← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 93

Sashe 47

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Misalin 12:30 na dare Majeederh da Aaliyyah na zaune saman gado Aaliyah ta ce "Bayan tafiyarki babu jimawa Abbu ya ce za a rushe wancan gidan namu a yi sabo, ya ce kuÉ—i ya samu sama da miliyan biyar, ni dai ban ce komai ba ban kuma nemi sani ba, sbd i don't have any business with that, kuma ubanwa ya bani ikon tambayar inda ya samu kuÉ—in ma? Muka tattara gabaÉ—aya muka koma Gidan Uncle Isma'il Mami Kuma da Ruma suka tafi can dangin Mami, ba a É—auki lokaci ba aka gina gida haÉ—aÉ—É—e aka dinga surutu a unguwa ina Abbu ya samu kuÉ—i shi ba sana'a ba?? Ya yi burus dai a lokacin akai bikin Ruma da Imran sai Raihana......,"
"Amma na gansu gida?" Majeederh ta katse Aaliyah da faɗin hakan ta ce "I have no idea, amma idan suka zo gida sai su yi wata gudu wai mazajan nasu basa gari" Majeederh bata ce komai ba, Aaliyah ta ɗora da cewa "Daga nan kuma Abbu ya buɗe shago a kantin kwari ya zuba kaya da yara masu kula da komai, ya ɗinka sutturu kamar yaƙi, lokacin da kika samu nasara a Misira da bayan wata huɗu ya ce gabaɗaya tashi za mu yi daga gidan nan zamu koma Lodge Road, haka muka koma bamu da wani option, shekarunki uku da tafiya akai bikin Anti Latifa" Majeederh ta waro idanu waje cike da mamaki sosai kafin ta yi magana Aaliyah ta ce "Wallahi anyi bikin bayan jinyar da Yaya Aliyu ya yi a ƙasar waje tsayin shekaru biyu, to bayan ya dawo akai bikin" Majeederh ta sauke numfashi ta ce "Ikon Allah, ina aka kaita?"...... "Gata nan kusa damu, ita ce neighbor namu fa" Majeederh kamar ƙaramar yarinya tai zuru ta ce "How?" Aaliyah ta ce "Good, bamu san mene ya faru ba daman akwai gida kusa damu dake duk kusan gidan haya ne na masu kuɗi kawai sai mu kaga ana fara gyara, daga nan ne Latifa take cewa Aliyu ne ya ce nan zai zauna yafi kusa da wajan aikinsa, ana yin bikin ya ta tare, amma a ranar auren ana ɗaura auren Aliyu ya tafi Cairo ƙaro karatu maganar da nake jiya ya dawo cikin dare" A gajarce Majeederh ta ce "Allah ya sa albarka, ke fa?" Aaliyah ta zaro idanu ta ce "Tab ai nayi al'ƙawari sai kin yi aure zan yi" Majeederh bata ce komai ba ta yi shiru da sauri ta ce "Abbu bai dawo ba?" Ta ce "Kai ai tun 7 ya shigo gida, baku gaisa ba?" Majeederh ta yi shiru kawai.
"Na manta ban faɗa miki ba" Aaliyah ta gyara zama ta ce "Bro Alpha an ƙara masa matsayi daga Captain zuwa General" Majeederh ta ce "Ma sha Allah, Allah ya riƙa" Daga nan Aaliyah ta nufi ɗakinta ba don ta so ba.
A hankali Majeederh ta miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabi hankalinta yana kan Abbu shi kawai take son gani, taga ya mahaifin nata yake? Kai tsaye part ɗin da aka nuna mata aka ce shi ne nashi ta nufa, sosai part ɗin ya haɗu iya haɗuwa gashi parlourn farko ta gansa buɗe da dinga kallon komai cike da sha'awa da mmki, ganin baya parlourn ta shiga wata ƙofa da zai kai ta ɗaya parlourn wanda daga shi sai bedroom, ta tsaya cak tare da yin knocking ta ɗauki good 10 minutes tana knocking kafin cikin faɗa aka ce "Who is there?"
"Majeederh ce, Abbu"
