← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 93

Sashe 91

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

50 Tunda suka shiga cikin jirgin Abraham ya rasa tunaninsa idanunsa jajur kansa a kife yana jin gabaɗaya kamar bashi ba, jikinsa ne kawai cikin jirgin amma tunaninsa da ruhinsa ya barsu a nan Nigeria, babu kuma wanda ya yi attempting kula shi daga Escorts ɗin Dad ɗinsa har Grandpa. 5 hours 42 minutes, ya kai su Germany, jirkinsu ya sauka a airport ɗin Berlin Brandenburg Airport (BER). Ya ɗauki wajan minutes kafin gently ya fito dan kansa, da sauri ya shiga taka matattakalar benen zuwa ƙasa, tun kafin ya ƙarasa wata black ɗin Mercedes-Benz S600 ta tsaya a gabansa, aka buɗe masa back seat ya shiga yana sauke numfashi motar Escorts a gaba ta Abraham a tsakiya sai ta Grandpa na bin baya, sai wasu Escorts ɗin a bayansu. Tafiya sukai sosai sun ɗauki hanyar zuwa Hammerschmidt Villa in Bonn, sai suka samu saƙon gaggawa akan su shige da shi President's Palace. Suka juya kan motar tare da nufar Bellevue Palace in Berlin. Tun daga bakin shiga Federal President's Palace ɗin zaka dinga cin karo da wasu manyan manyan sojoji ga wasu Escorts na musamman. Hakan zai tabbatar da yadda shugaban ƙasar yake da ƙarfin iko sosai. Kai tsaye motocin ciki suka shiga tun kafin a gama parking Abraham ya fito da sauri kamar zai tashi sama. Ko'ina na gidan fari ne tas idan ka ɗauke green grass ɗin dake waje, kai tsaye part ɗin daya tabbatar sai samu Dad ɗin nasa ya nufa, cikin sa a ya same shi tsaye ya juya baya da ƙofar shigowa cikin parlourn nasa, hucin da ya ji yasan stubborn boy ɗinsa ya ƙarasu babu mai zarrar shigowa part ɗin nasa kai tsaye dole sai shi. Gently ya juya idanunsa ya sauka akan Abraham dake tsaye jikinsa na rawa sosai ya ce "Wlcm back my dear" Wani ihu Abraham ya yi yana nuna Dad ɗin nasa ya ce "Who the hell do you think you are? Eh?" Dad ɗin ya ce "Son i need u" A hargitse ya ce "I hate you Dad, i hate you, i don't want see your face" Dad ya ƙarasa wajan Abraham zai taɓa shi ya ce "Faɗa mini wani abu, daɗin me kake ji a zaman Nigeria? Ko sbd kana son babbar mace Musulma?" Abraham ya yi shiru. "Buɗe kunne ka ji da kyau, kai da Nigeria har abada, zaka zauna dani a nan, ka je can uban yarinya na wulaƙantan ka bayan ka fi shi komai na rayuwa? You're my darling, President's son, kana da komai ka zauna wajan wanda basu da ko sisi" Abraham ya ture hannun Dad ɗinsa daga kafaɗarshi yana huci ya ce "Su ɗin sun fiye mini kai" Dad ya yi murmushi kawai yana ƙara jinjina ƙuruciyar ɗan nasa "Sbd wacce kake kira Mami? Ta faɗi nawa za a bata da rainon da tayi maka shi kenan?" Abraham ya ce "Aurenta zan yi, ina son ta" Dad ya koma ya zauna saman wata ƙatuwar kujera mai kyau yana girgiza ƙafa ya ce "Ba zaka sauya ba, my child is still young" Abraham ya sa ƙafa ya tar watsa Glasses ɗin dake kusa da shi ya ce "Young? To ka jira zan kawo maka ɗan da zanwa Jee ciki ta haihu, stay away from my life ka manta kana da ɗa kamar yadda