← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 93

Sashe 23

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me na yi?" "Oh! Baki sani ba?" Ya jinjina kai ta ce "Da gaske" Aliyu Zaki ya gyara zama sosai ya ce
"Firstly duk abinda ya halatta mace taiwa mijinta to ke zero ki ke a nan, ba sani ba ko baki da lafiya ne ko sha'awa ce babu da bakya buƙatar mijinki, baki iya girki ba kullum ina yawon zuwa restaurant sbd kunyar zuwa nake wajan Hajia na ce zanci abinci bayan ina da mata, irin kwalliyya ta mata baki iya ba, ba kitso ba wannan zanen abun ƙunshi, sai tara ƙawayen banza da iska da masifar kishin da bashi da amfani, wallahi wallahi ko zina na fara kece sila Latifa Allah ba zai barki ba, Allah kana kallo duk nauyin daka ɗora mini a matsayina na miji na sauke, kuma in sha Allah sai na auri Majeederh ita ce zata bani abinda nake buƙata ina son mace mai ƙarfin addini da iya soyayya amma ke text message wannan baki sani ba, Mrs zero!"
Yana faÉ—in hakan ya zari key tare da ficewa daga cikin gidan ya nufi Chikenza Park and Restaurant.
Misalin Tara na dare motocin His Excellency Abu-turab suka sauka gidan Uncle Isma'il, cikin sauri P.a ya fito tare da buɗe masa ƙofar mota a hankali ya fito yana zabga ƙamshi Dolce and Gabbana wanda sanyin ƙamshin ke fita a hankali cike da gamsar da mai shaƙar shi. Yana sanye da wata dakakkiyar shadda sky blue ɗinkin jamper da babbar riga ta zauna a jikinsa sosai a wannan lokaci babu ko hula a kansa sbd so yake yau Jiddo taga ainahin kyan da yake da shi, cikin takun ƙasaita kamar wahainiya haka ya nufi cikin gidan Uncle dake sun da zuwan na shi, Jawaad na parlour yana kallon ball ya yi saurin miƙewa ganin His Excellency Abu-turab da kan shi ya durƙosa da girmamawa ya ce

"Wlcm sir" Murmushi Abu-turab ya yi yana jinjina kai "Kana lafiya?" Ya ce "Allahamdulillah, sannu da zuwa" ya ƙara murmushi kawai. Jawaad ya yi masa rakiya zuwa parlour part ɗin da Majeederh ke ciki kana ya shiga ciki ya sanar mata lokacin tana zaune har yanzu ko sauya kaya ba tayi ba ta zubawa Ibrahimul-khalil Idanu. Ta jinjina kai kawai ya san ba zatai magana ba sai kawai ya fi ce. Abu-turab ya kasa zama har tsayin mintuna kusan goma kafin ya ji motsi a bayan shi. A hankali ya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya ƙarasa gabanta yana binta da kallo.
"Barka" ta furta can ƙasa ya ce "Can You remove the cover? Please i want see my wife ba wannan hijabin" Ta ɗago kai ta kalle shi tana son ce masa ya jiki tunda taga harda carnoner a hannunsa. "Please Jiddo, My wife aure ya halatta mini ganinki" ta runtse idanu sosai lokacin daya zare hijabin jikinta a hankali ya jata jikinsa ya rungume sosai yana sauke numfashi da ajjiyar zuciya ya ce "Allahamdulillah, Allahamdulillah, Allhamdulillah! Ina son ki Jiddertul-khair" Rayuwa Kenan bayan tarin ƙalubalan rayuwa data sha ta tsallake ƙaddarori da surutu da zunɗen jama'a yau ita ce matar babban mutum, ita ce first lady? Ita ce jikin Governor Abu-turab Alƙasim rungume da ita yana faɗa mata yana son ta? Sai a lokacin wasu hawaye Masu zafi suka shige fitowa daga cikin idanunta har bata san lokacin data ɗan ƙanƙame jikin Abu-turab ba. Sannu a hankali kamar gilmar fitila cikin duhu rayuwarta ta baya ta fara dawowa cikin Idanunta da tunaninta.... THE BEGIN OF THE BEGINING. Shekaru talatin da biyar da suka shige a baya al'amarin ya fara......

