Sashe 86
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
masa nasan babu kulawar uwa a tare da shi ita kuma ya yi missing, duk lalacewar yaro idan har a gaban mahaifiyarsa yake wlh zai samu nutsuwa da sauƙi wani abu, shi yasa a kullum muke addu'a Ubangiji ya bamu tsayin rai mai amfani mu rayu tare da yaranmu" Ta girgiza kai ta ce "I felt sorry for the boy, his life is full of challenges, wallahi ya bani tausayi yanzu da babarsa na duniya taya zai dinga garari? Ba sai dai su shiga duniyar tare ba?" Uncle Isma'il ya ce "Ƙaddara" Wani irin kuka Anti ta rushe da shi ta ce "Wallahi tallahi na ji gwara ɗana ya mutu ya barni da ace na mutum na barshi ban san wacce kalar rayuwa zai yi ba, ban san waye zai kula da shi ba, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Ubangiji kayi mana tsayin rai mu rayuwa da yaranmu cikin kulawa da amincinka ya Rahamanu ya Rahimu" Uncle Isma'il ya ce "Ke fa daman haka kike babu dama ki ji abu sai kuka haba" Ta girgiza kai kawai wani kukan na kwace mata ta ce "Yallaɓai baza ka gane ba, don Allah ka jawo Abraham jikinka plx" Ya yi shiru for good 3 minutes kafin ya ce "I'll think about that dear" Abraham na kwance saman 3 sitter a haɗaɗɗan parlourn shi kwana uku kenan cif babu inda yaje, duk ya fita daga cikin hayyacinsa. Taj ya kalle shi ya ce "Wani ya yi mini maganar zanen gida da kukai da shi, gashi har time ya shige" Abraham ya yi shiru idanunsa buɗe yana kallon sama alama ya lula duniyar tunani. Taj ya ce "Ina ta magana?" Sai a lokacin ya ce "Ka tura masa kuɗin shi ba zan ba" Taj ya ce "Nawa ne kuɗin?" Shortly ya ce "3M" Joshua ya girgiza kai ya ce "A'a ba za a mayar ba, a bashi haƙuri zuwa wani week ɗin kafin nan sai ka yi" Taj ya ce "Ya ce a mayar kuma daman shi zai aiki tunda ba zai ba bashi kenan ba?" John ya ce "Taj kada a mayar plx mu yi tunanin wani abun" Duk sukai shiru. John ya ce "Kunga news guy's?" Taj ya ce "What news? What's happening in the world?" A hankali ya ce "Wai President ɗin Germany aka kaiwa hari za a kashe shi" Da wani irin Mamaki Taj ya ce "Kashe kuma? President ɗin guda? Kuma a hospital?" Join ya ce "Daman wai jinya yake fa bashi da cikakkiyar lafiya, to a hospital ɗin akai attempting kashe shi amma ya kuɓuta, irin haka dole akwai haɗin bakin wani na kusa shi" Taj ya saci kallon Abraham da idanunsa ke lumshe yana jin duk abubuwan da suke cewa ya ce "Ayya! Shi bashi da ɗa ne wai?" A hankali Abraham ya miƙe ba tare daya kalli kowa ba ya nufi cikin part ɗinsa ya kwanta saman bed, haka kawai ya ji bashi da nutsuwa gabansa sai faɗuwa yake, ya runtse idanunsa sosai a hankali ya ce "Daddy" Majeederh ta kalli Latifa a sanyaye ta ce "Yanzu Latifa ya zan yi? Wanne irin baƙin jini ne irin wannan? Kamar wata mujiya" Latifa ta girgiza kai ta ce "Ki daina cewa haka komai lokaci ne, ƙaddara ce kuma tana da nata lokacin" Ta goge hawayenta tare da yin shiru a hankali ta ce "Surutun jama'a ya fara damuna ana son mini sharri" Cike da tausayawa Latifa ta ce "Duk yadda kake kare kanka ba zaka taɓa hana jama'a faɗar abinda su kai niyya ba, wani ma bai san waye kai ba labari kawai zai ji yaje ya ɗorar ba zaki taɓa yiwa kowa daidai ba rayuwa kawai ki tsarkake zuciyarki" Latifa ta ce "To yanzu da Uncle ya kira Abraham gidan nan parlourn Abbu me zai masa?" Ta girgiza ta kasa cewa komai. Uncle Isma'il ya kalli Abraham ya ce "Khalil me ya kawo ka bedroom ɗin Mamin take few days ago?" A hankali ya ce "Matata dai not Mami" Uncle Isma'il ya jinjina kai ya ce "Ohk me ya kawo ka?" Ba tare da damuwar komai ba ya ce "Just to see her, sai kissing ɗinta da na yi" Uncle Isma'il ya saki baki dan ya san da gaske anyi hakan tunda har ya faɗa don baya ƙarya. Abbu ya runtse idanunsa sosai yana jin kamar zuciyarsa ta fita. Uncle Isma'il ya ce "kiss fa kace Ibrahim?" Abraham ya ɗan kalli Uncle I sai kuma ya kwaɓe fuska ya ce "A small kiss, kaɗan na yi fa" Uncle Isma'il ya ce "Tab ɗin" Uncle Bello shi abin dry ya bashi yana kallon Abraham cike da birgewa ganin baya ƙarya ko kaɗan kuma hakan alamar mutum mai nagarta ce wanda zai iya riƙe amana ta komai. Uncle Isma'il ya ce "Khalil ka san me kake cewa?" Ya ɗan watsa kafaɗa cikin turanci ya ce "Exlty, kwana biyu bata kulani Uncle I ka barni naje ko ɗan hugging nata na yi da kiss ɗin sai nayi ta ganinta a baccina" Kallonsa kawai suke, Abbu kuma ji yake kamar ya shaƙe Abraham Uncle Isma'il ya lura magana ce sosai a bakin Abraham wacce ya jima bai ba dan haka ya ce "Ya akai to yanzu?" Abraham ya gyara zama idanunsa sun yi jajur yana riƙe hannun Uncle Isma'il ya ce "Uncle I Mamina muguwa ce, bata so na ta hana ni sakat a bacci sai na dinga jin kamar gani kwance da ita" Wani irin hawaye ya zubu masa a cikin idanunsa masu zafi wanda rabon da ya yi kuka har ya manta ya ce "Uncle ka aura mini Mami idan na mata ciki zai sanya sunanka ka barni naje wajanta yanzu na yi mata small kiss.......