Sashe 70
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
bashi address na gidana anjima ya zo ya saman" Ta yi shiru ita yanzu ina zata sake ganinsa ma? Uncle Isma'il ya ce "Kin ji ko?" A hankali ta ce "Bani da Digits nasa, kuma Abbu ya hanani fita" Uncle Isma'il ya ce "Akan me kuma? Aikin naki fa?" Ta ce "Wai na fito da miji immediately cikin 2days" Cikin ɓacin rai Uncle Isma'il ya ce "To ya garƙame ki a gida tayaya zaki samu mijin? Ko akwai wanda kuke dating da shi ne?" Cike da takaici da ɗacin rai ta girgiza kai ta ce "A'a" Uncle ya ce "Kina kina gida a garƙamen zaki samu mijin aure? Ko shi ne zai nemo miki mijin ne eh?" Uncle Isma'il ya saki tsaki ya ce "Abdul'aziz baya kyautawa kansa kuma kema baki kyautawa kanki ba, ai ba mijin aure kika rasa ba" Yana faɗin hakan ya kashe wayar rai ɓace. Majeederh ta kifa kanta akan pillow tana jin zuciyarta kamar tayi bindiga damuwa ta mata yawa, ita yanzu ina zata samu mijin aure? Waye zai aureta? Wama take da shi ita wallahi bata taɓa soyayya bama bata san ya take ba, daɗinta da wahalar cikinta duka bata sani ba, amma zo da nufin yaudararta babu wanda ya taɓa, ita ko gurgu ko tsoho ne ya zo da nufin aurenta wallahi da gudu zata amince masa ta gaji over gajiya rayuwarta a jirkice take gabaɗaya, ƙaddarar rayuwa ta sanya ta ciki tsaka mai wuya, rana zafi inuwa ƙona, a dangi a goranta mata rashin aure, a gidan da aka haifeta wanda take jin tana da ƴanci nan ma haka, few people suke supporting nata always. Miƙewa ta yi da nufin shiga bathroom idanunta ya sauka akan Card ɗinsa wanda da gayya ya ajjiye ta dauki card ɗin dake ta sheƙi taga an rubuta Dr. Abraham Denial David, so da gaske dai likita ne shi? How? Ita kam ta raina shekarunsa da zama likita, number ta gani uku ta ƙasashe daban-daban ta dubi ta Nigeria taga ganta special one domin kusan duk digit ɗin 1 ne. Ta saka number ta yi saving da _Son My world_ Kira ta yi lokacin Abraham na zaune cikin garden na gidan su idanunsa kwance a saman tsuntsayen da suke yawo wajan, a hankali yake kaɗa ƙafarsa wacce take cikin ruwa hannunsu riƙe da coke yana sha da kuma shisha gabansa. Wani cool ring tone ya shiga tashi kai tsaye ya fahimci me kira, tun ɗazo Gang team ke kiransa amma yaƙi ɗagawa, ya ɗaga kiran yana mannawa a kunne yana jin sanda ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Uncle Isma'il na kiranka, check your inbox za kaga address ɗin gidan nasa" Tana faɗin hakan ta kashe kiran yasan haushin Allura ne dai bata shige ba. Ya cije lip's yana shafa sumar ƙirjinsa yana gani ta yi mata Dm na address ɗin gidan a hankali cikin ƙasa da murya kamar shi ma da kansa bai son jin maganar shi ya ce "Mamina mai tsoran allura"..... Innati ta ƙanƙance idanunta tana kallon Mami zuwanta gidan kenan ita da Maman Alpha sbd acan Innati take da zama ta dubeta ta ce "Ke baki isa ba, bana buƙatar lalatacciyar munafukar gaisuwarki, mijinki nake nema maza kira shi" Mami ta ce "Kiyi haƙuri Innati" Innati ta yi shiru ta juya wajan Maman Alpha ta ce "Ai ka ji tsiyar da Maryama ce uban me zai sanya tayi shiru? Kin zo kin jaɓe kamar kayan wanki" Maman Alpha dai ta yi shiru babu jimawa Abbu ya fito cikin wata dakakkiyar shadda shampo sai ɗaukan idanu take ya tsuguna ya ce "Sannu da zuwa Innati, anzo lafiya?" Innati ta yi mitsi mitsi da idanu ta ce "Kai bayan son zuciya ta hakƙin lafiyayyiyar ƴarka mai zuciya mai kyau, hadda bakin uwa ke binka Audil azizu" Abbu ya ce "Subuhanallahi me na yi?" Kamar zata dage shi ta ce "Me kowa na ce kayi? Cewa na yi bari na zo na ji wanne marar tsoran Allan ne yake rusawa yarinya farin cikinta? A wanne dalilin ka hanata fita aiki? Kuma da zaka karkace