Sashe 48
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah ya amshi tubanmu, ya gafartama ya kyauta makwancin wanda suka gabace mu😪 0811923761631 Aliyu na zuwa ya bi ta gefenta ya shige da sauri, a hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana ɗan juya idanunta, fita ya yi waje can wajan mai gadi ya nemi waje ya zauna yana riƙe kansa. Ayuba ya ce "Yallaɓai lafiya? Yau kai ne zaune a nan?" Aliyu ya kasa cewa komai sai numfashi da yake saukewa, lokacin da idanunsa ya sauka akanta tunaninsa ne ya tsaya, amma yana ƙarasawa inda take sai yaga ta rikiɗe masa. "Yallaɓai" Maganar Ayuba ta dawo da Aliyu ya yi saurin ware idanu a hankali ya ce "Ka ce me?" "Na ganka a firgice, kamar baka cikin nutsuwarka?" Aliyu ya shafa kansa yana mai miƙewa tsaye hannunsa zube cikin Aljihu ya ce "No...." "Ka tabbata?" Cewar Mai gadin Aliyu ya girgiza kai ya ce "Goodness, lafiya nake" Ayuba ya washe baki ya ce "To... To ma sha Allah, ai yanzu naga magidanciya ta shige wallahi nutsastsiyya da ita kana ganin idanunta kaga Balarabiya amma ta bani tsoro kamar mai idanun maciji ko mage" A ɗan hargitse Aliyu ya dubi mai gadin nasa ya ce "Okay daman sa idanu kake zama yi ba gadi ba? Har kake description ɗin how beauty she's?" Mai gadin ya zaro idanu ya ce "Kwarankwatsa ba saka idanu nake ba" "Ok munafurci ne?" Aliyu ya faɗa yana saita kansa domin nan da nan ya ji ransa ya ɓaci, shi dai Ayuba bai ce komai ba. "This is the first and last time da zaka ke sakawa mace idanu more especially ita" Ayuba ya gwalo idanu ya ce "Yallaɓai da dai kayi mini da Hausa, wallahi ban ji komai ba banda ok, Daƙiƙe ne ni na ajin ƙarshe" Aliyu bashi da mood ɗin yin dariya. Rai ɓace ya ce "Ai kowa naga alama, ka tabbatar ka iya turanci domin I will not live with an uneducated and poor person in my house" Ayuba ya ce "Turanci fa kace?" Ayuba ya ƙara dafe ƙirji ya ce "Turanci? Dai irin wanda na ji kana yi to wallahi ko A..B..C sai na yi da gaske zan iya, ni dai ka rufa mini asiri" Aliyu dai bai sake furta komai ba ya juya zuwa garden na gidan.... Majeederh ta ɗan buɗe idanu akan Latifa ta ce "Ba dai a haka kike zaune ba?" Da alamar rashin fahimta Latifa ta ce "Kamar yaya kenan?" Majeederh ta kalli jikin Latifa tas, kaya ne haɗin bauta riga daban zani daban haka ɗan kwalin daban ta ce "Ina nufin haka" Ta faɗa tana nuna mata shigar jikinta, Latifa ta yi saroro sai kuma ta ce "Oh don mind me, zuwa anjima zan shirya kin san na ce miki bana jin daɗi" A taƙaice Majeederh ta ce "Allah ya bada lafiya" Ta miƙe tsaye tana mayar da liƙab Latifa ta ce "Meye haka to kamar kurarriyya? Ba dai tafiya ba?" Majeederh dai ba tayi magana ba tana ƙoƙarin fita Aliyu yana shigowa bakinsa ɗauke da sallama. Ya kalli Latifa ya ce "Baƙuwa ki kai ne?" Ta ce "Baka nan ta shigo ne?" Ya ɗan ɗaga kafaɗa ya ce "Am in the garden" Ya nemi waje ya zauna idanunsa akan Majeederh kaɗan, Latifa tayi dry ta ce "Nikam how long ka ɗauka ba kaga bestie ba?" A takaice ya ce "I can't remember." Latifa ta zauna kusa da shi "8yrs going to 9 fa, tunda yanzu