down na zuciyarsa godiya yakewa Ajlaal yasan Majeederh ta tsani ace bata da ilimi ko a jefata da kalmar _“Kasawa”_ Ya yi murmushi kawai yana ɗauke kansa gefe guda. Majeederh ta buɗe bottle water mai sanyi ta shanye tas, a hankali ta shiga safa da marwa idanunta rufe, idan ta ja numfashi sai ta sauke. Tana tsaye Wani malami ya ce "Ki nutsu, tunda kin fahimci weakness na ki sai ki kiyaye kallon mutane, mu je lokaci ya yi" Ta jinjina kai har yanzu idanunta rufe yana gaba tana binsa a baya. Cikar da hall ɗin ya yi har yafi na baya, kanta a ƙasa ta nemi wajan zamanta a hankali girgiza cinyarta idanunta rufe. Rabin jama'ar wajan idanunsa yana kanta mamakin yadda sauran ɗaliban aka rufesu malamai da jagororin ƙasar su, ita kuma ba kowa. Ɗaya bayan ɗaya aka fara gabatar da final round babu ƙasar data tsallake sai da suka sha gyara, gyara kuma na ban mamaki har aka zagayo kan Majeederh. Ta runtse idanu jin computer na gabanta ya yi ƙara kafin ta ji computer ta ce. "الله" "Ma hukumu?" Ma'ana hukuncin kalmar Allahu. Ta sauke ajjiyar zuciya a taushashe cikin sanyin murya mai daɗi ta ce "Tafkimun laámun ismul jalala" Computer ta nuna blue alamar “Mumtaz" ta yi daidai aka ci-gaba da yi mata tambayoyi na Alkur'ani kafin daga bisani aja mata aya “Allah taziru waá zirataán uƙƙurrah" Ba sunan sura ba number aya kawai ita ce zatai tunanin wacce surah ce. Ta yi shiru ta rufe Idanunta tare da dunƙule hannu exlty yadda take yi idan tana haddar Alkur'ani. Ajlaal dake hakimce saman kyakkyawar kujera ya zubawa Majeederh Idanu, haka Aliyu da shigowar shi kenan sai Alpha daya kasa Kallonta, matashin saurayi kuma ƙanƙame jikinsa ya yi waje guda.... Daga can ƙasa Nijeriya gabaɗaya Khan family ne zaune a babban parlourn gidan Uncle Isma'il, sun tisa plasma a gaba tsoro ya cika zuciyar kowa musamman Abbu. Ba iya Khan family ba duk wani gida idan ka shiga kallon musaɓar suke live, wanda basu da t.v a rediyo suke saurara. Abbu ya saka hannu ya share zufar data gangaro masa, ya kasa zama waje guda ya gama tsara plan ɗin yadda zai yi da duk wata kyauta da kuɗin da Majeederh ta samu, amma da alama yarinyar baƙin ciki take masa yana da tabbacin ta iya mugunta ce kawai. Ba zai iya zama ya ji wannan abun ba ya nufi hanyar fita daga parlourn daidai nan ya ji sautin saukar muryarta a cikin kunnenshi wacce ta wadatu da zallar ƙira'a Tajwid mukarijil hurum, ta fitar da komai da karatun Alkur'ani yake buƙata ta saka komai cikin muhallinta. Cak Abbu ya tsaya yana washe baki farin ciki fal zuciyarsa. Uncle Isma'il, Uncle Isma'il Bello, Maman Alpha, Anti, Mami, Aaliyyah, Ruma, Raihana, Widad, Innati... E.t.c suka sanya kabbara. Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Ajlaal Sultaan ya sauke yana tasbihi a ransa, Aliyu ya yi ƙasa da kansa hall ɗin tsit sautin ƙira'arta ne kawai yake tashi har computer ta tsayar da ita alamun lokaci ya yi. Lokacin daya shiga cikin kundin dairy ɗin Majeederh Abdul'aziz Khan, ta kasa tashi a hankali ta durƙoshe a wajan jikinta na ɓari rawa da ƙyarma wani irin raunataccen kuka ya ƙwace mata lokacin da alƙalai suka tabbatar da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Matsayin wacce ta zama Gwarzuwa a jerin ɗalibai sama da 100 wanda yake nufin Nigeria ta ƙwace kambon tarihi daga hannun Ƙasar Misira wanda sune su kai na ɗaya a shekarar data gabata. Shugaban ƙasar Nijeriya riƙe kai ya yi ashe kafin ya sauka da rabon a teniwarsa uwa Nigeria zata amsa wannan kambon? Sauran gwamnoni suka miƙe lokaci guda hadda gwamnan Kano suka shiga ɗaga hannu da kabbara, da sarkin Misira dana Saudiyya Sarki Sultaan suka nufi inda Majeederh Abdul'aziz Khan take durƙoshe, Zaytoon ta saka hannu ta ɗagota tare da jawota ta rungume tana cewa "Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar ma sha Allah" Majeederh daman waje take nema domin ta kasa believing na nasarar data samu, ta ƙanƙame Zaytoon tana sakin wani mahaukacin kuka, She just wished that her parents were here to see her suga nasarar data samu, musamman Abbu burinsa ya fara cika. Ƴan jaridu gidan t.v da rediyo sukai kan Majeederh ɗaukarta suke ta ko'ina, lokacin da aka ɗauki wata farar hula ta silver aka saka mata tare da ɗaukan wani abu mai kama da Award na zallar tagulla aka bata wanda ya biyo ta hannun Sarki Sultaan, yin duniya ta cire liƙab ɗin taƙi haka aka dinga yi mata photo wanda kai tsaye ake watsa su a duniya, wasu mahaukatan kuɗi aka bata wanda ita kanta ba zata ce ga adadin su domin hankalinta baya kai tunaninta yana ga mahaifinta. Aka rataya mata sarƙa gold daga nan aka dinga mata kyauta wannan gwamna ya ce ya bata kaza wannan ya ce ya bata kaza, Shugaban ƙasar Nijeriya har yanzu kasa tantance me zai bata matsayin kyauta, duk abinda ya yi tunani sai yaga ya yi kaɗan. Kyautar kujerar Umara data hajji aka bata sarkin Makka ya ƙara bata kyautar kujerar hajji. Kana aka dinga photo lokacin da aka sanya mata albarka bata san mene ya faru ba, Majeederh ta samu kanta da wani irin jin girma wani abu mai girma ya hau kanta daga nan taro ya watse sai walimar da za ayi da daddare. Ƙhulud ta rungume Majeederh tana kuka murmushi kawai Majeederh ta yi tare da bubbuga bayanta a hankali ta ce "Ina mijinki?" "Yana wajan takawa" cewar Ƙhulud, Majeederh ta ce "Rakani" Da sauri Ƙhulud ta kama hannun Majeederh suka isa wajan Ajlaal na tsaya rungume da Zaytoon da yake tsokanarta Majeederh ta tsaya kanta a ƙasa Zaytoon ta ce "Ba dai ita ce wacce kike bani labari ba?" “.... Ita ce Grandma” "Ma sha Allah, na yi farin ciki ina alfahari dake da ƙasarku" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Na gode Mama" Zaytoon ta ce "Laa, wacce
Chapter 44 · 0% Book details