← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 93

Sashe 73

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Not edited MIJIN MALAMA na kuɗi ne pay before you read..... More information via WhatsApp number 08119237616"Na auri mijinki? Do you want me to marry your husband?" Da wani Expression na tashin hankali take faɗar maganar tana kallon idanun Latifa Omar. Latifa ta watsa hannunta cikin rashin damuwa ta ce "To mene na tashin hankali a nan? Bayan iyayena dake, babu abinda nake a cikin duniyar nan irin mijina, amma wallahi na amince miki hundred patient da ki auri Aliyu, ki auri mijina mu zauna tare, ba zan taɓa yi miki kallon kishiyata ba, don Allah ki rufa mini asiri ki auri Aliyu" Latifa ta faɗa muryarta na rawa. Miƙewa Majeederh ta yi tana ɗaukan handbag ɗinta da wayarta ta nufi hanyar fita daga cikin parlourn. Da sauri Latifa Omar ta miƙe tana shan gaban Majeederh ta ce "Ina zaki? Ki tsaya mu yi magana don Allah, this is the right time da zamu kawo karshen matsalarki Majeederh" Murmushin takaici Majeederh ta yi hawaye na sakko mata a a kumatu ta ce "Well-done Latifa Omar, sbd na tako ƙafa da ƙafa har cikin gidan ki na faɗa miki matsalata shi ne zaki dubi idanuna kika ce i should come and marry ur husband? Are you mad?" Magana take amma hawaye ne ke zuba daga cikin idanunta. Latifa ta girgiza kai itama hawaye ya shiga sauka daga cikin idanunta ta riƙe hannun Majeederh sosai cikin nata ta ce "Wallahi that's not what i mean, tun kafin yanzu ayi miki maganar fitar da miji nake son faɗa miki ki auri mijina ina tsoran abinda zaki faɗa, Majeederh na san halinki nasan how hard you're, You have a deep heart, even if the worry will kill you, you will never tell anyone, na kasa jure yanayin na kasa fahimtar cewa jarrabawa ce, maganganun mutane akan ki ya fara yawa, me ya sa ina da maganin damuwar ki a hannu zan zuba idanu kina cutuwa? Aliyu na da kyau, ilimi both boko da Arabic, yana da kuɗi ko kuɗin mahaifinsa bai damu da shi ba, Hajia Mahaifiyarsa na da kuɗi, Ubangiji ya hore masa arziƙin da zai zauna da mata har huɗu ba biyu ba, Zan iya mallaka miki komai na rayuwa daga ciki har mijina If that makes you happy,if that will make you look like any other woman in her husband's house,Please marry my husband, Aliyu!" A hankali Majeederh ta zare hannunta daga cikin na Latifa Omar ta durƙoshe a wajan tana sakin wani irin raunataccen kuka, mai cin rai da ciwo a zuciya. Wani irin kuka take Wanda ta jima ba ta yi irinsa ba, ga ƙoshi ga kwanan yunwa,ga maganin matsalarta amma ko duniya da abinda suke cikinta zasu haɗu ba zata taɓa auren mijin Latifa ba, bata taɓa kawo hakan ba ko da, da wasa. Zubewa Latifa ta yi itama ta rushe da wani irin kuka kamar an musu mutuwa ta ce "Ashe ba zan iya rufa miki asiri ba? Ashe zumuncin banza muke? Ashe ban zama ƙawar da zata ɗauki damuwar ƙawarta matsayin tata ba? I have been friends since we were children, we trust each other, we know each other's behavior,Even if you marry my husband, there will be no worries between us, wlh ko Aliyu kika aura babu ɓarakar da zata gilma tsakaninmu, babu wani yaƙunanne ko shegen kan lafiya