na manta ina da uba, me ka taɓa mini na kyautatawa daga haihuwa zuwa yanzu eh? Sau ɗaya baka taɓa kwana tare dani ba, ban taɓa jin ɗumin jikin ba, ban taɓa ganin soyayyarka ba, cutarwarka kawai na sani, azabarka kawai na sani you're the reason behind anything duk abinda na aikata kai ne sila, ka zaɓi karuwarka fiye dani" Dad ɗin kallon yaron nasa kawai yake, yana mamakin yadda ya kasa mance lokacin daya same shi tare da Kiristi akan gado, memory na nan a kansa moment ɗin ba zai taɓa goshewa a wajansa ba, wannan ya riga a ransa wanda ya sa ya yi masa tsana mai muni. A hankali ya ce "Listen Son, zo nan I'll explain everything to you" Abraham ya ce "Everything?" Ya girgiza kai kawai ya rasa me zai ce tunda ya fara maganar yaƙi yadda ya kalli cikin idanun mahaifin nasa. Ya juya zai fice Dad ya ce "Ina zaka?" Ya ce "Nigeria" Dad ya miƙe ya ce "Kai ba zaka kaji wani iri ba? Ka zauna a inda ake wulaƙanta ka? Kuma waccar yarinyar kake son lalata ƙungiyarka a wajanta? Me ka gani a wajanta?" A hargitse Abraham ya ce "Abinda ka gani a wajan Kiristi, Jee da kake gani tafi mini komai na duniya, mulkin ka ɗin me? Kaga taɓa ji na nemi sisi wajaka Dad? Duk abinda na mallaka kuɗi na ne, halak ɗina ne kamar yadda Jee ta faɗa mini na nemi halak duk wahalarsa, to yanzu na girma baka isa ka faɗa mini yadda zan da rayuwata ba am maturel enough Dad" Dad ɗin masifar ɗan nasa da zafin ransa har mmki yake basa daman can haka yake? Shi ba zai ɗorar da komai akan rayuwar Abraham ba yana sawa dai ana bincika masa. Private Investigators. "Sweetheart na tara maka dukiya, na ajjiye maka komai na jin daɗi Debeka na jiranka hatta gidan da kake son rayuwa sai ka zaɓa, I am the president of Germany, I am your father, I have the power to choose what is right for you, I will decide, wancan Musulmin old woman ɗin ta maka ƙatuwa kaje ka nemi wacce zaka ji daɗi tare da ita, ba zaka taɓa komawa Nigeria ba" Wani irin dariyar takaici Abraham ya yi har yana durƙoshewa a ƙasa idanunsa na zubar da hawaye ya ce "Exlty, that's exactly who you are" Ya girgiza kai yana jan numfashi tare da riƙe ƙirjinsa ya ce "I need love and care not money, soyayyar ma dana nema a baya a wajanka ka wulaƙanta ni yanzu ban so ban so" Yana faɗin hakan ya miƙe zai fice daga cikin Parlourn Dad ya ce "Come in" Wasu sabbin Escorts ne wanda Abraham bai sani ba, suka damƙe shi "Take him out" Abraham ya ce "Don't do this to me, ina son Malumana i love jee i love Mamina ka sanya su cika ni na mata al'ƙawarin zan koma" Ya fara abu kamar hauka hauka hakan yasa Dad tunanin ya samu matsala few minutes ya saka akai masa wata mahaukaciyar Injection ta bacci akai kai sa wani part can ƙarshen Palace ɗin aka garƙame.. Har wajan sati uku Abraham sunan Majeederh a bakinsa ya yi ta surutu shi kaɗai damuwa ta samu gurbi a zuciyarsa tayi daram, ya daina cin abinci ya daina magana daman dariya bata dame shi ba zai ma iya irga sanda ya yi ta. Haka aka dinga masa allura ana saka masa drip sbd rashin cin