Sashe 56
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
sai na fara neman aiki" Abbu ya saki kuka wiwi yana cewa "Faɗa kawai kike Majeederh ki je kawai nama haƙura kiyi aurenki kawai kuma na yafe" A rikice, rikicewar da ko sanda aka faɗa mata Alpha ya gudu ya fasa aurenta ba ta yi ba ta riƙe ƙafar Abbu ta ce "Nayi asara Abbu, rayuwata ta halaka na shiga uku akaina kake zubar da hawaye mai yasa zaka ja mini azabar Ubangiji Abbu Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Abbu kuka kake a kaina??" Ganin yadda halinta ya tashi ƙarara yasa ya ƙara rushewa da kuka tashin hankali ya bayyana akan Majeederh amma ko ɗison hawaye babu a fuskarta zuciyarta ta ƙafe ta ce "Na tuba, wallahi na tuba gobe zan nemi aiki zan fara nayi maka al'ƙawarin wadataka da abinda kake so iya kacin iyawata, za ka yi alfahari dani Addu'arka da albarka ka nake nema kawai" Ya share waye ya ce "Da gaske zaki aikin?" Ta ce "Na yi alƙawari" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya ce "Kin cika ƴa, na gode ƙwarai Allah ya yi miki Albarka" Ta miƙe da ƙyar zata fita ya ce "Ga mata nan da yawa na garari duka babu aure, shi fa auren nan lokaci ne kiyi ta azumi" A wannan lokacin bata fahimtar komai, dishi dishi take gani ga jiri ga kuma haki da ƙyar ta lalubi hanya ta nufi part ɗin tana ta faɗi wanwarsa a tsakiyar ɗakin babu numfashi..... Bayan kwana bakwai da faruwar komai Latifa na driving fitowar su kenan daga B.u.k sun shiga duba wani ita da Majeederh, ganin ta ɗauke hanya ya sanya Majeederh ɗago kai a hankali tare da zubawa titin idanun sai dai bata ce komai ba, ta maida idanunta ta rufe mamakinta kuma bai shige ganin yadda Latifa take wani Mahaukacin driving ba. A hankali ta ce "Kee" Murmushi kawai Latifa ta yi cikin sauri ta ce "Ina da hankali ba kashe mu zan ba, nasan adadin giyar dana saka ban shige limit ba" Ta juya ta kalli Majeederh suka haɗa idanu ta ɗaga mata gira ta ce "Afuwa Malamarmu zan shiga Tahir Quest Palace ne" A gajarce Majeederh ta ce "Hotel?" Latifa ta ce "Eh, Abu zan amsa ai" Majeederh ta yi shiru tana tunani me zai sanya ita kowa ta shiga hotel? Ai hakan babban zunubi ne, kayi ta ganin kartin maza ba zata iya wannan mummunan saɓon ba. Bata ce komai suna zuwa gate ɗin shiga Majeederh ta ce "Wait" "Like how? Kamarya na tsaya?" Ta ya motsa fuska ta cikin liƙab ta ce "Amai nake ji" Jin hakan yasa Latifa tsayawa Majeederh ta fito da ƙafafuwanta daga cikin motar tana fitowa ta ce "Shiga,ki saman nan" Girgiza kai kawai Latifa ta yi taja motar a 150 ta shige cikin Hotel.... Tana tsaye bakin Hotel ɗin ta ji an ce "Malama Majeederh me kike a nan?" Da sauri ta ɗago kanta ganin ɗan unguwarsu yasa tayi saurin jan jikinta baya daidai nan mai napep ya tsaya ta shiga, saurayin ya dinga mamakin ganinta a bakin hotel. Har sama da awa guda Latifa bata fito ba, can sai ga motar ta ganin babu Majeederh ya sanya ta kirata a waya ta ce "Kina ina ne?" A taƙaice ta ce "Gida" "Gida kuma? Au tafiya ki kai" Ta ce "Kamar uzurinki babba ne, ni kuma ina jina Uncomfortable a wajan" Kafin ta yi magana Majeederh ta kashe wayar. Lokacin da Latifa ta isa gida ta samu Aliyu tsaye a balcony sanye da wata farar singlet sai gajeren wando hannunsa riƙe da coke yana sha, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, ta