← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 93

Sashe 11

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda Jeederh ta kai da son kamewa waje guda da riƙe kanta amma ka sawa tayi ta miƙe tsaye hannunta riƙe da Khalil, amma ta kasa motsawa sbd bata ƙara jin saukar sautin da kunnuwanta suka jiye mata ba. Shiru shiru sai kawai ta juya zata koma saman bed ta ƙara jin ance "Jee, Jee Malumana" a wannan karan muryar da aka kira sunan bata fita sosai kamar bai kiran yana cikin wani hali, ƙirjinta ya yi kyakkyawar bugawa, bugawar da sai data runtse Idanunta, me ya sa muryar ke yi mata tsananin kama data Little Son? Me ya sa hatta sunan ya zo ɗaya da wanda ya laƙaba mata sbd bashi da hausar da zai iya kiran complete sunanta Majeederh kamar yadda kowa ke faɗa, iya ƙoƙarinsa da faɗar sunan sai dai ya furta kalmar _Jee_ a sauƙaƙe? "Yaa Allah" ta furta domin tasan har abada har gaban abada idan akwai he never comes to her, amma meke damunta har haka me ya sa muryar ke mata amsa kuwwa a kunne? "Jeeeee!!!" Ya sake furtawa muryarsa bata fita sosai kamar wacce aka tsikara tayi wajan ƙofa tare da sanya hannu ta murɗa handle, tsaye ta gashi yana zabga ƙamshi daga shi sai wata kyakkyawar Arabian jallabiya brown kallo wacce tayi masa kyau sosai, ya ɗan sakar mata kyakkyawan murmushi kafin ya ce "Kina buƙatar wani abu ne?" Tayi masa kallo ta ɗauke kai ba tare data amsa shi ba, domin bata da yawon magana Majeederh nada matsanancin aji sosai, wanda kuma halittar ta ce hakan. Gani ya yi tana leƙa waje shi ma ya leƙa yana cewa "What are looking for? Me ki ke kallo?" A raunane wanda kuma ba kowa take son yaga raunin nata ba ta riƙe kanta sosai tana sake rufe jikinta da hijabi ta ce "Allow me to go" "Where?" Ya amsata da sauri. "Ban son zaman nan, kuma ka bari na leƙa waje" Abu-turab ya ware idanu yana shafa sumar kansa ya ce. "Me Jiddo zata yi a waje yanzu? 2 saura ok" tayi shiru ya ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin tayi saurin ƙanƙame jikinta waje guda lokacin Khalil ya fara kuka.. Sosai Abu-turab ya rufe ƙofar kana ya nemi waje nesa da ita ya zauna saman kujera ya harɗe ƙafa. Malama Majeederh hankalinta ya rabo wajan kashi uku, ɗaya na waje, ɗaya na kan Khalil dake kuka, ɗaya na kan Abu-turab daya sanyata a gaba tare da kafeta da idanu. Sai ta zama ira bata ƙaunar kallo yana takura ta ainun. Abu-turab yana ƙoƙarin magana su ka ji an daki ƙofar ya miƙe tsaye tare da kallon Jeederh ya ce "Sorry, na ce a kawo mini abin shur ina da azumi" bata ce komai ba ita dai. Ya nufi ƙofa yana fita ya rufe ta, kokawa ake sosai da Abraham Daniel David wanda yake son ta ƙarfi sai ya ɓalle ƙofar, gadai securities da yawa amma sun kasa controlling nasa ya jiwa kansa ciwo amma yaƙi ya yi giving up, wani irin ƙarfi ke zuwar masa. "Abraham" Abu-turab ya kira shi,ya juya kalli Abu-turab. "Me ka ke buƙata?" Da hannu ya nuna masa bedroom ɗin da Malama Majeederh ke ciki, kana ya nuna ƙirjinsa wajan zuciyarsa ya ce. "Jeena, nan" Abu-turab ya fahimci Abraham na son shaida masa Jee na cikin zuciyarsa ita