Sashe 77
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
motsin Majeederh yana gani juyawa spoon kawai take tana cakalkala dankali, few minutes ya sake ɗago kansa ya zuba mata Idanu "Hawwa'u" Ta ji saukar muryarsa ji tayi kamar tayi fitsari a wando ta ce "Na'am Abbu" Shortly ya ce "Leave" Miƙewa tayi tabar wajan da sauri tana jinta kamar ware a cikinsu. Mami ta ajjiya cup ɗin hannunta ta ce "Me ya sa kake yi wa yarinyar nan haka ne Alhji? Me ya sa kake son nuna fifiko a cikin yaranka, bana son haka a gaskiya ni" Bai ce mata komai ba, Aaliyyah ya tsame hannunta zata miƙe Abbu ya ce "Sit" Ta zauna tasan me yake nufi. "Raihana me kike cewa?" Raihana na rarraba idanu ta ce "Daman wani ne ke mini aike yana da hankali sosai daga ƙauyen Rurum yake naga da ƴar sana'arsa daidai gwargwado domin har ɗan dako yake, na ce ko shi za a haɗa da Majeederh tunda Kinga al'amarin nata shiru babu mashin shi ni, sunansa Tasi'u" Ruma ta ce "Lallai da kin yi aikin lada sosai Raihana" Mami ta ce "Shi ɗan dakon kenan?" Raihana na kallon Abbu ta ce "Wlh ai irinsu babu ruwansu, musamman ga Majeederh fara tas wlh haukacewa zai ya samu mata ta keta raini bama zai duba taimakon da ya yi ba, nan nan zai dinga yi da ita kamar ya lashe" Cak Abbu ya ajjiye cup ɗin hannunsa da yake ƙoƙarin kawai baki zai sha ruwa, ya mayar ya ajjiye tare da miƙewa ya fice daga parlourn. Compound ya nufa Driver na ganinsa ya miƙe tsaye, Abbu ya nufi wajan mai gadi ya ce "Waya shigo cikin gidan nan jiya?" Mai gadi ya kama kame kame Abbu ya ce "Ohk haɗa baki ake da kai ana shigo mini gida? Ka tattara kayanka na sallameka kuɗinka zan tura maka ta acct" Mai gadin ya rikice sosai ya zube yana bawa Abbu haƙuri amma ina tuni ya shiga mota... Zuwanta gidan Maman Alpha kenan ta nufi part Innati tabar Latifa tare da Maman Alpha, bayan sun gaisa Innati ta ce "Ina Kululu?" Majeed ta ce "Gani kusa" Innati ta ce "A to bana ganki ba kuma, ƙara tabbatarwa zan yi" Ta ƙara zama ta ce "Shikenan ku dangin mahaifiyarku basa ƙaunarku ne?" A sanyaye Majeederh ta ce "Me kika gani?" Innati ta yi mitsi mitsi da idanu ta ce "Ji wata wulaƙantacciyar tambaya?? To ke yanzu dan Allah wa kika sani a dangin Fulani?" Majeederh ta ce "I don't know anyone, I've never seen anyone from my mother's family" Innati ta saki baki ta ce "To banda kin so wulaƙanta ni a idanun jama'a meye zaki sauya raye, ni zakiwa turanci?" Ita dai Majeederh bata ce komai ba, domin jikinta duk ya mutu tana son yi wa Abbu maganar Mother's family ɗin su tana jin tsoro. Innati ta ce "Kawai ki rutsa mahaifinki shi ne nunafukin ki ce ya fito miki da dangin mahaifiyarki, ki ɗaga masa hankali sosai idan ma kidnaping ɗin su ya yi sai mu ji labari, tunda ba wani yarda nayi da zuciyar Audil azizu ba, sama taka mu kaga yayi arziƙi fa? Shi yasa yake ta wani fankama yana ɗaga kai, to ai mu munga ƙaruna ma" Majeederh ta yi shiru Innati ta ce. "Allahu Akbar, ai ba zaki san ƙaruna ba, munga ikon rabbi a wajan bawan Allan nan, gashi dai ƙarshen shi bai