MIJIN MALAMA
Littafin kuɗi ne book 1 and 2 1k ne.... If you read for free🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️
0811923761614
*Duk wata mace yana da kyau, ta nutsu ta bi labarin nan, ko bai zo daidai da rayuwarki babu shakka zai iya zuwa daidai dana wan bak... MATA MA SU JINKIRIN AURE.*

Al'amarin ya fara a garin kano cikin unguwar Ƴan-kaba. Yamma sakaliyya lis unguwar ta yi shiru saboda gabatuwar almuru. Yanayin ginin wajan zai baka tabbacin akwai ƙarancin wadata a cikin mazauna unguwar musamman yadda aka samu kwatoci a gaban ko wanne gida da kuma kan hanya akwai tarin gidaje wanda suke dab da juna kamar tsarin ginin cikin gari. Da sauri magidancin mutumin ke tafiya hannunsa riƙe da wata jakar ƙaramar kai tsaye gidan da ya fi ko wanne muni ya shiga lokacin daya shiga ya samu wata mata tsaye tana goge zufa ya dubeta cikin damuwa ya ce "Ya ya ta sauka ne?" Bilkisu ta girgiza ta ce "Ayya ai sai abin da hali ya yi naƙuda tun jiya ana abu ɗaya sai fama ake, gashi Malam ka ƙi a ta fi asibiti" Malam Abdul'aziz ya haɗe fuska ya ce
"Yanzu nan zata sauka lafiya, ni ban fiya yarda da aikin nasara ba yadda nayi wannan tofin babu shakka zata rabo da cikin salin alin" "Allah ya sa, amma Fulani na shan wahala" cewar Bilkisu.
Ta amshi maganin tare da É—aga labule ta shiga, rawar dai har yanzu bata sauya zani ba. Domin Nishi ake son ta yi amma abu ya gagara. Bilkisu ta ce "Sannu kin ji Fulani" ta bawa wata mata dake zaune gefen Fulanin ta ce "Yanzu Malam ya kawo wannan tofin, taimaka ki É—agata ki bata kin ji Asabe" Asabe ta amsa cikin alhini ta tallo kan Fulani ta shiga mata maganin jikinta duk ya riga ya saki.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, na shiga uku me zan gani ni Asabe Yaya Bilkisu ƙafa ce ta fito, haihuwar dire za ta yi"
"Wanne irin dire ni ƴar nan matsa muga Asabe" Asabe ta matsa Yaya Bilkisu na dubawa ta ga da gaske ƙafa ce guda ɗaya ta fito harta fara bushewa. Suka rasa yadda za su yi hakan alama ce dake nuna musu ruwa ya ƙarewa ɗan-kada. Suka yi rufdugu akan Fulani wacce take jin mawuyacin hali salati kawai take yi gefe guda kuma tana kiran sunan Hawwa'u.
Da ga bakin ƙofa Malam Abdul'aziz ya ce "Ya ake ciki? Ta kusa sauka ko?" Yaya Bilkisu ta ce "Wanne sauka za ta yi dire, Malam ka je ka kawo mota mu je asibiti ko na Murtala ko na nasarawa" sai a lokacin Asabe ta ce "Ai bama za su amsheta ba, domin bata taɓa zuwa awo ba, ko haihuwar Majeederh a haka ta zo mata"
"Ikon Allah, Ubangiji ga mu gareka" da ƙyar suka taimaka mata ɗaya ƙafar ta fito suka dinga yayyafa mata ruwa tare da bata shayi mai zafi cikin sa a nishi mai ƙarfi ya zo mata ta haifi ɗiya mace a karo na biyu. Murna sosai sukai harda hamdala aka yanke cibiya tare da gyara kyakkyawar yarinyar. Malam na waje Yaya Bilkisu ta fito tare da barin Asabe a ɗakin.
