← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 93

Sashe 74

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yana nan cikin babban parlourn na gidan Abbu, Uncle Isma'il da Uncle Bello, Innati,Yaya Bilkisu, Maman Alpha, Anti Hajiya Maryama, Sona, Du'a, Widad, Raihana, Ruma, Aaliyyah, Mami, Jawaad,Sahar. Kaf Familyn Khan General Alpha ne kawai babu a ciki, Idanun Maman Alpha ya nuna tsananin kewar ɗanta da take shekaru sun ja, babu ko labarinsa gashi abin mamaki fur Uncle Bello ya rufe ido akan bai yarda ayi cigiyarsa ba, ko headquarters na sojoji ba a maganar shi har sun yi replacing nasa da wani, kamar wanda aka rufe musu baki aka saka makulin a ruwan maliya. Bayan Addu'a da Anti tayi kasancewarta malama ita ma Yaya Bilkisu ta gyara zama ta ce "Ina Hawwa'u?" A sanyaye Majeederh ta ɗaga kanta ta kasa amsawa, a hankali kuma ta juya zuwa direction ɗin Abbu taga sam ba ita yake kallo ba, ko fahimtar yanayinsa ma ba zakai ba, ya sha shadda Light blue ɗinkin Jamper da babbar riga ba zaka ce haifi ƴar shekaru 31 ba, kullum ƙara fresh yake kuɗi sun zauna jiki ya murje. Yaya Bilkisu ta ce "Wannan zaman naki ne, dominki akai, Majeederh ɗago kan ki sosai ki dubeni" Majeederh ta kalli Yaya Bilkisu "Dubi a gabanki aka haifi Widad yaranta nawa? Du'a, Sahar, Raihana, Ruma gabaɗaya akan idanunki suka zo duniya yanzu ko wacce tana ɗakin mijinta ta rufawa kanta asiri, ke kuma kina nan zaune kina tsofa a gida, Hawwa'u mene damuwarki ne? Kina da kyau, ilimi, boko da arabic, kina da kuɗi kina da asali kowa yasan waye mahaifinki, yau a gabanmu a gaban iyayenki ki faɗa mana mene ya hanaki aure?" A wannan karan ma Majeederh ta kasa cewa komai sai kanta data ɗaga zuwa direction ɗin Abbu cikin sa a Idanunta ya shige nasa daya jima yana kallonta, ya zame idanuna ya miƙe tsaye zai bar wajan Uncle Isma'il ya ce "Daka zauna ai" Ya zubawa Uncle Isma'il ido a hankali ya ce "You can handle it" Ya faɗa tare da gyara zaman babbar rigarsa ya shige cikin part ɗinsa, gorar y ɗauka ya ɓalle wani chaset ɗin magani ya watsa a baki a hankali ya kwanta kan bed yana rufe idanunsa feeling relieved. Majeederh zata tarwatsa masa zuciya da issues ɗinta, Allah ya ware masa ita matsayin ƙaddararsa yaran dake neman ɓata masa suna a duniya, she really disappointed him, actually. Sosai Yaya Bilkisu ke faɗa kamar zata ari baki ta ce "Mun gaji da sanya miki idanu, tunda ke baki amfani da iliminki ba, wallahi wallahi idan baki fito da miji in few days ba zaki sha mamaki, wannan ƙannen naki duk sun fiki martaba a idanun jama'a, kuma tunda haka kika zaɓa aiki da neman kuɗi da kurɗa kurɗa ya fiye miki aure ga Sahar zata haihu sai ki ma zaman daɓaru mutuniyar banza" Anti ta ce "Ki yi haƙuri Yaya Bilkisu komai fa lokaci ne" Yaya Bilkisu ta ce "Saurara Maryama wannan yarinyar dole mu nuna mata ikonmu na iyaye" Maman Alpha ta ce "Haka ne, amma dole a fara binciken daga ina matsalar take?" Mami ta ce "Wacce matsala? Kawai ba auren a ranta tafi gane yawon Ngo ɗin nan da Foundation" Uncle Bello ne ya ce duk yaran su fice, su kaiwa Majeederh faɗa sosai kana ya ce "Ki shiga ki bawa Mahaifinki haƙuri bashi da lafiya" A sanyaye ta miƙe ta nufi ta nufi part ɗinsa tsaye ta gabashi hannunsa riƙe da waya kamar yana kallon wani abu ko dannawa. "Abbu" Cikin sauri ya kifa wayar ba tare da ya ce komai ba, Majeederh ta zube a ƙasa ta ce "Abbu ni mai laifi ce a gare ka, don Allah ka yafe mini In sha Allah zan yi abinda kuke buƙata" Ya juya da sauri ya kalleta