← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 93

Sashe 61

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Aliyu ya dai kalleta sai kawai ya girgiza ya ce "Bata jin daɗi, shi ne nayi takeaway" Ta ce "Allah ya sauwaƙa" Parking Aliyu ya yi a ƙofar gidansa bayan ya kashe motar ya fito yana zube hannu a aljihu wani irin baiwar kyau Ubangiji ya zubawa Aliyu, domin ko Ajlaal sai dai ya nuna mana hasken fata da suma mai yawa da kuma launin idanu, gashi da wani irin haƙuri da kawaici amma idan ransa ya ɓaci kamar Mahaukaci haka yake yana da ƙulafuci da saka abu a rai. Ya ce "Kamar an rufe gidan ko?" Ta yi masa shiru yana mmkin yadda Majeederh ke feeling kanta da yawa, tsayin shekaru bai taɓa ganin munafukar fuskar da ake rufewa ba. Jin shiru ta ɗago kai suka haɗa idanu ta kame fuska tana jan jakarta zuwa hanyar gate domin tuni gatekeeper ya buɗe tana jinsa yana magana amma ta yi shiru a gareta haramci ne babba da ɗaukar ƙaton zunubi ga yin magana da namiji baligi sai ya zama dole. Tana shiga cikin gidan taga Abbu tsaye a Balcony ta zube har ƙasa ta gaishesa ya amsa a wannan karan ta yi mamaki da ya ce mata "Congratulations" Ta nufi cikin gidan tana shiga Aaliyah ta rungumeta tana ihun murnar ganinta, Majeederh ta cire liƙab ɗinta bayan ta tsuguna ta ce "Barka da dare Mami" "Yawwa" Ta ce tana binta da ido, Raihana ta ce "Allah mai iko! Ana ta shiga rigar Muslunci ana ci da addini" Aaliyah ta kalleta ta ce "Idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana" Raihana ta watsa mata harara tana cewa. "Ji saƙarya, ana maganar kan giwa wake jiyo ƙamshin zomo? Mai da wuƙar ni ba tsararki ba ce" Aaliyyah ta riƙe haɓa ta ce "Hooo ƙaasa, to aini walkice daidai da ƙugun ko wanne lalatacce, kuma Majeederh kuturwa uwa ce zama da ita dole murucin kan dutse bai fito ba sai daya shirya" Raihana taja tsaki ta ce "To ai ga sararin subuhana ɗin nan, sai a zuba muga idan za a kwashe daidai, ba girin girin ba ta yi mai" Majeederh dai ikon Allah kawai take kallo domin ita bata ma iya karin magana da habaici ba shi yasa ta rasa fahimtar me suke cewa, Mami na zaune watching all of them. Aaliyyah ta saki dariya ta ce "Ai gurbin idon ba idanun bane, ni masallacin kurawa ce bawa kare limanci daidai yake da datse iskar dake shaƙa, kiyi a hankali domin na kawo kai nasan fari na san baƙi kada ki ja nayi miki wankin babban bargo, domin naga fahimtar ki daidai yake da fahimtar yaron goye, bana son kuma ya kasance duk kun far bakinki kiyi haihuwar guzuma" Raihana ta ce "Me kike nufi da haihuwar Guzuma? An faɗa an ƙara faɗa idan Majeederh tayi zuciya gobe muji loud speaker Liman na sanar da ɗaurin aurenta, waye bai san cewa Majeederh ba auren ne a gabanta ba? Office ɗin data buɗe na mene? Gari gari da take zuwa da sunan kaiwa marayu taimako bayan ƙarya ne na mene? Ke yarinya wahainiyarki ta kiyayi ramata, ta dauwama ba tayi aure ba har Mahadi ya bayyana" Aaliyyah idanunta a cicciko da hawaye ta ce "Bar gaigaye za kici tumu ne, ƙaddara zane gwara ita tata ƙaddarar ya fito sarari mun gani, kuma komai ya yi farko zai yi ƙarshe" Ruma ce ta fito daga ɗaki ta ce "Kaza uwar tune tune mene ya faru kuma?" Kafin Aaliyah tayi magana Abbu ya shigo gabaɗaya suka nutsu ya dinga binsu da kallo kafin ya ce "Kun kyauta, ko wacce ta fice mini daga cikin gida" Raihana ta ce "Abbu ka yi haƙuri baya nan fa, gidan shiru tsoro nake ji" A fusace ya ce "Ya kashe ki, kuzo ku fi ce mini" Jiki na rawa suka ɗauki mayafi da handbags ɗin su ya ce "Shashai, ku dinga faɗa kamar ba jini ɗaya ba zan yi maganin ko wannenku kada ɗan banzan yada dake dawo mini gida" Ya juya kan Aaliyyah ya ce "Dage, basu girmeki ba?" Ta ce "Kayi haƙuri Abbu Anti Jeederh sukewa gorin aure hadda sharri" Ya kalleta ya ce "To kashin awakai, ita Majeederh Ubangiji bai bata baki bane? Sai ke rasai? Ba ita ta sake musu ba da tana cin ubansu tun farko za ayi haka?" Mami ta dinga kallon Abbu sai bata ce komai ba, ya dawo kanta ya ce "Asabe kin kyauta,na kuma gode" Ya kalli Majeederh ya ce "Da safe ki same ni"..... Washegari da safe bayan Majeederh ta shirya cikin wata tsadaddiyyar Abaya Marron irin turkies Abaya ɗin nan ta samu Abbu a parlourn shi yana zaune ya yi shiru bayan sun gaisa ta ce "Abbu gani" Ya ce "Hawwa'u, Hawwa'u, Hawwa'u" Ya yi pointing nata ya ce "Sau nawa na kira sunanki?" Ta ce "Uku Abbu" Ya jinjina kai ya ce "To wallahi Allah na gaji da ganinki a gidan nan" Da wani irin Shock take kallon Mahaifinta tashin hankali ya bayyana akan fuskarta tsoro da wasa fargabar Abinda zai biyo baya ya wanzu a zuciyarta Abbu ya ce "Shekararki 31 a duniya kina gantali,duk sha'aninki suna gidan mijinsu harda yara uku wasu huɗu amma ke kina yawon neman abin duniya? Yaran da aka tsuguna aka haifa akan idanunki duk suna ɗakin mazajan su banda ke, kina jerawa da Majaufiarki kamar sa'arki? Ka kaf Family ke ɗaya ya rage idan kika ɗauke Aaliyyah da Sona? Wallahi wallahi idan ina ganinki a gidan nan zuciyata zafi take daurewa kawai nake idan kuma na ci-gaba da ganinki tabbas zuciyata bugawa za ta yi sbd baƙin cikin ki......
Chapter 61 · 0% Book details