ƙarasa inda yake tana murmushi ta ce "Sweetheart harka dawo?" Bai ce komai ba. Ta saka hannu ta karɓe coke ɗin hannunsa tana sha ta ce "Am sorry" "For...?" Aliyu ya tambaya yana zuba mata narkakkun idanunsa. A hankali ta ce "Da daɗewa, na raka Majeederh meeting ne a Tahir Quest Palace" Ya dinga kallonta sai kuma ya ce "Ohk" ta zauna a cinyarsa ta ce "Me kake yi kai ɗaya?" Ya haɗe fuska sosai ya ce "Ɗaga ni" Ta ɗaga shi ya dinga kallonta up to toe kana ya ce "Exlty, tun jiya kayan nan ke jinki kenan baki wanka ba?" Ta yi shiru ya miƙe tsaye tare bi ta gefenta ya shige ciki, yana zuwa ya haura sama not too long ya fito cikin tattausan voyel fari tas sumarsa kwance luf hannunsa zube cikin Aljihu ganinsa haka ta ce "Ina zaka?" Ya dinga kallon parlourn kamar na mahaukata sai warin yawu yake, Aliyu ya rasa me ma zai ce can ya ce "Ki tabbatar kin gyara gidan nan, Hajia na hanya" Yana faɗin hakan ya fice, ya ɗauki good 20 minutes kafin ya shigo yana fitowa daga mota ya nufi cikin gida, yadda yabar parlourn tun jiya haka yake ya ajiye takeaway ɗin hannunsa cikin ɓacin rai ya nufi bedroom ɗinta yana toshe hanci, ganinta ya yi durƙoshe jini na zuba ta ƙasanta a rikice ya nufeta yana faɗin "Wife lafiya badai cikin ne ya sake zubewa ba?" Cikin mawuyacin hali ta ce "Aliyu shikenan yanzu ma mun rasa shi, na rasa babyna Aliyu cikin ya zube" Gabaɗaya Aliyu ya rikice tashi ƙaddarar kenan ya ce "Taya kika san ya zube? Wife kada ki tarwatsa mini zuciya" Da ƙyar ta ce "Wallahi ya zube" Bai magana ba ya sunkuceta zuwa mota, suna zuwa likita ya tabbatar ya zube Aliyu har kuka ya yi domin wannan shi ne karo na uku.... Majeederh na zaune tana shigar da bayananta domin ta samu offer a B.u.k za tana koyarwa, da kuma gidan t.v akan yiwa mata wa'azi musamman da Ramadan ke gabatuwa. Mami ce ta fito fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Yawwa Majeederh shirya yanzu ki je gidan Amani ƴar wajan Hajiya Nusaiberh haihu tayi kuma babu wanda zai zauna mata" Majeederh ta kalli Mami ta ce "Mami kuma ni zan zauna mata? Ina cewa ko Aaliyyah ta girmi yarinuaty? Ina Hajja? Kakar Amani ɗin?" Mami ta ce "Hajja tana Gombe, yayyun Amani kuma duka aure ne da su Kinga ai ba a ce suzo ba suna gidan mazajen su, Su Raihana ma haka, za a Turo Hajja na ce kawai ta zauna ke kyaci tunda kina zaune gida ke ba aure ba, ki je kiyi mata arba'in ɗan wanki da abincinta dana mijinta" Majeederh ta kasa cewa komai ga biyya da take da ita bisa dole ta shirya ta nufi Badalawa.... Daddare Majeederh ta gama abinci tsaf tana zaune a parlour Amani ta ce "Allah sarki ashe Alpha guduwa ya yi wai za a ƙaƙaba masa ke kuma baya so? Haka Raihana ta ce mini, ni dai don Allah ba ruwanki da mijina daya dawo ki shige bedroom kawai haka kurum yadda mata suke kwantai ki aure mini miji na shiga uku" Majeederh dai ta yi shiru Amani ta ce "Kema dai ƙuruciya ke damunki ina ke ina Alpha? Yaran zamani kenan" Majeederh ta miƙe zuciyarta a ƙun ta ce wai ƙanwar ƙanwarta take faɗa mata haka? Maybe ƴar cikinta da auren wuri ta yi.....Majeederh ta fara koyarwa a B.u.k kuɗi take samu sosai ta zama feminist ɗin dole, a cikin shekarar Abbu ya je makka arziƙi ya ci uban nada, tsakanin Majeederh da kuɗi siyan suttura itama ba da yawa ba gudun kada Abbu ya ce ta kashe kuɗin....