wani kyau ba, ai wallahi wannan kyan na fuskarki da farar fatar nan kamar sadaka yalla to haka uwarki take, har ta ɗaraki a kyau mace mai sanyin hali da haƙuri, ta sha fama da talaucin Audil azizu sana'a kala-kala tayi fa? Ko Attajirin uban naku bai baku labari ba? Babu mamaki gadonku ya tattara ya siyar kwasha kwasha, domin har gwala-gwalai ne da ita" Majeederh idanunta ya cicciko da hawaye ta kasa cewa komai. Innati ta zabga sallati ta ce "Yanzu kamata Kululu ni zakiwa turanci? Ni zaki sauya harshe, yanzu fa muke Shira dake rumi rumi kawai sai kika sauyan raye ni ki kaiwa turanci" Majeederh ta miƙe ta ce "Kyaci kanki ke kaɗai" Ta yi waje abinta, Innati tayi ƙasa da murya ta ce "Tab, kaɗan ya rage ban saki fitsari ba yarinya kamar Aljana, zaki Albarka,zaki Albarka mijinki daban yake sananne ne shi tauraro ne, wanda duniya ta gama saninsa" Haka take something kamar wacce ake buɗewa idanu. Maman Alpha da kalli Majeederh ta ce "Majeederh Kinga ɗan uwanki har yanzu shiru? Ko yana raye ko ya jima da mutuwa? Ko a hankalinsa yake ko ciwon hauka ya same shi Allah kaɗai ya sani" Gently Majeederh ta kalli Maman Alpha ta ce "Ki yi haƙuri, addu'a za a yi" Murmushi kawai ta yi kafin ta ce "Ya maganarki kowa? An samu tsayayyen?" Kafin Majeederh ta yi magana Latifa Omar ta ce "Aliyu ya ce zai aureta, amma taƙi" Maman Alpha ta ce "Mijin naki?" Latifa ta ce "Eh" Da mamaki Ta ce "Son ta yake?" Latifa ta ce "Sosai, sbd ya ce na yi conversing ɗinta to marry him take gaba dani" Maman Alpha ta yi shiru for a second kana ta ce "Eh to gaskiya conversing Majeederh to marry ur husband Aliyu, kamar ki yi forcing nata ta cakawa kanta wuƙa a ciki ne, How do you think she can marry her Aminyya's husband? It is a difficult thing that the mind cannot handle. Honestly, even I do not support this useless thought, Majeederh tana buƙatar taimakonki,She needs your help, but not this way, think of something else besides this" Latifa ta marairaice ta ce "Ni wlh tallahi na amincewa Aliyu, ba zan taɓa kishi da Majeederh ba, zamu ci-gaba da zama kamar yadda muka sabaSocially there is sacrifice, I sacrifice my husband's love for Majeederh" Maman Alpha ta ce "Sacrifice?" "Eh" Cewar Latifa Omar Maman Alpha ta ce "Let me tell you something you don't know, ko da ƙanwarki da kuke ciki ɗaya aka haɗaki waje gudu wlh sai kin yi kishinta, balle Majeederh? Sanda zaki shige ɗaki kina ihu idan suka keɓe Allah kaɗai ya sani,We are dedicated to Love, it does not mean that we have stopped loving, in love there is jealousy, Think about that Latifa Omar" Kafin kowa ya yi magana Innati ta shigo tana kuka wiwi hannunta riƙe da sanda. Maman Alpha ta ce "Subuhanallah lafiya Innati?" Innati ta ce "Fatima wai ni Kululu zata juyawa yare ta yi mini turanci?" Maman Alpha ta ce "Allah gasky bata kyauta ba, turanci ana zaune lafiya?" Lafita ta dinga dariya sosai sun jima a gidan kafin su ta fi. A hanya Lafita ta nufi Tahir Quest Palace Majeederh ta dai kalleta ganin hakan ya sa ta ce "Abu zan karɓo