a hankali ya ce "Zaki me?" Ta ce "Zan kawo mijin aure" Wani dugun numfashi ya sauke ya ce "Are u sure?" Ta jinjina kai ta ce "Kayi haƙuri Abbu, na sanya maka damuwa a zuciya ban zama yarinyar arziƙi ba, ina ladama da kasancewata mara amfani a gareka, ka yafe mini ka dinga amsa gaisuwata" zuciyarsa ta kare tausayin ƴar tashi ya kamasa ganin ko hawaye ta kasa sai ƙirjinta dake harbawa, ya miƙa mata hannunsa ya ce "Stand up" Kama hannu ta yi ta miƙe, yaro a gaban iyayensa baya tsofa ya taka har gabanta ya saka hannu ya riƙo fuskarta a hannayensa cikin kasa da murya ya ce "Hanyar aljanna nake nema maki, ke ɗin tamkar amana ce dake da Aaliyyah" Ta saki kuka ta ce "Am sorry Abbu" Kasa magana ya yi sai buɗe hannunsa da ya yi ya ce "Come" Cikin sauri ta shige jikinsa tana wani irin kukan farin ciki yau Abbunta ya rungumeta rabonta da jin ɗumin jikinsa tun tana ƙarama. Can ya saketa ya juya zuwa bedroom da sauri.... Bayan sallar Issha tana zaune a bedroom ɗinta dake ba sallah take ba, ta jawo wayarta jin ƙara kafin ta ɗauka ya katse miss calls wajan 10 na gani 7 na Son my world, 2 na Latifa 1 kuma babu suna wata mahaukaciyar special number ce da bata taɓa ganinta ba, number Abraham ta kira tana fara ya ɗaga "Assalamu alaika Baby little me" Tana jin sanda ya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya jin bai amsa ba ta ce "Khalil" Nan ma shiru ta ƙara cewa "Baby are you okay?" Harta fara tunanin ko kiran ya katse ta ji can ƙasan maƙoshi ya ce "Are you crying?" Ta haɗe fuska kamar yana gabanta ta ce "Uhm Baka damu da Maminka ba, no calls no text, anyway how are you?" Ya yi shiru ta ce "Zan ajjiye wayata" Can ta ji ya ce "You're still crying as always, wahh happen?" Ta yi Ignoring nasa ta ce "Khalil ina mahaifinka wai? And ur mother ina ne garinku ina son sani Please kuma dai ba kana cikin wannan yaran bane ko? Baka faɗa da kowa....," A tsawa ce Abraham ya ce "Stop asking too much, why are crying? What's happening eh?" Ya faɗa tana jin yadda yake fidda huci kamar ma baya cikin hayyacinsa, haka kawai tsoransa ya kamata ta fashe da kuka sosai tana marairaicewa ta ce "Shi ne zaka mini tsawa Mamin taka?" Ya yi mata shiru cikin faɗa da kuma alamun damuwa ya ce "Don't let me to repeat myself Mami" Ta ƙara fashe masa da kuka ta ce "To ba cewa akai na fito da mijin aure ba?" Wannan karan a hankali ta ji muryarsa tana sauka ya ce "In english" Duk a tsorace take da tsawarsa cikin turanci ta ce "Abbu da Uncle's ɗina sun yi faɗa sosai wai na fito da mijin aure kwana nan, na rasa yadda zan yi kuma bani da kowa ba wanda ya taɓa cewa yana so na ko da wasa yanzu Little ya zan yi?" Ya yi shiru ta wayar yana jin tashin kukanta ƙit kuma ta ji ya kashe wayar, da sauri ta sake kira ta ji a kashe, sai yanzu take mamakin yadda akai harta faɗawa Abraham a matsayinsa na ɗanta bai dace ya ji wannan matsalar ba, raba dare ta yi tana tunani daga ƙarshe ta yi addu'a ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta, bata kashe wutar ɗakin ba sbd bata son duhu ko kaɗan... Can cikin dare fitsari ya kamata ta buɗe idanu da ƙyar ganin duhu gabaɗaya a bedroom ya sa gabanta ya faɗi, ko nepa aka ɗauke? Ko ai basa amfani da nepa inji ne 24/7 ta miƙe a hankali ta shiga laluba hanya, can ta ji hannunta ya sauka akan chest ɗin mutum ga suma nan fal kwance luff a tsorace take ƙoƙarin cire hannun ta ji an saka hannu an fizgota ta faɗa ƙirjinta baki ta buɗe za ta yi ihu ta ji ya rufe bakin da na....
Chapter 74 · 0% Book details