muna end of the year ne, gasky yau ya kamata ayi hirar yaushe gamo" Sosai Majeederh ta fahimci daga matar har mijin neman magana suke. Aliyu ya ce "Bestienmu ina yini?" A cikin nutsuwa a takaice ta ce "Allhamd, ya jiki?" "Sai godiyar Ubangiji jiki" Bata sake cewa komai ba ya juya kan Latifa ya ce "Wife yunwa ina ji sosai, wallahi kamar zan ci babu" Yadda ya langwaɓe kai da yanayin daya nuna yunwar yake ji da gaske kuma bashi da haƙuri akanta ya sanya Majeederh lumshe idanunta tunanin Little ya faɗo mata, ko yana raye ko ya mutu ko yana wacce duniya? Sai ta ji zuciyarta ta karaya ƙafarta tayi sanyi. Latifa Omar ta ce "Bestie taimakawa sweetheart da Superghetti" "What?" Majeederh ta faɗa lokacin da maganar Latifa ya dawo da ita daga tunanin Ɗanta Little. "Kinga bana jin daɗi, warin gas hawar mini ka yake ki taimaka please ki dafawa Sweetheart wani abu" Majeederh ta zare idanu har sai dai Aliyu ya ɗan sauke numfashi kamar ba zatai magana ba sai kuma ta ce "Amma kin san am not your maid?" "Mun sani" Aliyu ya ce "Don Allah, please Bestie me" Latifa ta faɗa a marairaice. Tasan weakness na Majeederh da zarar ka haɗata da Allah magana ta ƙare, Majeederh ta ja gajeren tsaki kamar wacce akai forcing nata wajan magana ta ce "Kitchen" A tare suka nufi Kitchen ɗin, Latifa na nuna mata ta dawo tare da zama kusa da Aliyu ya ɗan ja gefe da sauri ta ce "Me kuma?" Ya dubeta yana girgiza kai ya ce "Baki jin kunya?" Ta juya masa idanu alamar "Kunya? Akan me kuma" Ya taɓe baki yana faɗin "Rayuwarki abar tausayi ce, ban yi zatonki haka ba gaskiya" Latifa ta ware Idanu akan Aliyu ta ce "Kayi mini bayani, bana fahimtar wannan zancen" Ya ce “ina nufin ƙazantarki" Latifa ta ce "Sbd ka ganta?" Cikin rashin fahimta ya ce "Wa kenan?" Ta yi masa shiru ya ce "Yanzu ke baki ji kunyar Hawwa'u ba? Riga daban, zani daban, abin kanki daban? Ƙamshin parlourn daban da warin da yake fitarwa daban? What exlty wrong with you Latifa? Haka zaki haifi yara kina wannan ƙazantar su tashi da abinda suke ganin kina yi?" Bakinta cike da yawo ta buɗe zatai magana ya yi saurin ɗauke kansa zuciyarsa na tashi. "Oh! Daman fa haka ku maza kuke bazan kasan dalili banda cikin dake jikina har zaka ce haka?" Aliyu ya ɓata fuska ya ce "Sbd Allah duk matan da mazan su ke musu ciki haka suke wannan azababbiyar ƙazantar? Parlour warin yawo, part ɗinki haka nikam na shiga uku" Zata buɗe baki sai ga wayo zarara Aliyu ya yi saurin tashi ta juya kanta bayan kujera ta zubar da yawo ta ce "Nikam ina yin iya bakin ƙoƙarina, baka da godiyar Ubangiji" Aliyu ya kasa cewa komai dan takaici can ya ce "Tun satin aurenmu ai haka kike, matsalolinki nada yawa idan zasu zan yi a zuciyata tsaf zata buga tunda na kawo abokaina suka ci abinci suka dinga amai na sare miki, ciki kuma wannan shi ne na biyu wancan ya zube wannan kuma sai ki kula zan kawo ƴar aiki kawai" Ta yi saurin miƙewa ta ce "Kan uban nan a wanne gidan zaka kawo ƴar aiki? Ai wallahi baka isa ba, tsohuwo ko yarinya bana mara ba da su, haka kurum a aure mini miji, matan yanzu da