← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 93

Sashe 51

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari ya kama weekend ne, Aaliyah na zaune a parlour watching Ds t.v lokacin 10:10 na safiyar Saturday jin ana sallama ya sanya Aaliyah É—ago kanta tana amsawa da faÉ—in "Wasalamu Alaiki, Anti Latifa" Latifa ta zauna tana cewa "Ashe fa yau weekend da tuni kina school" Aaliyah ta yi murmushi ta ce "Ina kwana?" Ta amsa da "Lafiya lou" Sukai shiru can Latifa ta ce "A level nawa kike ne yanzu?"
“... 200" Aaliyah Said, tana ɗan buɗe Idanunta akan series ɗin _My heart knows_ da take kallo a zee wrld. "All The best little sister, ina Malama?" Aaliyah ta nuna mata hanyar kitchen da hannu ta ce "She's in the kitchen" Lura da hankalin Aaliyah nakan series ya sanya Latifa miƙewa ta nufi hanyar kitchen ɗin tana zuwa ta samu Majeederh tsaye gaban sink tana wanke hannunta tayi dariya ta ce "Sannu da aiki Madam koko" Majeederh ta ɗan yi murmushi ta ce
"Uhm" Latifa ta ce "Gasky am lucky na samu abinda nake so"
“... Kike so? Ko ya ke so?"
Latifa ta ce "Shi wa?"
Majeederh ta watsa mata harara tana É—auke plate É—in data wanke ta ce "Nasan ciki ne dake"
Latifa ta ce "A'a ba ciki ba, baya ne dani" Ta faɗa tana tofar da yawo a bakin kitchen ɗin har sai dai Majeederh ta runtse idanu a ɓoye.
"Ni dai zuba mini breakfast yunwa na ke ji" Da mamaki Majeederh ta ce "Idan na baki mijinki fa?" Latifa ta jima tana kallon Majeederh can ta ce "Na yi fa, idan ni nayi bana iya ci sai na kwaɗayi" Bata ce mata komai ba, ta haɗa mata breakfast fal cikin warmer hadda kunun gyaɗa mai kyau, tana bata tayi godiya ta fita a hanya taci karo da Raihan tana shigowa cikin compound ɗin a haɗaɗɗiyar motar ta, bata kulata ba ta fita tare da shigewa nata gate gidan... Lokacin da Raihana ta shiga gidan duk suna parlour suna breakfast ta cire mayafinta tare da ajjiye hand bag ɗinta tana zama saman dining ta ce "Ki ce nazo a daidai" Aaliyah bata ce komai ba haka ma Majeederh, sai da Raihana ta kai abinci bakinta ta ce "Majeederh ba gaisuwa?" Da sauri Aaliyah ta ce "Wakike so ta gaisheki Anti Raihana?" Kai tsaye ta ce "Majeederh?" Baki buɗe Aaliyah ta juya ta kalli Majeederh kana ta kalli Raihana ta ce "Anti Jeederh ce zata gaisheki? Bama ke ki gaidata ba?" Raihana ta ce "Ai ni ya dace ta gaisar" Aaliyah da ranta ya fara ɓaci ta ce "A sbd kin haifeta? Shekaru nawa Anti Jeederh ta baki?" Raihana ta saki dariya hadda buga dining ɗin dake gabanta ta ce "Ji banza wake ta ƙama da shekaru? Ai tunda nayi aure to yanzu ni ce gaba da ita, bayan nayi aure haihuwa zan yi Kinga durƙosawa wada ba gajiyawa bane ko? Ai aure shi ne martabar ko wacce mace, kiyi ƙoƙari ki aure sai mu iya haɗa kafaɗa dake"