kuma yake nema. Cikin nutsuwa yana murmushi ya ce "My friend zo ka ji" Abraham ya kafe waje guda domin babu na biyunsa a taurin kai. Cikin tattausa harshe ya ce "Ita Jee ɗin bata nan, amma ka dawo gobe zan kaita wajanta" ya faɗi hakan cikin harshen Ingilishi yadda Abraham zai fahimci mai yake nufi. "Promise?" His Excellency ya ce "Promise" Abraham ya sanya hannu a tsakiyar rigarsa inda ya yage ya zaro wata kyakkyawar flowers sai ƙamshi take ya miƙawa Abraham yana wani irin buɗe ido ya ce "Malumana" Ma'ana the flowers is for her. His Excellency ya amsa deep down na zuciyarsa cike da mamakina Abraham who is he to her?. Securities ɗin za su kama shi ya girgiza musu kai tare da yin gaba yana ɗan tangaɗi yana yin gaba ya ji saukar muryar Khalil na kuka ya tsaya cak, sai ya juya kawai sai su kaga ya yi murmushi ya ce "My pregnancy" "An samu matsala" In ji Khamal. Abu-turab ya saka hannu ya tsige flower ɗin tare da zubar da ita ya ce "Make sure baku sake sakaci ba, i hate noises" "We're sorry Sir, Hakan ba zai sake faruwa ba, wallahi ta sama ya hauro mahaukaci ne daya kama hannun Captain sai da ya ƙarya shi,ya sha duka sosai wajanmu amma bashi da haƙuri yana da zuciya ban san wani abu giving up ba" His Excellency bai ƙara magana ba ya buɗe bedroom ɗin har yanzu tana zaune saɓanin ɗazo Madara take bawa Khalil, Abu-turab ya jima yana satar kallonta da tayi ƙoƙarin ɗago kai sai ya janye idanunsa ya basar "Jiddo, we need to talk please" yadda ta ƙara nutsuwa ya san cewa ta bashi dama cikin nutsuwarsa ya ce "Majeederh kina da hankali, ko ban girmeki ba zamu iya zuwa age mate don haka duk abinda zan faɗa miki ba zai zama cutarwa a gareki ba" ya sauke numfashi ya ɗora da "Don Allah kada ki ji zafinki akan hukuncin da ya yanke miki, iyaye ba a taɓa fushi da su ki ɗauki hakan matsayin jarrabawa kuma ƙaddara wacce babu yadda zaki iya dole sai ta kasance, ba zan miki nasiha akan yarda da ita ƙaddarar ba domin kusan kin fini sani, sai dai na nemi ta barraki a wajanki" ya ƙara yin shiru ya ce "I feel your pain, kafin na zama gwana na sha wahala,ina rayuwa da mahaifiyata after my father's died, dangin mahaifina they are so selfish sun ƙwace komai dana mallaka wajan Abbana, filaye, kadarori all the properties, mun fara yawo yawo a dangi kowa yana gudunmu sbd babu ran mahaifina sun manta alherin da ya yi musu, dangin Mamana basa kusa, na fara dako ina garuwa ban taɓa yarda ba zan iya ba, burina Mamana ta ji daɗi na zama wani abu" ya ɗan sauke numfashi kamar lokacin abin ke faruwa kafin ya zuba mata Idanu ya ce "I was thinking mene ya sa mutane suke manta alheri? Kuma da yawan mutane suke sawa ka zama mutumin banza, ko dana fito takarar House of assembly kin me ne ya faru?" Sai a lokacin ta ɗago kai ta kalle shi some seconds kafin ta janye ganinta daga gare shi, tana ɗan ɗauke numfashi sbd abubuwan da suka tukare mata bata san ranar faɗawar su ba. Abu-turab smile yana jan idanunsa zuwa sama kafin ya ce "Cewa akai kada a sake a zaɓeni wai bani da uba, ba wannan ya daman ba familyna sune kan gaba wajan ganin na