basu da mutumci kamar mayu haka suke akan mazajen wasu musamman yanzu da za a saka ƴan candy marriage, ina son ka ina Mahaukacin kishinka kai ka sani kuma......," Shiru tayi ganin Majeederh na shigowa cikin parlourn hannunta riƙe da wani kyakkyawan warmer wanda Latifa bata taɓa amfani da shi ba, Kullum a warmer ɗaya take zuba masa abinci idan tayi ma kenan. Latifa ta yi murmushi ta ce "Thank you Bestie sannu da aiki" Majeederh ta ɗora warmer ɗin akan table tana nuna tamkar bata jin Conversation ɗin su ba, Aliyu ya dinga satar Kallonta Majeederh na ƙoƙarin miƙewa Latifa ta ce "Ina zuwa" Ganin ta nufi part ɗinta yasa Aliyu shafa cikinsa ya ce "Zuba mini please" Ta cikin liƙab ta harare shi sarai ya gani sai kawai ya shafa kansa yana jan plate tare da zubawa a ciki, sosai Superghgett take tashin ƙamshi gashi ta sha sadin, kasancewar kaɗan ta dafa kuma gas ne ga komai a zube ya sa cikin ƙaramin lokaci ta gama dafawa. Idanunsa ya rufe lokacin da daɗin abincin ya ratsa cikin kunnuwansa Gabaɗaya jijiyoyin da suke amsar saƙo zuwa ƙwaƙwalwar sun ɗauka tuni sun kaiwa tasa ziraya, cin abincin kawai yake hannu baka hannu kwarya har ya mance Majeederh ce gabansa, ya daɗe bai ci abincin mai daɗinsa ba. Ya goge bakinsa da tissue a hankali yana kallonta ya ce. "Kin ceci rai" Ba tayi magana ba, ya saita murya ya ce "You're the best cooker Hawwa'u thank you" Miƙewa tayi bata jira zuwan Latifa ba tayi gaba abinta tare da ficewa daga parlour bakiɗaya... Shigowarta compound ɗin ya yi daidai da fitowar Abbu daga cikin mota, har zai tafi sai kuma ya tsaya yana Kallonta har ta ƙarasu, Majeederh na zuwa ta zube a ƙasa ta ce "Barka da dawowa Abbu, ina yini?" Ya dinga Kallonta kafin ya ce "Lafiya, daga ina?" "Gidan Latifa..." Ta bashi amsa kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ya numfasa ya ce "Ki sameni a part ɗina" Yana faɗin hakan ya juya cikin gidansa nasa wanda ya zama sai mai hannu da shuni ne kawai iya gina gida kamarsa, iya compound na gidan abin kallo ne balle kuma ciki wanda duk sanadin ƴar cikinsa Majeederh ya same su ta tara masa kuɗi na ban mamaki. Lokacin data shiga main parlour tuni Abbu ya shige ɓangarensa Mami ce kawai zaune tana kallon shirin Mata a yau, ta shiga da sallama tana cire liƙab ɗin fuskarta tare da zama, Mami ta kalleta ta ce. "Sai yanzu?" Ta ce "Eh" Ta ƙara cewa "Zaman me ki kai a gidan ma'aurata?" Kamar zatai shiru sai ta ce "Latifa bata jin daɗi shi ne naiwa mijinta girki" Da mamaki sosai Mami ke kallon Majeederh ta rasa ma me zata ce kafin ta ce "Ba kiji nauyin cewa Aliyu ki kai abinci ba? Ba kiji nauyin furta kalmar nan ba? Mijin Aminiyyarki ki kai girki? Ban taɓa jin haka ba ko da wasa na Asabe" Mami ta ƙara tafa hannu ta ce "Sai kika shige madafa kika bar miji da mata a parlour suna jiran abinci" Majeederh kanta a ƙasa ita sam ba taga aibun hakan ba, tunda taimako ta yi Mami ta ce "To liƙab kika cire?" Ta girgiza kai ta ce "A'a" Sai a lokacin Mami ta sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya kafin ta ce "Na gode Allah" Miƙewa ta