Aaliyah ta miƙe tsaye itama tana sakin dariya ta ce "hehehe, matar na tuba bata rasa miji aure, ai dake da Anti Jeederh da ke kwaryar sama ce take dokan ta ƙasa, mene marabarki da ita? Sunan kinyi aure amma kullum kina hanyar barbaɗa na zuwa gida ana ƙarar da albarkar aure akan titi, Anti Jeederh da izinin Ubangiji ba zatai auren barbaɗa irin naki ba, zata auri miji wanda yake kishinta yake sonta wanda zai jure duk wani ƙalubale nata wanda zai sota fiye da yadda take son shi zatai aure inda aka san darajarta, ba zata taɓa auren wanda zai sallamawa duniya matarsa ba" Aaliyah ta riƙe ƙugu ta ce "Mema kika ce haihuwa? Ai sai dai kici ki haifi kashi ba dai ɗan mutum ba, domin juma'ar da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta....,"
Hannu Raihana takai zata kifawa Aaliyah mari tayi saurin ja baya, Raihana na huci ta ce "Zan yi maganinki dan uwarki idan ni sa'arki ce" Aaliyah ta zare idanu ta ce "Ni na isa na haɗa kaina da uwar mata mai aure? Wlh wani ya kalleki sai ya ɗauka kin yi shekaru 20 da aure duk kin rakwaɓe kamar tsohuwar mota" Wani baƙin ciki ya turnike Raihana ta ce "Ni kike faɗawa haka?" Sai a lokacin Majeederh ta tashi ta zabgawa Aaliyah mari ta ce "Ya zama ƙarshe" Aaliyah saka kuka sosai ta ce "Na gaji Anti Jeederh na gaji da abinda suke miki, su basu da aiki sai gorin aure? Kamar ke zaki aurar da kanki sun manta komai lokaci ne? Ita Anti Raihana da take yin ɓari ta taɓa zama ta tambayi kanta me yasa cikin baya zama? Da aure da haihuwa da arziƙi duka na Allah ne, wani jinkirin alheri ne kuma da aure irin nasu wallahi gwara mutum bai aure ba, mata nawa suke aure amma baya zuwa ko'ina auren ke mutuwa" Majeederh na ƙoƙarin yin magana suka ji gyaran murya a tare suka juya Alpha ne tsaye hannunsa harɗe a ƙirji fuskar nan kamar an aika masa da saƙon mutuwa, yana sanye cikin wani jeans da Racing jersey ya saka p.cap a kansa sai ƙamshi yake. Gabaɗaya sukai shiru jikin Aaliyah da Raihana ya ɗauki rawa musamman Aaliyah domin tasan Alpha baya son raini da rashin kunya ga babba bakinta na rawa ta ce "Ya...yaya A.b don Allah....,"
Hannu ya ɗaga mata, idanunsa akan Raihana ya ce "Ke dan kan uwarki Majeederh sa'arki ce?" Raihana ta yi shiru ya ƙara sakar mata tsawa ya ce "Shegiya munafuk za kici ubanki daga ke har mijin da kike tunanin kin aura wanda yasa kikewa wata gori akan haka, duk sanda na ƙara ganin ƙafarki a gidan nan without any reason wlh sai na kusa karya ki" Ya nuna mata ƙofa ya ce "Bar nan wajan kafin na karyaki na karya banza, shi ma mijin naki bashi da tunani bai san ciwonki bane" Ganin ta juya zata shige part ɗin Mami yasa ya nufeta ta kwasa a guje tana kurma ihu ta faɗa part ɗin Mami, tsayawa ya yi yana shirin komawa kan Aaliyah yaga wayam babu ita sai Majeederh dake tsaye. Bai ce mata komai ba ya juya zuwa part ɗin Abbu. Mami ta kalli Raihana dake haki duk tayi wujiga-wujiga ta ce "To shi haka ake bai ji ta bakin kowa ba sai ya hau faɗa?" Raihana ta ce "Shi daman baya son mu ai, ya fi son Anti Jeederh da Aaliyah he's so selfish" Mami ta ce "To ai shi ba Allah bane, kuma ke matar aure ce yana dokanki Shari'a ba zata barsa ba, yabar ganin shi soja ne wlh garƙame shi za ai a bayan canter" Raihana tayi shiru Mami ta kalleta ta ce "Kema bana son rashin