fasa kujerar da nake nema, kamar yadda suka so ban samu ba, gabaɗaya deligate suka juya mini baya, cikin ikon bayan an cinye tenuwa huɗu cif na sake fitowa takara i won the election, nayi shekara huɗu a lokacin ne na haɗu da ƙaddarata, wacce ta zame mini Dafi a zuciya, ta zame mini wani tabon da bana tunanin zai taɓa gogewa da jikin zuciyata sai dai idan zuciyar ce ta samu abinda take buƙata, Jiddo ban faɗa miki haka domin ki tausaya mini zuwa gaba ba, shi ya sa ma ba zan baki labarin cikakkiyar ƙaddara tawa ba, amma ki sani ko wanne mumini idan har amsa sunansa dole Ubangiji ya jarabce shi da jarrabawa, bafa don ya son mutum yake jarabtar shi ba, sau tarin wanda Ubangiji ya fi jarabta to ya fi samun kusanci da shi, kiyi haƙuri ki ɗauka haka zanen taki ƙaddarar yake, babu mamaki mahaifinki ya fiki jin zafin abun da ya faru kiyi masa uzuri, ki addu'a cikin sauƙi komai zai zama labari" ruwa ya ɗauka ya sha yana sauke numfashi. "Thank you!" Ta furta cikin kamewarta da nutsuwarta a koda yaushe, da nuna cewa ita ɗin babba ce mai ƙiba da daraja wacce a yanzu ta rasa ko wanne daga ciki. "It's my pleasure, an kawo Raguna na raɗin sunan baby" "ba buƙata" "Akwai" ya furta cikin tsare gida. "Kada ki zama mai son kan ki Jiddo, kada ki zama mai musu after all this am elder than you na je 42 ke kina 35, kin ga akwai respect na girman dana baki" shi kansa mamakin surutunsa yake a yanzu ya manta rabon da ya yi magana mai tsayi, lallai zuciya bata da aji ga abinda take muradi da kwaɗayin zama da shi.. "Khalil na godiya" "Mamin Khalil fa?" Bata ce komai ba ya watsa hannu ya ce "Alright, i don't need your thanks" Ganin yadda take kallo agogo ya sa ya fahimci tana son kwanciya ya miƙe tsaye yana shafa sumar kansa ya ce "Ya Rabb! Good night" Har ya je bakin ƙofa ya sake juyawa ya zuba mata idanunsa ya ce "Lailatan sa'ida" ta bisa da kallo har ya fice. Majeederh Yaronta Khalil ta zubawa idanu wanda yake barci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bata da sanya damuwa a rai, amma kunnuwanta sun kasa manta sautin Abbu da yake cewa "Allah ya isa Majeederh" Ta rufe ido da sauri ta buɗe data tuna kalmar "Tamkar gawa haka ki ke a waje na" "Fasiƙa!" Ƙirjinta ya fara ɗagawa numfashinta na tsayawa ta fara kokawa da iskar dake kaiwa zuwa hunhunta ta miƙe da sauri tare da shigewa Bathroom tana daga tsaye ta sakarwa kanta ruwa mai sanyi shower ta dinga ratsa tsakiyar kanta jikinta ya jiƙe ta mance ciwonta sam, ita da ace ciwon zai zama sanadin tafiyarta lahira da wallahi sai tafi kowa murna da kan ta yarda ta koma wajan wanda ya halicceta ya bata ikon kare mutuncinta amma wani mugu azzalumi ya rusa wannan ƙimar, ya shiga gonar da bashi da ikon ko mallakarta bare ya yi tunanin yin noma ya zuba iri. Ana cewa sai ƴa mace ta bada dama ake cin mutuncinta, kamar yadda kalamar sai bango ya tsage ƙadangare yake samun damar shiga. "Wata bawa dama?" Zuciyarta ta tambayeta. A fili ta furta "Ba zan yafe ba, ko waye na tsane shi Allah ya hana shi kwanciyar hankali" Ta cire kayan jikinta tare
Chapter 11 · 0% Book details