Sashe 19
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
#Za ku samu littafin DAUƊAR GORA! Na ɗaya kyauta. For 2 & 3 shi ne na kuɗi akan ₦500,SP 1k,za'a tura kuɗin ta wannan account ɗin 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank,kou a tura zuwa 8165726609-Hauwa Usman Muhammad,Opay digital wallet. Mutanan Nijar/Mali zaku tura dala ɗari,SP jaka ɗaya,ku tura shaidarku zuwa 08165726609. Ku bi zazzafan alƙalamin #REAL-SMASHER domin samun cikakkiyar amsarku game da wannan matsala data taɓo wanda ya zama ruwan dare a ƙauyuka har da birni,labari ne mai cike da fa'idodi wanda sai kun bi za ku fahimci mene ne a cikinsa..11 Cikin sauri Barrister Aliyu zaki ya shiga mota tare da bin bayan Abraham, His Excellency Abu-turab ya shiga zagayawa a wajan yana sauke numfashi a wahale jiri na neman ɗaukan shi, ganin yadda yake shirin rasa Jiddo a lokacin na biyu. Al'amarin na neman zame masa tamkar ta leƙo ta koma ne, ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Wanda bashi da mara ba da inuwar giginya na nesa kasha daɗi. Ya fesar da numfashi tare da juyawa ya kalli Uncle Isma'il wanda ya fito tare da tsayawa a harabar gidan nasa, gabaɗaya ya shanye mamakin da Abraham ya shayar da shi ta hanyar zubawa bakin gate idanu a tuninsa ko Abraham zai dawo da Malama Majeederh. Amma zaton shi ya saɓa tunaninsa. "Uncle a ɗaura auren kawai" Uncle Isma'il ya dubi His Excellency, duba na tsanaki. "Matsayin auren fa?" His Excellency ya ce "Zan sanya a rufe ko wacce tashar mota, data jirgin ƙasa, zuwa na sama, dana ruwa, zan zuba jami'an tsaro a kama shi zuwa gidan yari, ita kuma sai a akai mini ita gidana" "Kada ka tsauwala, gaggawa aikin shaiɗan Your Excellency" ya ƙara girgiza kai ya ce "Majeederh ba auren sadaƙa za mu yi mata ba, tana da daraja sosai ƙaddara ce kawai ta faɗa mata, yadda aka juya mata baya ni ba zan bari ba" cikin girmamawa His Excellency Abu-turab ya dubi Uncle Isma'il kamar zai rusuna ya ce "Afuwan bana nufin haka, ka fahimci ni, ka dubi halin da nake ciki Uncle" Mahaifin Aliyu Sufyan ya numfasa ya ce "Ita mace allura ce a cikin ruwa, mai rabo ka ɗauka, ina tunanin abar maganar zuwa sanda wannan ɗin zai dawo da ita" "Mahaukaci ne fa, zai iya aikata abinda ya furta" cewar Abuturab. Murmushi kawai Uncle Bello ya yi, domin ya fahimci hutar son Majeederh a cikin idanun His Excellency. Sun sha bamban da Abraham, shi a fili yake nuna maitar shi wanda yake sawa ayi tunani jikin Majeederh da kyanta ke fisgar shi tare da ingiza shi zuwa tubalin da bashi kenan ba. Shiru ya biyo bayan maganar ta su ko wanne akwai abinda yake saƙawa a ran shi. Abu-turab ya kasa jurewa hankalinsa yana can kan Jiddo, zuciya ke raya masa yanzu ga su can ɗan iska yaron can mai idanu a tsakiyar kai yana yi mata tijara da keta mata haddi, ya samu damar da shi baya tunanin zai samu musamman da bai hango soyayyar shi a zuciyar Malama Majeederh ba. "No, i can't take it" "Me za ka yi?" Inji Uncle Isma'il. "Zan nuna masa ni ke mulkarshi, zan yi amfani da ƙarfin iko, na manta waye ni, na