abinci. Dad ɗin ya ce da dai Abraham ya auri Musulma kuma older gwara kawai yaga gawar ɗan shi duk da irin son da yake masa. He will never allow him to be MIJIN MALAMA ba. Ba zai taɓa barinsa ya zama MIJIN MALAMA ba, wannan babban abin kunya ne ga mabiya addinin su na Kirista magoya bayan Yesu su ji labarin ɗan shi yana auran Malama, ba zai taɓa faruwa ba hakan zai iya sawa ya samu matsala da kujerarsa ta shugaban ƙasa,He doesn't want that to happen hakan ba zai taɓa faruwa... After 1 mnt. Majeederh na zaune a dining room tayi shiru tun ranar data dawo daga hospital ta koma shiru shiru. Yau kuma ta tashi bata jin daɗin gabaɗaya tayi tunanin ko al'ada za ta yi? Tana wannan tunanin Latifa ta yi sallama Mami ta ce "Latifa da sanyin safiya?" Latifa ta ce "Wlh Mami, an tashi lafiya?" Ta ce "Allahamdulillah" Latifa ta zauna tana kallon Majeederh ta ce "Lafiya kike?" Ta ɗan lumshe jiƙaƙƙun idanunta tana girjiza kai can a hankali ta ce "Headache" Mami ta ce "Gashi bamu da paracetamol a gidan nan" Latifa ta buɗe jakarta ta ce "Ga wani maganin ciwon kai mai kyau ne, tun sanda Aliyu ya ce waje da bashi da lafiya maganin yake yana da kyau sosai" Majeederh ta kalli maganin sai kuma ta jawo gorar ruwa tare da zubawa cikin cup maganin kala biyu ne ta haɗa ta watsa a baki, ta haɗiye da ƙyar dan ba zata iya kallo ai mata wata allura ba. Ji tayi amai na zuwar mata ta kifa kanta ta kifa saman dining tana mai da numfashi. Mami ta ce "Latifa ki rufawa kan ki asiri kina zama ɗakin mijinki, ki daina biyewa yawon majeederh kada azo ayi haihuwar guzuma dake da ita, ita ba aure ke kuma ki kashe naki" Lafita ta ce "Haba Mami, wai ba zaku yadda da ƙaddara bane? Mene laifin Majeederh a rashin aurenta bafa yin kanta bane itama da zaɓi za a bata wlh da tuni tana gidan mijinta da yaranta, amma miji bai zo ba zata auri kanta ne?" Mami ta ce "Ke wane ya ce miki miji ne bai zo ba? Bata niyyar aure ne amma a yawon da take na Ngo da faɗar kar da matan da take kaɗai ya isa wani ya ganta ya ƙyasa, ba lissafin aure a cikin lissafin rayuwarta" Latifa ta girgiza kai ta ce "Jinkirin aure ne kawai ta samu, Ubangiji kaɗai ya san manufar hakan itama ba da ra'ayinta ba, nasan Majeederh nasan halinta da wani yace yana sonta da aure tabbas zata faɗa mini, Mami da aure da haihuwa duk na Allah ne, amma duk kun bi kun juya mata baya sbd kawai ba tayi aure ba? Idan iyaye basu jawoka jiki a irin wannan condition ɗin da take ciki ba, bai ci ace sun juya mata baya ba, suna bawa jama'ar gari damar d su faɗi duk abinda sukai niyya akan Majeederh, Mami cikar imanin mutum shi ne yadda da ƙaddara cikakken mumini shi Ubangiji yake jarabta ko dan tabbatar da imaninsa, wallahi ba gama garin mutane Ubangiji yake nunawa jarrabawa da ƙuddirarsa akan su ba, mu yarda ne bai kawowa Majeederh mijin aure ba, mu yarda jinkirin aure ta samu" Mami ta ce "Idan mu mun yarda jama'ar gari fa?" Latifa tayi shiru can kuma ta ce "Mami mutum tara yake bai cika goma ba, a
Chapter 91 · 0% Book details