"Ga kyautar da Ubangiji ya ƙara yi maka, uban ƴa ƴa mata" Malam ya yi murmushi ya ce "Hakan ma suttura ce Yaya, kuma ina alfahari da ɗiyata Majeederh wacce zata bani abin dana rasa a baya" Yaya Bilkisu ta yi murmushi tana faɗin
"A kan Soyayyar Majeederh baka da ɗauke ƙafa, tana ina ne?"
"Makaranta Yaya Bilkisu, ai tun tana shekaru biyu na sanyata a makaranta gashi yanzu dab take da yin sauka" Yaya Bilkisu ta zare idanu sosai cike da mamaki da al'ajabi ta ce
"Yau na ga abin da ya isheni ni Mai gadon zinare ba bu tausayi shi ya sa gata nan duk a fige saboda tsabar karatu" Wani Uban kira Asabe dage cikin ɗaki ta shiga ƙwalawa Yaya Bilkisu jiki na ɓari har zaninta na faɗowa ta tsuguna zata ɗauka domin gyarawa ashe takalmi ta ɗauka tana faɗin.
"Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Wanne irin ɗaukan alhaki ne haka Asa....," Abin da idanun Yaya Bilkisu ya gane mata ya hanata ƙarasa duguwar maganar data ɗakko. Fulani ce ke kwance kamar Matacciya sai jijjiga take harshenta ya fito waje ga jinin dake fita a ƙasanta kamar an yanka rago.
Yaya Bilkisu dake zuciyarta da rauni tuni ta fara sharɓar hawaye tana faɗin "Oh, mu mata muna ganin jarrabawa a wajan haihuwa rabu ba a tsira ba" Fulani da numfashinta ke sama fuskarta tayi fari sosai saboda jinin daya ƙare a jikinta ta ce "Ƴa ƴana, Ƴa ƴana Yaya a kira mini Hawwa'u kafin na koma ga mahaliccina"
"Assha, Assha daina faɗa mai haƙuri albarkacin haƙurin ki Ubangiji ba zai amshi rayuwarki yanzu ba, ke zaki raini yaranki da kan ki kamar yadda kika haifa" Fulani tayi shiru banda salati babu abin da take ana haka Malam ya shigo jin shirun ya yi yawa. Wani bugawa ƙirjinsa ya yi ganin halin da matarsa Fulani ke ciki, tsananin kyan da Ubangiji ya yi mata kasancewar ta Fulanin Gombe Usul gaba-da-baya Fulanin kuma makiyaya masu kiwon shanu wanda nono ya zamr musu jarin su wanda a yanzu shi ake sarrafawa zuwa madarar Rufaider yoghurt. Tun tana shekara goma sha biyar da haihuwa aka ɗaura mata aure da Malam Abdul'aziz, a lokacin ya ziyarci garin Yobe shi da abokinsa yin dillacin wata saniyya domin kiwo. At first sight soyayya mai ƙarfi tayi dirar mikiyya a zuciyar matashin saurayin Abdul'aziz. Har Ubangiji ya tabbatar da auren su, bata sami haihuwa ba sai da tayi shekaru ashirin da biyar a gidan shi, sannan ta haifi ƴar ta Hawwa'u Majeederh Abdul'aziz Khan! Wacce kamar ka ki tayi ta zubar saboda zallar kamannin da su ka yi. A nan ya samu wadata ya ƙara aure Majeederh na da shekara wacce ya aura ta haihu ta samu ɗiya mace. Kasancewar kwanika take ta sake haihuwar wata ƴar lokacin Majeederh nada shekara huɗu ana haka Fulani ta samu ciki. Har ya isa mizanin zuwa duniya a daidai gaɓar da Malam ya bar gidan domin kawo tofi a lokacin naƙudar da ta ke tun jiya ta tsanan.
Chapter 23 · 0% Book details