kin san mu ƴan jarida, muna amfani da Opportunity da zarar ya samu" 5 days left. Tun ranar Majeederh bata ƙara jin motsin Abraham ba even on the phone, har numbersa ta kira ta ji a kashe. A hankali ta rufe Idanunta da sauri ta buɗe kuma tama rasa wanne kalar tunani za ta yi, tana zaune wayarta ya fara ringing dubawa ta yi taga new number sharewa ta yi, kuma ba a fasa kiran ba, tunaninta ya bata masu neman taimako ne ko wani abu ne ya tashi a Ngo ɗinta. Ta ɗaga kiran tare da cewa "Assalamu alaika/ki" Taj ya yi wa Salamon alama da ya yi shiru a ladabce ya ce "Good day Mami" Sosai Majeederh ta ɗauki muryar ta yi shiru, Taj ya ce "Sorry na kira without ur permission, am very sorry about that" Bata ce komai ba, a ransa yana mamakin girman kanta ya ce "Abraham, baya da lafiya kwana biyar kenan, baya ci baya sha sunanki kawai yake kira gashi Grandpa baya gari" Majeederh ta yi shiru a hankali ta ce "Bashi wayar" Taj ya ce "Dr ya duba shi yanzu bacci ya ɗauke shi, amma yana da kyau idan ya buɗe idanu ya ganki" Shortly and silently ta ce "Address" Ya ce "Ohk check ur Dm" Kashe kiran ya yi ba jimawa ya tura mata da Address ɗin gidan. Sosai ta dinga duba location ɗin tana mamakin unguwar. Shiryawa ta yi cikin mik ɗin Abaya mai kyau ta ɗauki hijab ta saka tare da liƙab, waya da key kawai ta ɗauka ta nufi waje. Mami na zaune Main parlour watching TV ta ce "Mami zan ɗan je dubiya" Mami ta ce "Subuhanallah wani ne bashi da lafiya?" Majeederh ta ce "Eh" Ta jinjina kai ta ce "Kada ki jima" Fita tayi ta nufi wajan baƙar motarta tare da buɗewa ta shiga bismillah ta yi tare da yin key tai reverse gatekeeper ya buɗe mata, tana fita motar Abbu na shigowa, Aliyu dake tsaye a bakin gate ya ji he need to follow her, ya ga where she's going to?.... Babban gida ne wanda kafin kaga irinsa sai an tona, tsayawa faɗin yadda gidan yake ɓata baki ne, ga wasu mahaukatan securities birjik, gidan ta ciki part part ne. Gang team ne zaune a wani haɗaɗɗan parlourn gidan wanda ya kasance mallakin Abraham shi ya zana gidan da kansa. John ya ce "Taj me ya sa ka yi mata ƙarya?" Taj ya ce "Kawai ta zo ta gansa" Salamon ya girgiza kai ya ce "Baka da kirki wlh" Dry ya yi sosai duk sun cika parlourn da hayaƙin Shisha ya ce "Na kusa barin country ɗin nan" kafin su yi magana sun ji ƙarar doorbell. Taj ya miƙe ya ce "Ta ƙarasu, ku ɓoye kayan drugs ɗin nan" Da sauri suka kwashe komai, ya buɗe mata ƙofa ya ce "Wlcm Mami" Bata kula su ba sai parlourn data shiga ƙarewa kallo ya ninnka na gidansu a komai, ta yatsuna fuska. Gabaɗaya suka miƙe kamar marasa gsky sbd kwarjini ta yi musu duk da fuskarta a rufe yake. Salamon dake ya fi kowa bin diddigi ya shiga ƙarewa yatsun ƙafar Majeederh har wani yellow suke don fari. Waya Taj ya ɗauka kira Abraham dake can cikin wani narkakken part. Majeederh ta kasa zama har wajan minti biyar kafin ta ji John ya ce "Gashi nan ma" Bata ɗago kai ba haka nan Moment ɗin su ya faɗo mata, da tunanin wanda aka ce bashi da lafiya me ya fito da shi? "Hold on.