Sashe 33
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
"In capital letters, FINE" Aliyu-haydar ya faɗa yana janye jikinsa daga bed ɗin kansa ya yi masa nauyi sbd rashin bacci na kwana biyu, hakan ma jiya ta kasance masa sai daya dawo daga masallaci bacci ya ɗauke shi. Musty ya bisa da kallo musamman yadda yake tafiya kamar bai so sai kawai ya girgiza kansa ya shiga danna waya. Yana zaune har Aliyu ya fito ɗaure da towel cikin sauri ya shirya cikin wani carton ɗin Yadi mai kyau da taushi wando da half ɗin riga sai hannun rigar half dark blue ya haska farar fatarshi. Bai saka hula ba sai sunglasses daya saka ko gyara sumar shi bai ba. Ya nufi waje kai tsaye, Musty ya miƙe yana mita "Ji wulaƙanci na gama gadinka har ka shirya shi ne zaka fita?" "Waya kake dannawa fa Yaya?" Suna fitowa a jere Hajia ta miƙe tsaye a daidai lokacin Papa ya fito cikin shirin fita office. Ya dubi samarin yaran nashi a tare suka ce "Mrng Papa" "Babana, Almustapha, kun makara yau" Almustapha ya ce "Yanzu zan fita" Papa ya juya ga Aliyu-haydar ya ce "Kai fa?" Ya ɓata fuska ya ce "Ina gida" Da mamaki Papa ya ce "Gida? Daga fara aikin?" Nan da nan Aliyu ya nuna Autansa a fili ya marairaice fuska tare da langwaɓewa, Papa murmushi kawai ya yi ya ce "Hajia bari na fita" Hajia ganin yadda idanun yaran nata ya sauka akanta suna jiran su ji me zata ce, ta girgiza ƙafa kawai ta ce "Allah ya tsare ya kiyaye" Papa ya yi jim kamar na jiran wani abu sai kuma ya ce "Amin" A tare suka fice shi da Almustapha kowa ya shiga mota, Almustapha na driving kansa, Papa kuma yana baya Busy reading news paper driver na jansa a haka suka fice. Hajia ta dubi Aliyu ta ce "Auta sai yanzu?" Ya rufe idanu ya ce "Just woke up Hajia" "Ka yi breakfast?" Ya girgiza kai kawai tare da miƙewa tsaye ya ce "Ki mini addu'a zan fita yanzu zan dawo" Tana lura da yadda yake yawan lumshe idanunsa yana riƙe kai ta ce "Allah ya tsare" Hannunsa ɗaya zube cikin Aljihu ɗaya riƙe da key ya nufi harabar gidan, motarshi ya shiga yana yi mata key while yana kiran number Latifa Omar. Majeederh na zaune idanunta ya yi zururu sun faɗa fuskar nan jajur karan hancinta ya yi jaa sosai sbd damuwa. Da ƙyar ta cira kai ta kalli Latifa Omar ta ce "To ya zan yi? Mahaifina ne, na haƙura da Little" Latifa Omar ta ce "haka zaki zauna Takaicin Uba na cin zuciyar ki?" Kallon da Majeederh ta yiwa Latifa Omar ya sa ta fahimci bata ji daɗin maganar ba ta ce "Ki yi haƙuri, yanzu kina nufin bakya nan zan yi aure?" Kamar ba za ta yi magana ba ta ce "Aure zaki?" Latifa ta yi dry tana gyara zama ta ce "Aure zan yi In sha Allah, ina wannan wanda ya kaimu gidan Uncle Isma'il da Yaya Bilkisu? To shi ne ya ce yana so na, na ji tsoro ganin shi ne wani ne masu arziƙi kuma ni gani ƴar gidan Malam Shehu, amma ya ce babu komai iyayensa basu da matsala yana da kyawawan hali" Ba zata iya gane yanayin reaction na Majeederh ba kanta a ƙasa yake. "Majeederh kina ji na?" Ta ce "Allah ya sanya albarka" Kafin Latifa Omar ta yi magana wayarta ta fara ƙara ganin wanda yake kira yasa tafiya murmushi hannunta na rawa ta ɗauka ta ce "Hello" "Is not allowing, Assalamu alaiki" Majeederh ta miƙe zuwa ɗakin Abbu cikin ƙaton hijabi har ƙasa kana kallonta kasan a hargitse take. Ta yi sallama yana zaune hannunsa riƙe da wani file na takardun Majeederh ya ce "Hawwa'u kin fito? Yanzu zan office ɗin zaki?" Ta ɗaga masa kai ya ce "To ya za ayi? Bani da kuɗin mota" A sanyaye ta ce "Ina da shi" Ya miƙa mata file ɗin yana murmushi na nuna jin daɗi ya ce "Allah ya yi miki Albarka, Kinga kina zuwa Misira Shekaru takwas kin gama karatunki, idan da hali kawai ki yi zamanki a can ki fara aiki ance albashinsu akwai auki sosai" Ba zata iya tantance halin da maganar Abbu ya sanya zuciyarta a yanzu ba, kuma ta yi alƙawarin ba zata sake masa ƙorafi ba. Ta miƙe taiwa masa sai ta dawo taiwa Mami ma, Aaliyyah da su Ruma na makaranta. A hankali ta nufi waje kanta a ƙasa ga yunwa domin kafin ta farka har an cinye abinci abincin safen, jiri na ɗaukarta a haka ta yi waje ganin mota a ƙofar gidansu ya sanya ta ɗaga kanta cikin rashin sa a Idanunta ya faɗa cikin nasa suka kafe juna da wani irin kallo....