ajjiya matsayina akan samun Malama Majeederh amma wani na can da ita" "Ba zai cutar da ita ba" cewar Uncle Isma'il. "Zai aikata abinda ya ce, ai Mahaukaci ne" "Depression ne" "Ba su da mara ba, abin da ke gidan ƙaura shi ne a Goje, ka bani dama ka kuma share mini fage" Sai a lokacin Haseenatou ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Abin mamaki baya ƙarewa, raƙumin dawa ya ga na gida,ko a labaran Hikaya, da film da littafan hausa ban taɓa ji ko ganin yadda ake rurrumar auren mace mara tsafta wacce ta haihu ba aure ba sai yanzu" Daga Mama har Abu-turab kallon Haseenatou su ke. "Yes, duk soyayya ta rufe ku,kun makance kun kasa ganin gaskiya na tabbatar da a hayyacinku ku ke ko da kuɗi aka haɗaku ba zaku taɓa sha'awar aurenta ba, to yanzu baku da mara da wanda su ke turo" ta faɗa rai ɓace domin har ranta bata ƙaunar auren Abu-turab da Majeederh. Ta yi ƙwafa ta ce "Abin da sake an bawa mai kaza kai" Sona da ke tsaye ta riƙe ƙugu ta ce "Abin nema ya samu, matar dan doka ta haifi ɓarawo, ka dai ki ce halin dangin miji ne ya motsa miki?" Kamar Sona na karantar zuciyar Haseenatou, bata da burin daya shige irin Abu-turab ya auri ƴar uwar shi Intisar ta gyara tsaiwa tana kallon Sona ta ce "Aikin banza talaka ya girmi sarki, ina abun yake? Ai da tsohuwar zuma ake magana" "Hankaka mai da ɗan wani naka, na aza cewa kan ki ki kewa farauta, to ai ke kin yi kaɗan kuma Anti Jeederh dashen Allah ce, murucin kan dutse bai fito ba sai daya shirya, kuma ƙaddara bata bar kan kowa ba" har huci Sona ta ke don masifa ta ƙara watsawa Haseenatou harara ta ce "Hannu ɗaya baya ɗaukan jinka, kin yi kaɗan a wannan wasan kina iya komawa ki samo nagartattun ƴan wasa sai a fafata kuma....," "Stop it" Uncle Bello ya faɗa yana nunawa Sona hanyar shiga cikin gida ya ce "Ƴar banza uwar magana,ba ki ɗauka a ƙasa ba" murmushi kawai Uncle Isma'il ya yi domin surutun ƴar ta shi a yau ya yi rana. Almustapha shi ma ya ji daɗin bayanin Haseenatou, Ubangiji ya sa Aliyu zaki ba zai taɓa samun Malama Majeederh ba har abada. Musty ya kada baki ya ce "Idan kaga kare yana sunsuna takalmi ɗauka zai, ba bu rami mai ya kawo rami Allah dai ya kyauta" Hajia ta watsa masa harara. Duk abinda ake Abbu yana ciki bai fito ba, baƙin ciki kamar zuciyarsa zata fito wai yau ƴar shi ta lalace? Take ƙoƙarin lalata masa family?. Ganin yadda duk a kayi shiru kowa yana jimanta al'amarin a ran shi. Uncle Bello ya ce "Ina tunanin mu bar wannan maganar, zamu ƙara zama idan komai ya daidaita" "Ba zai dawo da ita ba" cewar Abu-turab. Uncle Isma'il ya ce "Zai dawo da ita, da hannun daya ɗauketa ka sanya cewa wacce ta haifeka ba zata cutar da kai ba, to Abraham ba zai taɓa iya cutar da Maminsa ba" His Excellency ya dubi Uncle Isma'il, ganin kamar shi ne babba kuma waliyyin Malama Majeederh, ya ce. "Ka bani dama, ka yi mini alfarma a ɗaura auren nan" daga baƙin ƙofa Abbu dake fitowa ya ce "Ni na ce ka auri Majeederh, kuma yanzu na ce kada ka aureta domin zata ɓata maka iri, kuma sam bata dace da kai ba" Abu-turab ya ce "Don't say that Abbu, kayiwa mata uzuri, kuma ka nasan ita alheri ce a gareni" murmushi kawai Abbu ya yi kana ya ce "Allah ya taimaka, ko mene ya faru ka kuka da kan ka" yana faɗin haka ya nufi motarshi, Mami na bin bayansa suka shige ya ja ya rufe. Uncle ganin Abu-turab ya kafe ya ce "Ka je, zuwa dare sai ka zo mu yi magana" "Thank you" "It's my pleasure Your Excellency sauka lafiya" Haseenatou kamar zuciyarta tayi bindiga haka ta shige fuuuu! Ta nufi mota shi na motarshi ya shiga ɗaya daga cikin motocinsa Chevrolet Silverado. Ash colour, dake tafiyar sirri ce ya sa baya buƙatar motar gidan Gwamnati hatta P.a ɗinsa Hammad bai taho da shi ba. Hajia da Papi tare da Almustapha suka ta fi suma gidan ya rage daga Uncle Isma'il sai Uncle Bello da Yaran da suke cikin gidan. Sosai Abraham ya take giyar motar gudu yake ba tare da ganin abin da yake gabansa ba, idanunsa sun yi jajur ta jikin madubin motar ya hango Aliyu dake biye da su. Ya cije leɓe yana girgiza kai a fili ya ce "Fouk You, zan kashe ka" ya ƙara sanya giyar motar shi ma Aliyu ya ƙara gudu cikin sauri Abraham ya yi reverse kamar zai tsaya hakan ya sanya motar shi ta daki da Aliyu ya ƙara yin baya da motar ta sake hankaɗe ta Aliyu kamar zata kifa. Duk yadda ta so share shi ta kame kanta ta kasa ganin da gaske kisan kai ya ke son yi akan Idanunta a gabanta "Meke damunka, zaka kashe shi fa" "And so f****** what?" Ya faɗa yana kallonta, sosai tayi mmkin ganin yadda idanunsa su ka yi bata taɓa ganin hakan ba sai ranar da haura cikin gidan su kowa na barci. Gudu yake sosai tuni ya hankaɗe motar Aliyu,ta firgita ba kanta take ji ba ɗanta take ji ta runtse Idanunta cikin wata kalar murya ta ce "Stop the car, right there" ya yi mata banza. Hannu ɗaya ya sanya ya ɓalle bottle na rigar jininsa da ta yi masa nauyi bai saba saka kaya irin haka ba, yana cire rigar ya cilla ta gidan baya, ya rage sai singlet fara rabin faffaɗan ƙirjinsa a buɗe. Ga Brest ɗin shi kamar wata ma ce jikinsa duk a murmurɗe naman dake arms ɗin shi sai rawa yake. Ya kai giyar motar ƙarshe. "Stop, ka saurara" Ya yi banza da ita, domin ya fara losing mind ɗinsa. Da ƙarfi tana ƙanƙame jikinta ganin sun nufi wani rami ta ce "Don't, listen to me Little" Cak! Ya tsayar da motar dab da ramin tare da kifa kansa a kan sitiyarin motar ya shiga fitar da numfashi mai zafi yana dafe kansa da yake jin kamar zai rabe biyu. Yadda zuciyarta ke harbawa haka ta shi take harbawa, ta rasa me zata ce masa, ta san kuma ba zai taɓa cewa komai ba. Sun ɗauki wasu daƙiƙo zuwa mintinu ni kafin ya ɗaga kan shi. ba tare daya kalleta ba cikin turanci ya ce "Ki shirya mutuwa!" "Wait!" Ta faɗa ya harɗe hannu a ƙirji girman kai biyu sun haɗu, Majeederh ji da kai da nuna isa musamman da take ganin da auren wuri tayi da tuni ta haifi kamar Abraham. Ya sauke numfashi zuciyarsa tayi masa nauyi without looking at her ya ce "Why!" "Shi ne tsarina" "Liar" ya furta ya gyara zama sosai tare da juyawa ya kalleta ya ce "Na ce ki jirani, na jima da bada saƙon haka, mene na cin mutumci haka?"