ta ido, ina ke ina zabgawa Majeederh wannan maganganun? Kar na kuma ji balle ki ja mini zagi" Raihana ta tura baki Mami ta ƙara cewa "Yau kuma me ya kawo ki?" Ta ce "Jiya da daddare ya dawo, ya kuma da asubar fari a haɗa kayansa wai wani aiki ke ya taso masa" Mami ta zabga tagumi ta ce "Shi kuma ƙaddararsa kenan tafiye-tafiye? Wai aikin me yake ne?" Raihana ta ce "Ni ban sani ba" Ta ce "To Allah ya kyauta"...... Kwana biyar kullum sai Alpha ya zo wajan Abbu ba tare da sanin meke kawosa ba, da yamma liƙis Anti ta shigo gidan ƴarta Sona bayan sun gaisa da Mami ta ce "Ina Majeederh?" Mami ta ce "Ta leƙa gidan Latifa daga nan ance sun fita" Kafin Anti tayi magana Majeederh ta shigo bakinta ɗauke da sallama Anti ta amsa "Daga ina kike?" Majeederh ta ce "Mami gidan Latifa" Cikin faɗa Mami ta ce "Ji munafukar ƙarya ba ance kun fita ba?" Majeederh ta ce "Oh na rakata asibiti na sameta tana ta amai ne ashe ɓari za tai" Mami ta ce "Au ciki ne da ita?" A hankali ta ce "Eh" Mami ta ƙara cewa "Yanzu ya ɓare cikin?" Nan ma Majeederh ta ce "Eh" Mami ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, wannan ɓarinta na uku kenan, mahaifarta ce bata da ƙauri ina zato" Babu wanda ya yi magana tsakanin Anti da Majeederh, Mami ta gyara zama ta ce "To me Likitoci suka ce kuma" sai a lokacin Anti ta ce "Haba Asabe wannan tambayoyi kashi da kashi ita yanzu Majeederh me zata ce?" Mami ta ɗan yi murmushi, Anti ta ce "Daman abin alheri ya same mu" Mami ta ce "Ma sha Allah" Anti ta kalli Majeederh kana ta ce "Alpha ne yake son Majeederh yana son ya aureta" Da wani irin Shock mai kama da mamaki Mami ta ce "Shi Alpha ɗin? Kuma Abbu ya amince?" Anti ta ce "Shi ne ma ya saka ranar auren ai" Da wani irin Scorned expression Mami ta ce "Ikon Allah bani da labari Allah ya sanya albarka" Majeederh ta yi shiru She couldn't say a word sai bin Anti da idanu take. "Majeederh kin amincewa da yayanki kuma ɗan-uwanki Alpha? Kin aminci ya zama mijinki?" Buri Majeederh ta auri wanda ya san kima darajar ta, wannan yasa take yawan kallon Alpha matsayin crush ɗinta take jin inama ya aureta? Ganin bashi da interested akanta yasa bata taɓa sanyawa ranta ba, Majeederh ta tsinci kanta cikin tashin hankali sbd babban burinta ta zama matar A.b Alpha Bello, It's her dream tun sanda ta buɗe idanu ta gansa yana kula da ita, She can't afford to lose him, her life will be incomplete without him, She's felling scared and restless me yasa take jin tsoro?... "Majeederh"
Anti ta kira sunanta. Ta ɗan kalleta kana ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Kina son auren Alpha?" Majeederh ta ce "Anti ai zaɓi ba nawa bane kamar taimakona ya yi" Anti tayi shiru sai kuma ta ce "Shikenan jeki Allah yasa haka ne alheri a rayuwarki" Miƙewa tayi ta shige bedroom amma deep down na zuwarta mamaki take anya shi yace zai aureta? Mai yasa bai fara neman Soyayyarta ba? "Ke da za a taimakawa ina ruwanki da neman soyayya?" zuciyarta ta bata amsa.
Chapter 51 · 0% Book details