da zai sako lalataccen bakinsa, zamu zama abu ɗaya, zuri'a ɗaya one single family mu zama Matan Aliyu, ki haifa masa yara tunda har yanzu Allah bai bani haihuwa ba" Majeederh kuka take sosai kamar ance Abbu ko Little ko Aaliyyah wani ya mutu, ta kasa cewa komai sai jikinta dake mahaukacin ɓari da ƙyarma kamar an jona mata shocking. Bar Aliyu Sufyan Alhassan da tunda ya yi parting da motarshi ya shigo gidan ya tsaya cak a ƙofar da zata sada shi da main parlour na gidan nasa, tun daga farkon conversation ɗin su har kawo yanzu ya ji komai, zufa ce kawai take yanko masa all over himself, jira yake ya ji me Majeederh zata ce akan requesting ɗin Latifa?. "Majeederh say something, ki daina kukan hakan" Majeederh ta kalli Latifa Omar da rinannun idanunta wanda ba lafiya ya cika ba, ta ce "Dole na yi kuka Latifa, ban taɓa tunanin watarana da zata zo ace zan auri mijinki ba, me ya sa kike tunanin zan iya auren mijinki, why should I do that? Me mutanen unguwa za su ce? Me ƴan-uwan ki za su ce? Su ce na zama munafuka, maci amana mayaudariya, wacce ta aure mijin aminiyyarta? That's what you want? Sbd ina kawo miki matsalata ashe ke tunaninki mijinki zan aura? Sbd ƙaddara ta faɗa mini shi ne zaki manna mini hauka ki zautar dani da gurɓataccen tunaninki mara amfani a gareni, zaki forcing mijinki ya aureni? Bayan kin san mazan guduna suke, basa ƙaunata, balle muradin aurena, banda Imran daya taɓa furta kalmar so a duniyata babu wani ɗa namiji da ya ce yana so na, ko da sunan iskanci ne....," Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanya ya kasa ci-gaba da maganar ta haɗe kanta da qiwwa kamar ƙaramar yarinya. Latifa kukan take sosai ta ce "Ba zan taɓa forcing Aliyu ba, nasan ba zai gujewa maganata ba, ku zauna da juna na 1week am sure zaku ƙaunaci juna, mutanen gari kuma ki barni da su" Majeederh ta miƙe tare da goge hawayenta tas ta saki liƙab ɗinta. "Kin Amince?" Aliyu dake tsaye cikin zuciyarsa ya ce "Say Yes, Hawwa'u" Har bakin ƙofa Lafita ta biyota amma Majeederh bata kulata ba, lokaci ɗaya suka saka hannu akan handle jin an murɗa ya sanya Majeederh saki tare da komawa baya, a hankali ya buɗe Ƙofar ganinsu a har gitse ya sanya Aliyu dake cikin nevy suit hannunsa ɗaya riƙe da rigarsa ta lauyoyi sai zabga ƙamshi yake, a hankali ya ce "What did i miss?" Latifa ta ce "Ka tsayar da ita" Muryarta bata fita sosai ta ce "Bani hanya" Gefe ya koma ta raɓa ta shige abinta, muryar Latifa na rawa ta ce "Me ya sa zaka bata hanya, ba zata taɓa dawowa ba fa, kuma na ce ka tsayar da ita" Bai ce mata komai ba ya mayar da ƙofar ya rufe, hannu tasa zata buɗe Ƙofar Aliyu ya yi sauri riƙo hannunta ya ce "Let her go, Wife" Kuka ta fashe masa da shi ya jawota jikinsa "Sorry" kawai ya samu zarafin faɗa sbd zuciyarsa da tayi masa nauyi, ganin taƙi yin shiru ya sa ya jata har zuwa bedroom ɗinsa dake tashin wani cool ƙamshi na air-freshener, cikin dabara ya shiga bata saƙo albarkacin Majeederh Aliyu ya samu abinda ya daɗe bai samu ba a wajan matarsa Latifa tsayin wata wajan goma. Yana zaune saman wata ƙatuwar kujera ya harɗe ƙafafuwanshi saman sofar idanunsa lumshe breathing ɗinsa na sauka