← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 93

Sashe 40

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"May i knw You?" Cewar Ƙhulud Arzaan Majeederh ta ce "Me zai hana?" Ta gabatar mata da kanta ganin yarinyar nada nutsuwa, Ƙhulud Arzaan ta juya idanu ta ce "Ina mijinki?" "Bani da aure" Majeederh ta faɗa a taƙaice, Ƙhulud Arzaan da bakinta baya shiru ta ce "Oh sorry, kuma Abbanki ya barki barin ƙasarku zuwa wata babu muhrrami? Ba kyau hakan, shi namiji Garkuwa ne" "Nawa Uban da kansa ya tursasani zuwa, ko da zan mutu a nan" Majeederh ta faɗa a zuciyarta tana ƙara karaya da lamarin mahaifinta. Daga nan gabaɗaya babbar mota ce ta sake kwasar su zuwa inda aka tana ta domin su, zuwa wayewar gari kuma za su fara shiga Al-Azhar University. Tana kwance idanunta a sama tunanin rayuwarta da makomarta kawai take na yadda zata iya gabatar da rayuwa a ƙasar Misira babu kowa nata, har dare ya tsala bacci ya kasa ɗaukan idanunta a lokacin kuma ta mance da batun wanda suka haɗu a jirgi. Ta mirgina kaɗan tana riƙe mararta dake mata wani irin murɗawa tsigar jikinta sai tashi take tana zubewa kofofin gashin jikinta duk suka buɗe alamar a shirye suke da karɓar abin da suke buƙata. Ta ƙanƙame jikinta tare da jurewa waje guda tana jin gabaɗaya duniyar na yi mata zafi, al'amarin da take ji ya tsananta ta miƙe tare da tsugunawa tana girgiza kanta a raunace ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangiji ka kawo mini ɗauki, Allah ka dubeni ka kare mini martaba da kimata har zuwa ɗakin mijina idan ina da rabon yin aure idan bani da rabo Ubangiji ka tsare mini imanina ka kare mini budurcina har zuwa sanda raina da ruhina zai dawo gareka" Jikinta duk ƙyarma da ɓari yake ji take kamar ana kwara mata wuta a fatarta mararta ta kumbura, ƙirjinta ya ƙara girma fiye da ƙima tabbacin tana kan buƙatar namiji. Tana nan har ta ji kiran farko na sallar Subhi da sauri ta miƙe tsaye tare da shiga toilet ta sakarwa kanta shower tana sauke wani wahalallan numfashi, ta fito ɗaure da towel duk a tsorace take na rashin sabo. Duguwar riga ta saka ta buɗe fridge ta ɗauki fruits da ruwa da dabino kaɗan ta ci ta sha ruwa sosai kana ta ɗauki niyyar azumi kamar yadda ta saba. Raka'atul fjr ta yi tana zaune Ƙhulud Arzaan ta shigo cikin kyakkyawar shiga ta ce "Zo mu je masallaci" "A masallaci ake sallah?" Ƙhulud Arzaan ta ce "Eh" Ta faɗa ne kawai amma hankalinta duk yana kan fuskar Majeederh bata taɓa ganin zubi da tsarin halitta kamar na Majeederh Abdul'aziz Khan ba, har ta shirya cikin wata abaya ruwan huda idanun Ƙhulud Arzaan akanta ta sanya hijabi mai kyau kana ta saka Liƙab sabo. A hanya Ƙhulud ta ce "Kuma are you sure a Nigeria kike?" "In sha Allah" cewar Majeederh "You look familiar" "Me??" Majeederh ta tambaya domin bata ji ba, Ƙhulud ta watsa hannun ta ce "Mafi mushkila"..... Suna shiga Al-Azhar University Majeederh ta cike komai da komai akai sa a department ɗaya suke da Ƙhulud Arzaan, course ɗin farko Majeederh ta ɗauke komai da komai a kanta domin da gaske karatun ta zo ba wasa ba, burin mahaifinta zata cika har ƙarfe biyar