Sashe 45
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
irin Mama bayan zan iya jika dake?" Ta yi murmushi kawai Ajlaal dai yana lafe da bayan Zaytoon ya kasa Kallon Majeederh ya ji ta ce "Thank you" "For?" Ajlaal ya tambaya yana gyara tsaiwa ta ce "Kai ne ka ƙarfafa mini qiwwa na kasa mance kalmar Daƙiƙiya" Ajlaal ya ɗan shafa gemunsa ya ce "Congratulations" Yana faɗin hakan ya bar wajan. Bayan sun fito tana ƙoƙarin shiga mota domin komawa gidansu ta ji ance "Hawwa'u" Cak ta tsaya ta kasa tuna inda ta ji muryar ta juya, yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu sanye da wani tissue ɗin farin yadi ƙal da shi ta yi murmushi ta ce "Aliyu" Ya yi jim domin bai ɗauka ta san sunan shi ba ya ce "Congratulations Hawwa'u ko wani zai nuna mini farin ciki ina tunanin bayan Abbu ne" Kafin Majeederh ta yi magana aka ce "A sbd kai ne wa?" Majeederh ta ware idanu ganin Captain Alpha bakinta na rawa ta ce "Yaya?" Ya ware mata idanu ya ce "Me kike? Yana da kyau ki huta" Ta ce "Ayya yau ai bana iya bacci, Aliyu baka da lafiya?" Aliyu dai bai ce komai ba sai kafeta da idanu da yake ya ce "Congratulations once again, take this matsayin nawa gift ɗin" Ya dubi hannunsa ta box ne ɗan ƙarami ta ce "No thank you, hakan ma ma gode sosai" Calmly ya taka har inda take ya ce "Please, ki amsa kamar yadda kika amshi ta kowa" Tana ƙoƙarin amsa Alpha ya karɓa ya ce "Mun gode, let's go" Majeederh bata ji daɗi ba amma haka ta daure ta ce "Jazakallah-bil khair, ina Latifa Omar? Kun yi aure hala?" Ta faɗa cikin muryarta wacce ta juye bai amsata ba ya juya kawai tare da barin wajan. Majeederh ta shiga mota Alpha ya shiga baya kusa da ita, driver ya ja suna tafe ya buɗe box ɗin wani ɗan ƙaramin ring ne mai kyau sosai, sai wani farin tissue da akai rubuta cikin good handwritten a hankali ya fara karantawa da sauri kuma ya tura tissue ɗin cikin aljihu ya maida ring ɗin yana tafe baki. Har Magriba Majeederh na tare da yayanta Alpha sosai tayi farin ciki, har akai walima. Ƙarfe 12 na dare ta buɗe wayarta message kamar hauka musamman daga wajan Aaliyah da Anti cikin sauri ta dinga dubawa ko za taga na Abbu domin tasan he's the first person da zai cnrgt nata amma har ta gama dubawa babu nasa jikinta ya yi sanyi a hankali ta danna number Abbu ringing ɗin farko ya ɗaga ta ce "Assalamu alaiyka Ya Abbu" Abbu ya ce "Majeederh na ji labarin irin kuɗaɗen da kika samu, da na yi lissafi sun haura miliyan 20 banda kujerar makkan " Sosai abin ya bata mamaki ta ɗauka zai farin ciki ya sanya mata albarka kan nasarar data samu amma sai ta ji babu batun hakan a bakinsa maganar kuɗi kawai yake? Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ban san nawa bane Abbu, amma dai da yawa" Abbu ya ce "To da kyau ai tuni na lissafa, a hakanma banda kuɗin albashinki" Ta jinjina kai idanunta cike da hawaye wanda ya fara sakkowa saman fuskarta ta ce "Abbu ka shirya tafiya aikin hajji, ni ma zani Uncle Isma'il da Mami su je Umara" Abbu ya yi zumbur ya miƙe daga zaune ta cikin wayar ya ce "Ashe Majeederh baki da hankali baki da wayo?" Muryarta na rawa sosai ta ce "Me na yi Abbu? Ka yi haƙuri don Allah" Ya ce "Daga ni harke har su Uncle Isma'il ɗin da ita Asaben babu mai zuwa ko nan da airport balle aikin hajji, siyar da su za ayi a haɗe kan kuɗin tas" Majeederh ta ware Idanu while hawaye na zuba a fuskarta ta rufe bakinta ta kasa cewa komai "Hawwa'u?" Muryarta na rawa ta ce "Na'am Abbu?" Ya ce "Kuka zaki akan na ce haka? Shikenan riƙe kuɗaɗenki" Da sauri ta girgiza kai tana zubewa saman gwiwoyinta jikinta na rawa ta ce "Ka yafe mini Abbu wlh ba kuka nake ba, idan kukanne ma na farin ciki nake, na bar maka kuɗin halak makal ko biyar ba zan ɗauka ba, amma don girman Allah Abbu ko kai ɗaya ne ka je aikin hajjin idan ya so sai a siyar da sauran" Abbu ya girgiza kai ya ce "A'a ai tas za a siyar da su, nan gaba sai ki sama mini kuɗin da zan je aikin hajjin hakan ya fi ko?" Ta jinjina kanta ita gabaɗaya ba ruwanta da kuɗin ba shi take buƙata ba burinta kawai ta ji ya ce "Majeederh Allah ya yi miki Albarka" Wannan kalmar ita kawai take buƙatar ji, babu uwar da zata sanya mata albarka uban kuma bai damu ba. Abbu ya ce "To sai anjima aci gaba da ƙoƙarin adana kuɗi banda ɓarnatarwa" Kafin ta yi magana ya kashe wayar, sakin wayar ta yi tare da durƙoshewa ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita tana buƙatar sanya albarka ko sau ɗaya ne idanunta ya kumbura sosai da ƙyar ta iya kiran Uncle Isma'il ya yi mata addu'a haka Uncle Bello ta kira Anti da Mama kana ta kira Mami sai Aaliyyah ji tayi duniyar ta yi mata zafi komai ya jirkice mata bacci ya ƙauracewa idanunta...... Majeederh ta tattara komai ta ajjiye waje guda karatu take sosai, shaƙuwa sukai sosai da Ƙhulud Arzaan Ajlaal kuma basu taɓa magana ba tun ranar, duk wata sai ta turawa Abbu kuɗi bata san me yake da su ba, Majeederh kullum cikin azumi take ta rame sai ɗan jiki fatarta ya goge sosai, zamanta da Ƙhulud ya ƙara sawa ta zama wayayyiya sosai rashin magana ya ninka nata, tun a lokacin da Abbu ya ja mata kunne ta cire batun aure a ranta, tun tana sha'awar yi har ta fice mata a rai, ta sanyawa ranta ba zata taɓa yin aure ba, duba da cewa tun a lokacin babu wanda ya ƙara cewa yana sonta, a shekarar ƙarshe ta zanna jarrabawa mai kyau ta samu first class tayi farin ciki sosai ta zama cikakkiyar Malamar addinin Muslunci ga tarin magoya baya da take da shi a facebook ta fara faɗakarwa akan maza da mata kamar yadda taga Fauziyya d sulaiman tana yi....