a hankali alamar bashi da lafiya, ya ƙara yin wani farin idanunsa sun faɗa, cikar haiba da da zati da kamalar shi na nan zaune daram a jikinsa. Wata Embroidery Islamic jallabiya ce a jikinsa fara tas, sai jiramin daya ɗora akansa looking so good. Rohaan dake tsaye cikin damuwa ya ce "Allah ya ƙarawa Mai martaba Ajlaal Sultaan lafiya, wannan tunanin da kake isn't good for ur health" Mai martaba Ajlaal bai magana ba sai idanunsa ya buɗe yana kallon ɗan uwan nasa Rohaan, ganin kallon da Mai martaba Ajlaal Sultaan yake masa ya sa ya ce "Ba tare da sanin abinda ke faruwa ba, a karo na farko wani jininmu ya sako ƙafa zuwa Nigeria, ka matsa yanzu kuma gashi ka ce mu tafi ba tare da yin abinda ya kawo mu ba" Nan ma Ajlaal bai ce komai ba, Rohaan ya numfasa ya ce "Idan akwai abinda ke damunka yana da kyau ka faɗa, tunda kasan idan har a duniya yake dole zaka same shi, ka tsallake Zaytoon, da Mimi wacce kai kaɗai kake controlling ciwonta idan ya tashi, ka bar Fulani Ƙhulud da tagwayen yaranta, Palace ba kowa sai Hadiman, Meke faruwa dakai Mai martaba? Yana da kyau ace....," “Rohaan” Ajlaal ya kira sunan Rohaan da ɗan ƙarfi a kuma taushashe, Rohaan ya ce "Tuba nake Mai martaba" A nutse Ajlal ya duba agogon Rolex dake hannunsa yana mai kikewa tsaye cikin izza har ya je bakin ƙofa sai ya tsaya ya juya kaɗan ya kalli Rohaan, da sauri Rohaan ya durƙosa ya ce "Prvt jet ɗin na hanya, ban san ya akai aka samu labarin zuwanka Nigeria ba, gabaɗaya zuwan naka shi ne latest new in the world" Da wani irin Expression Mai martaba Ajlaal Sultaan yake kallon Rohaan jin abinda ya ce, zufar dake tsastsafo masa a tsakiyar goshinsa ita ke nuna tashin hankalin jin mummunan labarin, ya dunƙule hannu tare da kallon Rohaan alamar ƙarin bayani. Rohaan ya ce "A karo na farko Sarki makka Mai martaba Ajlaal Sultaan magajin Ex Sarkin Makka Sultaan ya sauka a Nigeria, har yanzu ba a san dalilin zuwansa ba, ana kyautata zaton zuwan sirri ne ya zo ganawa da wani ɗaya daga cikin sarakunan Nigeria, zuwan nasa ya ja hankalin dubban mutane ganin tun ƙarnin baya na kafuwar masarautar Saudiyya jininsu bai taɓa zuwa ƙasa Nigeria ba, ko mene dalilin zuwan nasa?" Daga nan Rohaan ya kashe T.v da remote ɗin hannunsa ya ce "Ire-iren wannan sune news ɗin da suke trending a duniya da Social media tare da photonka, alamarin ya fi tsamari a Al Jazeera, BBC World News,CNN International da kuma Arise News" Duk maganar da Rohaan yake a tsorace yake yinta, Ajlaal ya zame idanunsa yana riƙe kansa da kyau, duk da tashin hankalin da yake ciki, a taushashe cikin tarin ilhamarsa nutsuwa da kamalar dake zaune a jikinsa cikin kamilalliyar muryarsa yana lumshe idanu ya ce "A san yadda aka yi, aka dakatar da news ɗin" Ya shiru yana juyawa can ya ƙara fesar da iska ya ce "Kowa na Palace, ya zama lafiya, a san yadda akai aka ƙaryata zuwan namu Rohaan" Da girmamawa Rohaan ya ce "An gama Mai martaba, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana" Tuni ya kai cikin bedroom ɗinsa yana hana kansa jin abubuwan da suke masa yawo a jiki... Majeederh na zaune a ƙasa an haɗa family meeting kowa da kowa
Chapter 73 · 0% Book details