suna cikin makaranta. Abbu ne tsaye a gaban wani mutum ya ce "Maganar gaskiya nake maka, gidana da nake ciki nake so a rushe komai a sauya sabo kafin bikin ƴata Ruma" Alhaji Bashir ya ce "Taya zaka biya?" Abbu ya ce "Ni nake da hanyar biya, mai ƴa kamar Majeederh har a faɗa masa wani abu?" Alhaji Bashir ya yi dariya ya ce "Ƴarka jarinka, to yanzu dai gasky ko zan maka wannan kwangilar sai na ƙara maka kuɗi a ƙalla dubu ɗari biyar akai shi ne ribata, idan kuma ni zaka bani auren yarinyar ma shikenan zai na yi maka haɗaɗɗen gida 200by 200 matsayin sadakinta kaga data dawo sai ayi maganar biki, ko kuma a ɗaura auren idan ya so sai na bita can" Abbu ya yi shiru Alhaji Bashir ya ce "Think about that Malam Abdul'aziz, bayan gida har kyauta zan maka muddin zaka aura mini Majeederh" Abbu ya ce "To a nawa zaka iya bani?" Alhaji Bashir ya zaro takarda ya ce "Faɗi adadin miliyan nawa ka ke so, ni kuma take zan baka zaka tashi daga matsayin Malam ka koma Alhaji" Jikin Abbu na rawa ya ce "Na amince, na amince wallahi zan baka auren Majeederh.....27 Alhaji Bashir ya gyara tsaiwa yana shu'umin murmushi ya ce "Bana ɗaukan asara ba kuma zan fara akan ka ba, ka yarda zaka bani auren yarinyarka Majeederh? Ni kuma na baka dukkan abin da ka ke so?" Abbu bai dugun tunanina ba ya ce "Na baka aurenta ƴata Majeederh halak makal, ko bayan bana raye" Alhji Bashir ya ce "Baka raye to waye zai tashi matsayin shaida?" Ya yi jim kafin ya ce "Allah da Manzonsa su ne shaidar hakan?" Alhaji Bashir ya haɗe fuska ya ce "Na san da haka, amma mutane huɗu shaidu nake so" Abbu ya shiga nazari idan ya ce a'a ya san tabbas zai dauma cikin wannan gidan nasa da baya samun ci-gaba, mafarkinsa na zama wani a duniya ba zai tabbata ba, hanya ɗaya ce wacce ta kasance madafar shi shi ne “Majeederh” Abbu ya ce "Zuwa dare sai ka dawo ni kuma zan haɗa maka shaidun" Alhji Bashir ya ce "Never mind, Allah ya kaimu" Su kai sallama Alhji Bashir ya shiga mota ya tafi, Abbu kuma ya koma gida. Yana shiga ya samu Mami zaune ya nemi waje ya zauna tare da yin shiru yana mamakin abin da ya hana Majeederh kiransa gashi har anyi kwana biyu. "Lafiya?" Ya sauke numfashi ya ce "Ina yaran? Aaliyyah, Raihana, Ruma?" Mami ta ce "Ruma ta tafi raka Imran, Aaliyyah da Raihana sun je gidan Widad" Abbu ya numfasa ya ce "Rumana ta dinga janye jikinta daga yaron nan" "Wanne yaron?" Abbu ya tsareta da idanu babu alamar wasa ta yi saurin cewa "Naga aurenta zai yi shiyasa bana damuwa" Abbu ya ce "Kina da tabbacin haka? Baki san meke ɓoye ba" Mami ta yi saurin cewa "Me ka ke nufi? Bayan shi ya ce yana son ta zai aureta?" Bai ce mata komai ya miƙe ya shiga duba gidansa lungu da saƙo deep down na zuciyarsa yana tunanin wa zai kira matsayin shaidu?... Da daddare misalin ƙarfe tara Latifa Omar na kwance idanunta a sama kewar rashin Aminiyyarta na damunta, ga rashin kiran Aliyu wayarsa ma gabaɗaya a kashe take, she so much loves you ya yi tasiri a zuciyarta sosai. Ta ƙara juyawa idanunta rufe a hankali ta sake jawo wayarta tare da danna kira a number da tayi saving da “Heart choice” Cikin sa a kiran