Sashe 12
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
da ɗaura towel jikinta sai sheƙi yake ko'ina yana glowing tunda hutu take samu. Dirarriyar mace ajin farko, kyawun Majeederh na iya sanya ayi raped nata balle Mutum ya yi arba da surar jikinta. Fitowa tayi ta ɗauki wata push pink ɗin abaya ta sanya tayi rolling kanta tare da tsayawa gaban window tana kallon waje tare da shaƙar fresh air, a hankali ta ƙara buɗe Idanunta domin daga bayan ɗakin da take gate ɗin bayan gidan ne idon ba gizo Idanunta ke mata ba babu shakka mutum take hangowa zaune shi ɗaya ya zuba uban tagumi... Washegari ta shirya tsaf ita da Khalil tana cikin wata blue black ɗin Abaya tayi rolling kanta da babban mayafi fuskar nan fara fat kamar wacce jini ya ƙarewa ga yawon jiri da take yi da ciwon kai duk dare, ta ajjiye cup ɗin hannunta Mama dake zaune ta ce "Ko ke fa, ai jego ba zai yiwu babu cin abinci ba, shi ya sa babu ko ruwan nono a jikinki, ina tunanin zan yi wa Haseenatou magana ta zo ta tayaki zama kyafi sakewa" "Na gode sosai Mama, am ina son tafiya" "Tafiya zuwa ina? Kina kallon yadda jama'a suke fakon ki kamar kin kashe rai wani bai san meke faruwa ba, kawai jita jita zai ji ya kama ya ɗorawa kansa, Ƴata duk wata daraja mace gidan mijinta idan babu shi ne ake rayuwa cikin gidan iyaye, yanzu an shige zamanin da idan ƙaddara ta faɗawa ɗan ka zaka gujesa, a lokacin ma zaka jawosa jikinka, Malama Majeederh baki da wajan zuwa sama da nan kiyi zamanki ki raini ɗan ki har ki samu mijin aure" Majeederh jin Mama kawai take domin ita ba aure yanzu a shafin rayuwarta, babu ma namijin da zai iya sha'awar zama da ita matsayin miji. Suna zaune aka buɗe ƙofa wata kyakkyawar yarinya ta fara shigowa da gudu hannunta riƙe da teddy tana zuwa ta haye jikin Mama ta ce. "Uncle ba ni" "To ƴar gatan Uncle" P.a Hammad ya shigo da murmushin tare da zubewa ya ce "Ina kwana Mama" Mama tayi murmushi ta ce "Allhamdulillah ya mutum gidan" ya amsa da "Suna lafiya" ta miƙe tsaye ta ajjiye Jidda ta ce "Bari na shiga na kalli labarai" ya yi mata adawo lafiya cike da ladabi da girmamawa domin yana da tabbacin Malama Majeederh ta girme shi ya ce "Barka da Safiya Anti Majeederh" idanunta akan Khalil a kullum shi ne abokin wasanta, ya zame mata t.v Ta jima tana kallon Khalil kafin ta ce "Kana lafiya?" "Allahamdulillah ya baby" ta juya idanunta kawai bata ce komai ba. "Jidda ce Mami good morning" ta kalli Pa. Hammad ta ce "Mami ce?" Daga bakin ƙofa aka ce "She's your Mother, jeki gaidata" His Excellency Abu-turab ya furta yana shigowa cikin wata dakakkiyar shadda mai kyau sai zabga ƙamshi yake sosai nutsuwarsa ta gama bayyana kamalar shi. Jidda tana tsalle da murna ta ce "Mamina" Ta faɗa tana leƙa fuskar Malama Majeederh. Jeederh ta yi wa Jidda murmushi tana shafa kanta, P.a Hammad ya yi waje ya bar daga His Excellency sai Malama Majeederh da Jidda. "Is my daughter, mun rasa mahaifiyarta wajan haihuwarta honestly sunanki na saka mata" da mamakin sosai Majeederh ke jin abun ina ya santa har ya sanyawa yarinyarsa sunanta? Lallai karamcin Abu-turab daban yake, kamar yadda ya ce haka aka yanka rago tare da ƙara yiwa Ibrahimul-khalil huɗu ba da sunan daya samu. Tun daga nesa yake danna horn cikin sauri mai gadi ya buɗe masa ya shigo, a hankali ya sako kan motar cikin harabar gidan nasa, mamakin ganin motoci daban daban a parking lot ya kama shi. Ya buɗe ya fito yana sanye cikin wani tattausa brown ɗin yadi mai laushi ya ɗora hula jaddara, hannunsa ɗaya ya saka cikin Aljihu har zai tambayi mai gadi baƙi akai ne? Sai kawai ya buɗe ƙofa ya shiga, shiru gidan babu motsin komai sai wani slow music dake ta shi, ga parlourn kaca-kaca sai wari da ƙaurin abinci yake, kwalayen exotic birjik plate ɗin abinci har a saman kujera, nan da nan cikin Bar Aliyu Sufyan Alhassan ya fara juyawa ya toshe hanci da sauri yana haurawa sama tare kiran "Latifa, Latifa" Yana ƙoƙarin buɗe Ƙofar bedroom ɗin ta tayi saurin fitowa, ya shiga kallonta frm head to toe, towel ne a jikinta iya qiwwa gashin kanta duk a har gitse ya dubi gefen bakinta ya ga jambaki. "Lafiya?" Aliyu ya ce "Su waye a gidan?" Ta ce "Friends ɗina ne, yanzu zasu bar maka gida" ya yi jim kafin ya ce "Yanzu dake da friends ɗin mahaukatan ina ne Wife? Ki kalli gidan nan kamar bola wanne irin abu ne, kema kalleki babu tsafta ba komai irin ƙamshin perfume ɗin nan ma babu, babu mamaki part ɗina ba haka yake ba gyara a haka ki ke ihun kada nayi aure? Ko son ki zai kasheni idan har zaki dinga gallaza mini da ƙazantarki wallahi tsanarki zan yi" ya juya rai ɓace bai taɓa ganin ƙazanta irin ta Latifa ba ta rasa yadda za tayi amma tayi farin ciki domin ita tunaninta ya manta da batun Latifa... Gidan ya yi shiru Mama tana part ɗinta, His Excellency Abu-turab ya fita zuwa Wajan meeting a Government house, securities ɗin na bakin ƙofa. A hankali ya dinga leƙo kansa ta wajan gate ɗin dake kusa da bedroom ɗin Jeederh, shigar yau ta musamman ce gashin kansa ya ƙarya hargitsewa ya kwanto gaban goshinsa, hannunsa riƙe da wani teddy da flower mai kyau rabin faffaɗan ƙirjinsa a bayyane sbd yagewar da rigarsa tayi wandon jikinsa 3gauter ne, ga ƙatuwar sarƙa a wuya. Ya kama gate ɗin tare da dirowa cikin gidan, da sauri ya nufi bedroom ɗin cikin sa a yana kama handle ɗin bedroom ya jisa a buɗe, Abraham ya lumshe idanunsa masu cike da kewa ba sallama ba knocking ya tura kansa cikin bedroom ɗin daidai lokacin ta fito daga toilet tana sanye towel iya cinya...