Sashe 81
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zan aureka? Kalleka U just 16 yrs, gwanini da kai kake cewa zaka aureni? Kai tsakani da Allah baka ji kunya?" Ta gyara tsaiwa ta ce "I understood, baka son ganina babu aure ne? To i promise you zan fito da mijin aure ka ji Yarona, kabar maganar u still be my son my baby" Abraham she dry ba ta bashi magana take amma bakinta rawa yake inda take kalla kuma da ban. A hankali ya taka har inda take tsaye ya ɗan leƙa fuskarta tayi saurin rufe Idanu ya taɓe baki numfashinsu na haɗiye can ƙasa daga shi sai ita ya ce "I want you Jee, i want to you to be in my side, Ina son ka ƴar madara" Ta watsa masa harara ta ce "Har abada, ƙuruciya ke damunka" Hannu ya miƙa zai riƙeta ta yi saurin yin baya ta ce "Is prohibited in my religion" baya ya ja kaɗan yana ɗaga mata hannu a taushashe ya ce "Ohk, Your religion is difficult" Ya ɗan shafa kansa yana maida hannunsa baya a shagwaɓe ya ce "Marry me, I'll give u all the happiness in our life" Majeederh ta yi shiru, wannan kamar wani opportunity ne na gyara Abraham zuwa yadda take so, zata gyara masa rayuwarsa da tarbiyya da komai. Murmushi ta yi ta ce "Khalil" Calmly ya ce "Maa" Kujera ta nuna masa, ya miƙa hannu zai riƙe ta ta ƙara janye wa ta haɗe fuska. Zama ta yi saman kujera, shi kuma ya nufi wajan fridge ya buɗe ya ɗauki Favorite juice ɗinsa da apples guda biyu, gently ya juya ya ce "Maa i need food" Ta yi masa shiru har ya gama kwasu komai, ya dawo ya zauna ya ɓalle murfin lemon idanunsa lumshe yake ɗan sha yana ya mutsa fuska he lost his appetite. "Who are you, Ibrahim?" Sosai ya jita ya basar ya ce "Yunwa ina ji" Ta ce "Ibrahim-Khalil" Ya zuba mata idanu sosai ta ce "Who are you? Where are you coming from? Me kke ɓoyewa?" Shortly ya ce "hiding?" Ya girgiza kai ya ce "Jesus" Ta numfasa cikin dabara ta ce "Ka taɓa ganin ayi aure ba a san mutum ba? Iyaye family e.t.c?" A hankali ya ce "Me kike son sani a kaina?" Ta ce "Ur Father, country da sunan mahaifiya" Murmushi kawai taga ya yi, tare da yin baya ya kwantar da kansa yana rufe idanun, bottle ɗin hannunsa ya matse nan take ta fashe juice ɗin ya zube hannunsa ya fara zubar da jini. "Khalil" ya yi mata shiru tana danne tsoranta ta ce "Abraham" Idanunsa ya buɗe tare da zuba mata su, wani irin ja taga yayi wanda bata taɓa ganinsa ba, a nan kuma ta ƙara tabbar da zuciyarsa rauninsa kuma iyayensa. Murmushi taga ya sake yi wanda ya fito da kyansa duk da baya yanayi na jin daɗi cikin sauyin murya ta ji ya ce "Mother? Uhm" A hankali ya sunkuyar da kansa ya ce "I don't know her, ban santa ba, she's alive or not I don't know" Kallonsa kawai take a hankali ya sake cewa "Idan an ce uwa ke nake kallo, kece mace ta farko data kula dani ta nuna mini soyayya ta uwa, wacce na rayuwa da wannan soyayyar har yanzu, Bayanke maza ne kawai suke tare dani Gang team ɗin nan su ne ahhalina, ina da 10yrs na gama secondary school na fara University a wata ƙasa" Ya yi shiru ta ce "Wacce ƙasa?" Calmly ya ce "Germany" Ta ce "Ohk ina jinka" Ya ƙara lumshe idanunsa wanda duk suka rine ya ce "Daga nan na sauya University, har dai na kammala" Ta jinjina kai ta ce "Ur Father?? Mahaifinka fa?" Ya ce "I hate him" Da mamaki ta ce "Why? Me ya sa me ya yi maka?" Murmushi kawai ya yi yaƙi ce mata komai. Ta ce "Ok Shi ne ya biya maka kuɗin makaranta?" A nan ya yi wata kalar dry sosai yana girgiza ya ce "Funny, ina yaga kuɗin kai ni Germany? Kuma Karatun Likitanci, Welder fa yake" shi kansa ya san ya yaudari kansa sai ya ji kansa ya masa girma na ƙaryar da ya yi. Majeederh ta ce "Kuma ina kai kke samun kuɗi? Me haɗinka da Gang team ɗin nan?" Ƙuri ya yi mata da idanu ta ji ya saki dry ya ce "you're asking too much, are you trying to change me? use your chance on me" Ya ƙara yin murmushi kawai idanunsa jajur jijiyoyin kansa duk sun fito kallo zakai masa kasan ba daɗin hirar yake ji ba, ya watsa hannunsa tare da cusa yatsunsa cikin suma ya birkitata ya zuba idanu ya ce "You can because I love you, kawai dai Gang team is my happiness in bani da lafiya sune, suke iya ɗaukan haukana" Idanunta ta ji ya ciko da hawaye sbd tausayinsa ya yi kamar bai gani ba ya ce "Me kike so?" Ta ce "Bana son Debeka" Da wani irin sauri ya ɗago ya kalleta bai ce komai ba, ta ce "Bana son Shaye-shaye, yawon banza, kula matan banza, bana son faɗa da kowa ka koyi controlling kanka, kana zuwa wajan mahaifinka bana son gajeren