farko ta ji an ɗaga a marairaice cikin damuwa ta ce "Sweetheart" Almustapha ya yi shiru yana gyara zaman wayar a kunnenshi tare da juyawa ya kalli Aliyu dake kwance saman gadon asibiti ya yi mahaukacin ramewa "Hello" Muryar Latifa ta sake dawo da shi hayyacinsa ya ce "Majeederh Abdul'aziz Khan, right?" Latifa ta zaro idanunta waje zuciyarta na bugawa, mene haɗin Aliyu da Majeederh? Ta yi shiru tuna muryar da ta ji kamar bata Aliyu ba, a hankali ta ce "No, Latifa Omar ke magana, Aliyu fa?" Ta yi saurin tambayar hakan cike da bin umarnin zuciya. Almustapha ya ce "Ok, mai wayar yana kwance asibiti" A ruɗe cikin tashin hankali idanunta har ya ciko da hawaye ta ce "Subuhanallahi! Wanne asibiti" Musty ya ce "Aminu Kano" "Am on my way" kafin ta ajjiye wayar ya ce "Amma kamar dare ya yi, da kin bari zuwa safiya" Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce "I can't, ba zan iya bacci bangan shi please" Musty ya ce "Ok, daman daya farka ke ya kira, so na kira ki wayar a kashe shi ne ya ce a nemi Malama Majeederh kuna tare" Ya faɗi hakan yana gyara ɓarnar da ya yi a baya. Daga haka ya yi hanging off. Papa dake jin duka maganganun Musty da Latifa ya ce "Me ya sa kayi mata ƙarya Almustapha Sufyan Alhassan?" Almustapha ya shafa kansa ya ce "Shi ne mafita Papa, zan so a ɗaura auren shi da Latifa in prioud time. "He doesn't like her" cewar Papa. Almustapha ya ce "Yanzu mene amfanin haka Papa? Duk jiya yake kira mana suna ɗaya Majeederh, Hawwy, Hawwa'u, na tambaye shi me ya sa yake son Latifa bayan Majeederh ce a bakinsa?" "Me ya ce?" In ji Papa. "He refused to answers my question" Hajia ta juya kan Aliyu dake jin duk abin da suke faɗa amma idan ka ganshi zaka ɗauka bacci yake, hannunsu dake danne da ƙirjinsa kawai ke motsawa dalili bugawar da zuciyarsa ke yi. "Me ya sa Zaki?" Ya buɗe gajiyayyun idanunsa da sukai jajur kamar ba zai magana ba har Hajia ta ƙara cewa "Meke faruwa ne?" Ya yi saurin riƙe hannun Hajia ya ce "Ban sani ba, Amma ina sonta a gefena" "Aurenta za ka yi?" Hajia ta tambaya tana riƙe nasa hannun. "A duk sanda na ji ina son aurenta sai na ji na tsaneta, amma idan na cire batun auren sai na ji babu wacce nake son gani sai Majeederh, i want to see by my side, ko sunanta na ji zuciyata bugawa take don Allah ki taimaka mini Hajia please" Papa ya yi zuru yana ganin ikon Allah, wani abu mai kama da almara. Bai taɓa ganin hakan ba, ko a film na hausa, Indian movie ko series balle novels, ace wacce mutum ke son aura daban wacce kuma take zuciyarsa daban "Ikon Allah" Cewar Papa Hajia ta ce "Ikon gaske, Yanzu me ka keso" Cikin sauri Aliyu ya ce "Majeederh na keson gani Hajia please" Hajia ta zabga tagumi Idanunta jajur alama ta jima tana kuka domin tun jiya Aliyu bai san inda kansa yake ba sai yanzu, Papa ya sauke numfashi cike da jimamin al'amarin da kuma tausayin ɗan nasa ya ce "Zan nema maka auren ita Majeederh a wajan Mahaifinta idan ka amince, kada ka sanwaltar da rayuwarka akan ta" Aliyu ya girgiza kai ya ce "Ba aurenta zan ba" Almustapha dake tsaye harɗe da hannu ya ce "Ok ita Teddy
Chapter 40 · 0% Book details