← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 93

Sashe 41

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ce da za a ajjiye maka ita kai ta Kallonta? Me ya sa ka ke son kan ka har haka? Kana ganinta, But you don't want to marry her? what kind of nonsense and stupidity is that??" Aliyu ya marairaice ya ce "Ka tausaya mini Yaya, ni kaɗai na san halin da nake ciki idan kai baka rarrashi su Hajia ba waye zai taimaka mini?" Jikin Almustapha ya yi sanyi ya ce "Papa Hajiya help him don Allah kada wani abu ya same shi" Papa da ran shi ya fara ɓaci ya ce "Ok kai ma da kake da hankali kenan ko? To ba zan ɗauki wannan haukan ba, zan je na nema masa auren Latifa Omar ƙilan hakan zai sanya ya manta da batun Majeederh" Wani irin rikitaccen kuka Aliyu ya saka jikinsa sai rawa yake ya riƙe Hajia da ƙarfi numfashinsa na sarƙewa yana riƙe ƙirjinsa, Almustapha ya shiga faɗin "Dr... Dr... Dr.." Likitoci suka haɗu akan Aliyu da ƙyar suka dawo da numfashinsa tare da yi masa allurar bacci dake jininsa mai ƙarfi ne sai bacci ya gagari idanunsa ya dinga surutai. Dr ya kalli su Papa ya ce "Alhaji zaku tafka babban kuskure idan zaku dinga yin abin da zai ɓata masa ran shi" Papa ya kasa magana sai kan shi da yake jinjinawa. Suna haka wayar hannun Almustapha ta fara ringing ganin sunan “Latifa Omar” ya sanya ya ɗaga kiran "Ok" ya furta yana barin cikin ɗakin, not too long suka dawo tare da Latifa da kanta ke ƙasa sanye da hijabi ta yi sallama tare da durƙosawa ta ce "Ina yini ya mai jiki?" Hajia ta dinga kallon Latifa Omar frm head to toe a taƙaice ta ce "Alhmd" kana ta miƙe ta bar ɗakin, Papa ma ya fita Almustapha ya ajjiye wayar Aliyu ya fice wajan ya rage daga Latifa Omar sai Aliyu dake kwance. A hankali ta miƙe ta zauna a gefen gadon ta ce "Nasan ba bacci ka ke ba, ya jikin?" Aliyu sai ya ji tamkar muryar Majeederh lokacin da take cewa _“ I don't want to interfere”_ Da sauri ya buɗe idanunsa tare da sauke su akan Latifa Omar wacce a yanzu ta zame masa Majeederh Abdul'aziz Khan sak! Duk da bai san fuskarta ba amma zubin yadda idanunsa suka kalle masa Latifa sai yaga kawai Majeederh ce gabansa, ya mance drip a hannunsa ya tashi zaune yana kafeta da idanunsa wanda suka sauya Latifa na ƙoƙarin magana ta ji gabaɗaya ya jawota ya riƙeta tsam a jikinsa ya ƙanƙameta yana sauke wata mahaukaciyar ajjiyar zuciya cikin magagin allura ya ce "Don't leave me alone please, ban so kada ki barni please Hawwy" Ya riƙe ta yana cusa kansa a wuyanta, Latifa Omar tsoro ya kamata sbd babu wani namiji daya taɓa yi mata hakan a tsayin rayuwarta, gefe na zuciyarta kuma bata jin zata iya hana shi yin haka sbd Allah kaɗai ya san irin son da takewa Aliyu. "Ba zan barka ba, ni ɗin taka ce Allah da Manzonsa ma sun shaida hakan" Ta faɗa a sanyaye ta kuma rasa faɗuwar gaban na mene?.. _*5 Month later...