Abbu ya maimaita "Majeederh?" Ta ce "Eh" muryarta duk rawa take gefe guda kuma farin ciki take zata saka mahaifinta a Idanunta can ta ji ya ce "To ya akai?" Sosai tambayar ta bata mamaki da tsoro ta ce "A'a daman tunda na dawo ban ganka ba, ina ta duba ka ina so mu gaisa" Daga cikin parlourn Abbu yana zaune saman lallausan kujera watching TV hannunsa riƙe da cup yana shan black tea ya ce "Ok bani da lokaci zuwa safiya" Majeederh kamar zata zunduma ihu sbd abin da ya tsaya mata cikin rauni ta ce "Please naga kowa banda kai, shekara 8 ban ganka ba" A ɗan hassale ya ce "Ok na bar abinda nake na fito ki ganni kenan ko Hawwa'u? Bani na ce ki bari sai safiya ba, ni ma ina da buƙatar ganin naki" A sanyaye ta ce "Kayi haƙuri" Tana faɗin hakan ta nufi part ɗinta. Waje ta nema ta zauna a saman bed tana cusa hannunta a tsakanin cinyoyinta tare da yin shiru tana girgiza ƙafa, ita kanta ba zata iya cewa ga abinda take tunani ba.....
Washegari misalin 7 na safe Majeederh ta fito tana mustsike idanu sbd baccin daya É—auketa bayan sallar asuba, ta ci karo da Mami ta ce "Ina kwana?" Mami ta kalleta sosai ta ce "lafiya, me ya samu idanun naki?" Majeederh ta É—an yatsuna fuska ta ce "Sometimes ya yi ta mini zafi, wani lokaci kuma ban fiya gani ba musamman duhu" Mami ta ce "Kuma Kinga Dr?"
"Eh" Ta bawa Mami amsa a gajarce, Mami ta ce "Result?" Majeederh ta kalli Mami da idanunta ya fara yin ja ta ce "Wai yawan karatu da nake hasken littafi dana computer wajan Research, amma an bani medical Glasses bayan an yanka daidai idanuna sai drugs" Cikin damuwa da alhini Mami ta ce "Subuhanallahi, Allah ya sauwaƙe yanzu dai sai ki haƙura da wasu abubuwan ki huta sosai ki rage duba wayar ko?" Ta jinjina kai a sanyaye kamar jin tsoro ta ce "Abbu fa?" Mami ta ce "Ai tun 6 ya fita wai yana da appointment da wani" Sai duk jikinta ya yi sanyi ta juya zuwa bedroom. Wajan 12 tana zaune wayarta data saka line ɗin Nigeria ya fara ƙara, ganin sunan Latifa Omar ya sa ta ɗan yi cute smile tana answering "Amarya" Latifa Omar ta ce "Ke dilla wacce amarya, ai mun zama tsofaffin hannu" Majeederh bata ce komai ba "Ya hanya? Da Misira da kuma baƙunta?" A taushashe ta ce "Allahamdulillah" Latifa Omar ta ce "Please ki zo mana, ni ban tambayi Sweetheart ba, kuma he alrdy left" Majeederh kamar bata gane ba ta ce "Nazo ina?"
"Wallahi kin gane" Ta yi shiru, Aliyu dake zaune a kujerar dake facing Latifa ya yi mata nuni da hannu ta cewa Majeederh bata jin daɗi ne da tuni ta shigo don Allah ita ta zo, Latifa ta kanne masa idanu ta ce "An gama Sweetheart" Majeederh ta ce "Me?"Latifa ta yi saurin rufe baki ta ce "Wallahi bani da Lafiya ne da tuni na shigo kema ai kinsan ba zan iya jira har haka ba, shekaru takwas ba kwana takwas ba" Majeederh ta ce "Ok" Tana ta zaune sai da ta yi sallar zhur kana ta yi wanka ta shirya cikin abaya ruwan toka tayi rolling kana ta saka Liƙab ta nufi fita daga cikin gidan, mai gadi jikinsa na rawa ya dinga gaida Majeederh murmushi kawai take masa, tana fita ta nufi gate ɗin gidan da akace na Latifa ne. Latifa Omar duk a hargitse take ta shiga gyara parlourn cikin sauri tana fesa air-condition Aliyu dai na zaune cike da mmki yana binta da kallo, yana ƙoƙarin magana ya ji knocking Aliyu ya saka hannu ya danne saitin zuciyarsa yadda take bugawa da ƙarfi ya san cewa ita ce, tabbas Majeederh ce "In"
Ya ce, ta murɗa handle ta shigo cikin sassanyar muryarta mai tasiri a zuciyarsa tana ƙarasa shigowa yana miƙewa tsaye ya zuba duka hannu a aljihu idanunsa kafe a kanta da ɗan sassarfa cikin sauri ya nufi inda take tsaye hakan yasa ta gwalo ido tare da haɗe fuska...

Ƙilan sai bayan sallah🤓 Idan Allah ya saka mini shauƙi kuma ku gani gobe, a samu masu kawo mini naman sallah da barka da sallah domin za ni ƙasa mai tsarki na roƙawa Abbu ya fiyar Ubangiji Allah ya shirya ya ɗangwalawa zuciyarsa tausayin Jeena🙁.... Masu karantawa As free common baby an daina yayin haka ki waye ki biya a saka ki grp albarkacin wannan ranar🙏🏿
Chapter 47 · 0% Book details