ɗuwawu bayan ta tara maka arziƙi ka ce cikin kwana biyu ta nemo mijin aure, ita ƴar bori ce ko aiki da ruhainai da zasu bata mijin aure?" Abbu ya ce "Ni Majeederh ta tarawa arziƙi? Duk faɗi tashin da nake har Ubangiji ya dafa mini? Kuma sbd kare mutuncin kanta na ce ta fito da mijin aure, shekaru 31 banda ita wa kike gani a family bashi da Aure? Sai fa Sona da Aaliyyah, ka kaf area ɗin nan namu babu mai shekarunta sai dai kullum ta yi wanka ta saka kaya ta shiga mota ta tafi aiki? Ba batun aure a ranta ta mayar da kanta tamkar namiji sbd gogagawa da take da su ta zama kamar wata feminist sai dai ta bawa wasu shawarar zama gidan miji da yadda za su yi haƙuri da rayuwar aure amma ita tana zaune gabanmu tana haɗa kafaɗa da uwarta?" Innati ta ce "Ka gama?" Ya yi shiru ta gyara zama tana saka hannu a ƙirji ta fito da yagulallen nono duk a bushe ta ce "Me ya wannan Audil azizu?" Ya saurin cewa "Don Allah Innati ki yi haƙuri Please" Ta girgiza kai ta ce "Ni fa ƴar banza ce, shiru dai kawai nake bance komai ba, idan kana jin kai ka haifi Kululu to ni kuma ni na haifeka ina umartarka daka gaggauta janye sharaɗin ka akan ta, ko kawai na saki nonon ya faɗi ƙasa kasan me hakan ke nufi" Abbu ya ce "In sha Allah" Ta ce "Maza kirata, ai ba wani yaƙunanne bane ya tara arziƙin gidan" Abbu ya ce "Asabe kirata" Mami ta miƙe tare da nufar part ɗin Majeederh not too long suka dawo tare, ta yi wanka ta shirya cikin wata designer ɗin Abaya mai kyau da tsada tayi rolling kanta kyanta ya bayyana idanunta ya faɗa kamar Balarabiya. Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Ta tsuguna ta gaida Maman Alpha da Innati da kuma Abbu bai amsa ba ya ce "Ki koma aiki" Innati ta ce "A'a daman waye ya sanya ta fara aikin ba kai ba, cewa za ka yi ka janye maganar miji ta nemo a nutse ba tashin hankali" Ya faɗi yadda ta ce Majeederh ta ce "Na gode Abbu" Fita ya yi Innati ta bisa da idanu ta ce "Yanzu ma jin kansa yake wani ɗan iskan me kuɗi ne, rabon daya taka ya je ya gaidani anfi shekara Ashirin wallahi tallahi" Maman Alpha ta ce "Shi ne ina ta kiranki shiru ko Majeederh?" Ta sunkuyar da kai ta ce "Zan zo In sha Allah" Sun jima kana sukai sallama... Yau tunda ta tashi da ciwon mara a hankali take duba lokacin tana jiran zuwan Latifa kafin ta shige B.u.k Allah yasa yau ba mutane a office ɗin nata tana zaune saman duguwar kujera zufa na yanko mata, ta saka hannu ta riƙe wajan dake mata ciwo daidai mara duk iya yadda takai ga dauriya ta kasa jure zafin ciwon jikinta ɓari yake, hannu ta kai da nufin ɗakko wayarta ta faɗo daga kujerar ta kwanta saman carpet rolling ɗin kanta ya cire yalwatacciyyar sumarta tayi ɗaiɗai a saman carpet ɗin sbd zamewar ribbon kanta, kiran sunan Allah kawai take domin ta gama fidda ran mutuwa ma za ta yi idanunta har ya fara ɗaukewa sai fari, shigowarsa cikin office ɗin ya yi daidai da sarƙewar numfashinta a rikice ya ƙarasa shiga ciki yana cillar da wayarsa yana zuwa ya zube a ƙasan carpet ɗin duk da kyan kayan jikinsa da ƙamshin dake ta shi yana zuwa ya saka hannu ya ɗagota zuwa jikinsa gashin kanta na rufe masa fuska ya shiga girgizata ya kasa cewa komai, can ta ja numfashi jinta a jikin mutum yasa ta fashe da kuka Majeederh bata ƙaunar ciwo ko kaɗan balle wannan ciwon cikin da take jin kamar ta mutu bata taɓa jin irinsa ba, ta ƙanƙame wanda take jikinsa sosai a hankali muryarsa na fita da ƙyar ya ce "Sorry, meke miki ciwo?" Ta kasa bashi ba tare data san waye ba sbd bata hayyacinta ta kama hannunsa da manna a mararta ta ce "Zan mutu, ciwo wayyo" Ya yi shiru yana jin kansa na sarawa tsigar jikinsa na tashi ta ƙara danna hannunsa a marar ta ce "Ka danna mini....