*_ Majeederh ce ke ta fe a hankali kanta a ƙasa hannunta riƙe da littafai yadda take tafiya zai tabbatarwa da mai Kallonta a mugun gajiye take, kusan haka ɗin ne domin karatu ya yi mata yawa bata da lokacin komai da kowa sai karatu tsayin watanni biyar da zuwanta Egypt bata taɓa kiran number kowa a Nijeriya ba, haka kuma bata da ƙawa idan ba Ƙhulud Arzaan ba, hakan ya sa da yawan student suke mata kallon mai masifar girman kai suka yi tunanin ƴar gidan wani ce a duniyar ma bawai a Nijeriya ba, Ilimin da Majeederh take da shi ya ƙara mata kwarjini a idanun malaman jami'ar da sauran ɗalibai, ita kuma suka zaɓa matsayin shugaban ɗalibai duk da ta ce bata so amma aka tilasta mata amsa, da yawan Student na zuwa ta ƙara musu haske, wasu kawai don su ji maganarta wasu kuma ko Allah zai sanya suga fuskarta suga mene dalilin rufe fuskar. A cikin watanni biyar harshenta ya juye sak cikakken Balarabiya ba zaka taɓa cewa ta san hausa ko English ba idan tana larabci, to ta je garin larabawa uwa uba ɓangaren Arabic take karanta. Duk rashin son maganarta sai da ta saba da Ƙhulud Arzaan ba tare da sanin dalili ba, haka kawai take son yarinyar kamar Aaliyyah, Ƙhulud Arzaan ta taka rawa sosai wajan wayar da Majeederh ta jata har shopping ta kwasu mata abayas masu mahaukacin kyau tsada very expensive classic one and unique. Liƙab ɗin ma ta sauya mata irin na Larabawa da suke sawa, a cikin 5 Month ɗin nan Majeederh a rame take bata gaba bata baya jia iyau kamar kazar matsiyata ramar kuma ta samu asali akan abinda ke hanata bacci kullum yake sanyata azumi wanda babu fashi ya zame mata jiki kullum. "Majeederh... Majeederh" Kiran ya dakatar da ita daga tafiyar da take Ƙhulud Arzaan ta ƙarasu tana dariya ta ce "Shi ne kika taho ko?" Majeederh ta ɗan saki numfashi ta ce "Kin tsaya gulma" Ƙhulud Arzaan ta ce "Gulmar ta yi mini amfani kam" Ita dai Majeederh bata ce komai ba sbd an kusa kiran sallar Magriba bata so ta yi mata a hanya Ƙhulud Arzaan ta ce "Musabaƙar Alkur'ani za a yi, Ta duka ƙasashen duniya na Muslunci" Majeederh ta waro idanu ta ce "Ma sha Allah, za mu ga manyan malamai mu tada haddarmu mu ma" Ƙhulud Arzaan ta ce "Au haba? Kin san me gabaɗaya ko wacce ƙasa ta bada sunan wanda zai wakilce su, ƙasar ku Nigeria kawai ta rage" Majeederh ta yi shiru tana tunani wa Nigeriya zata zaɓa? Allah ya sa ko waye ya dawo musu da martabar ƙasar su. Kafin ta yi magana Ƙhulud Arzaan ta ce "Kuma Saudiya ta sallamawa Misira kamar yadda suka buƙata ayi Musabaƙar a nan ƙasar, kuma hadda Granny ta a mutanen da zasu zama masu tantance ƙasar da tayi nasara" Majeederh ta ce "Kullum ana bani labarin Granny Finally zan ga Granny" Ƙhulud tayi dariya sosai ta ce "Like serious, ba ruwanta idan kin ganta sam ba zaki ce ta haifi Sarki Sultan ba" Majeederh ta ware idanunta ta cikin liƙab ta ce "Kai, ke jinin sarauta ce?" Ƙhulud Arzaan ta yi shiru domin bata son cewa Majeederh ita surukar gidan ce babanta kuma ƙanin Sarki Sultan ne. Suna hira har suka ƙarasa gidansu Majeederh ta yi part ɗinta Ƙhulud Arzaan ta shige nata. Wanka Majeederh ta yi kana ta yi sallah sannan ta sha ruwa, tana mai yin watsi da maganar Ƙhulud Arzaan. A nutse ta jawo wayarta ta kunna cikin nutsuwa ta danna number Abbu, ringing ɗin farko ya ɗaga ta cikin wayar ta ji ya ce "Ko baki faɗa ba nasan Majeederh ce" Ta sauke numfashi ta ce "Asslaymu Alaika Ya Abbu" Ta faɗa a nutse.
Chapter 41 · 0% Book details