wando ka maida hankali akan sana'arka, idan ba wani doke ba bana son shiga cikin Gang team ɗin nan" Tunda ta fara magana yake kallon bakinta da idanunta ta ce "Kana jina?" Calmly ya ce "Ohk" A wannan karan da ƙyar muryarsa take fita ta miƙe tsaye zata ta fi ya bita da idanu ya saka remote ya cire password sai da ta je bakin ƙofa ta ji ya ce "Zan aureki dole, Abraham baya ƙarya" Da sauri ta fice daga cikin gidan tana sauke numfashi. Akan idanun Bar Aliyu ta fito da sauri ta shiga motarta tare da yin key, dake ya sauya mota bata sani ba, kuma bata hayyacinta hakan yasa sam bata gansa ba. Kifa kansa ya yi a kan hannun motar yana jin zuciyarsa kamar ta fito gabaɗaya ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa, he want Majeederh in his whole life, amma tsoranta yake sauya masa take a ko wanne lokaci, duk sanda ya yi attempting faɗa mata he loves her sai yaga kamar ba ita ba, nan da nan ransa ya ɓaci. He couldn't sleep, eat, everything komai nasa ya tsaya ya yi asarar contract da yawan gaske. Failing a Shari'a ba a magana. A hankali ya kunna motarshi kai tsaye gidansu ya nufa, lokacin Hajia da Almustapha na zauna a parlour. Tunda ya shigo Hajia ke Kallonsa har ya nemi waje ya zauna yana mai da numfashi ta kasa daurewa ta ce "Aliyu lafiya?" Ba tare daya buɗe ido ba ya ce "Good, ina yini Hajia?" Ta yi shiru ta kasa amsawa. Wayarta ta ɗauka ta kira Dije ta ce "Ki haɗawa Babana abinci yanzu" Dije ta ce "Done Hajia" Ta ɗauke kallonta ga Aliyu ta ce "Almustapha ya matar taka?" Ya ce "Da tare zamu zo ma, bata jin daɗi ne" Ta ce "Ohk, Allah ya sauwaƙe" Ya ɗan juya ya ce "Papa fa?" A nutse ta ce "Ya je meeting, kasan an fara shirye-shiryen tsayar da ɗan takara" El ya ce "Kai, Shi Papa mene haɗin sa da wani takara ne, ban son ya tsaya wata siyasa wlh" Ta yi Murmushi kawai El ya ƙara cewa "Ohk i understand, jam'iyyar su ai ke kan mulki a yanzu, baya so mulki ya fita daga hannunsu" Almustapha ya yi dry ya ce "Kuma wallahi na ji jam'iyyar hamayya da ƙarfinta ta fito, suna da ƴan takarkaru har biyu dole sai sun yi primary election zaɓen cikin gida kafin fitar da gwani, amma da ina zaɓe Abuturab zan zaɓa, he's a kind of person that i have never seen before, a dai ƴan siyar nan tamu, ya taɓa neman takarar ko house of representatives or assembly na manta, yanzu na kamar ya yi aure wai, amma baya ƙasar jinya yake" Aliyu zancen ya ji yana hawa kansa haka kurum kuma Abuturab ɗin bai masa ba. Hajia ta ce "To Aku, duk ina kake jin wannan labaran?" Almustapha ya ce "Hajia media, a twitter a nan nake ganin latest news na ƴan takarkaru, musamman wanda suka ke viral suna trending in the world" Almustapha ya ce "Kuma ƙyakƙyawa da shi so Masha Allah" Sai a lokacin Aliyu ya buɗe ido tare da kallon Almustapha ya ce "To kai mace ne? Da zaka na description kyan ɗan uwanka namiji?" El ya ce "Kai ban taɓa cewa kana da kyau bane? Idan kaga abu mai kyau ka yaba shi ne kawai, day before yesterday na je gidanka ai" A tsorace Aliyu ya ce "But baka faɗa mini ba?" Almustapha ya dinga kallon Aliyu, shi kuma Aliyu tsoro da kunya ya kama shi "Na je, matarka ta iya girki sosai fa, na ganta tare da wata kamar munafuka mai liƙab" Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke, Majeederh ce ta yi girkin. Suna zaune Dija ta kawo Hajia ta saka Aliyu a gaba sai gashi ya tashi da abincin cikin babban plate Kallonsa kawai take tayi tambayar duniya ya ce "lafiya".... Abuturab na zaune feeling better gabaɗaya kwanan shi biyu da dawowa ƙasar daga Switzerland. Idanunsa ya buɗe da ƙyar jin Maysoon na cewa "Ka fita duba lafiyarka, ka dawo and you're still sick wai meke damunka ne Yallaɓai? Ina ta ƙoƙarin ganin na kyautata zamana da kai but i couldn't, ka hana ni duk wata dama da zan kafa soyayyata a zuciyarka" Hawaye na zubu mata hannunta dafe da cikinta wata tara ta ce "Nasan baka so na, amma ni ina son ka, bani da tabbacin zan haife cikin nan lafiya, inma mu mutu tare inma na mutu na barsa ko ya mutu ya barni, don Allah ka nuna mini soyayya a kwanakin nan kafin cikar EDD ɗina na roƙeƙa Haydar" Kuka Maysoon ta saki sosai tana dafe cikinta, Abuturab ya zuba mata Idanu a hankali ya miƙa mata hannu ya ce "Come" Ta ƙarasa ya zaunar da ita saman cinyarsa idanunsa akanta ya riƙo fuskarta ya ce "Maysoon" Tana kuka ta ce "Sir" Ya ce "Ina da ƙulafuci ina da naci, zuciyata nada kafiya akan abinda take so,ki yi mini uzuri ki amsheni a yadda nake, first