← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 93

Sashe 24

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nishin da Fulani ta yi tare da salati ya dawo da Malam daga tunanin daya lula firgigit ya zube gabanta yana faɗin "Fulani kada kiyi magana haka, ba mu shirya zuwan wannan ranar ba" ta riƙe hannunsa sosai tana salati ta ce "Malam ka kira mini Hawwa'u ina son ganinta, ina son faɗa mata wani abu mai muhimmanci a rayuwarta" Malam ya fara addu'a tare da cewa "Ki faɗa mini ko ma mene, ni ne uban Hawwa'u kuma zan riƙe amana" ta girgiza kai ta ce "Al'amari ne daya shafi uwa da ƴarta, da kuma dangina ka je ka dawo mini da Hawwa'u, dole zata ɓukaci sani a lokacin da buƙatar hakan ta zo" Ta dinga rufe ido tana salati gabaɗaya wajan aka fara salati Yaya Bilkisu ta zari mayafi ta ce "Wacce ƙaddararriyar makaranta ce har kusan almuru? Wallahi yanzu zan je na dawo da ita, Allah ya baki lafiya Fulani"
Tana faÉ—in haka ta yi waje lokacin yaran duk suna makaranta banda guda É—aya.
A hankali Yaran suke tafiya wajan su biyar, uku a gefe guda biyu a can gefe sai. Wacce ta fi ko wacce nutsuwa ta ƙara ƙanƙame Alkur'aninta a ƙirji tana sauke numfashi, a hankali ta yi kyakkyawan murmushi ta cikin liƙab ɗin dake maƙale a fuskarta. Murmushi daya haifar da lomawar dimple ɗinta guda ɗaya. Farin ciki yau take ta ƙarasa bada haddar Alkur'aninta surar ƙarshe kuma shafin ƙarshe na Suratul Bakrah. Latifa dake kusa da ita ta ce "Majeederh kina dariya ko?" Ta jin jina kai ta ce "Uhm, Mimana na siyo mata alawa, kuma zan ga babyn da zata haifa na samu ƙanwa" Latifa ta ce "Laa Mima haihuwa za ta yi?" Majeederh ta bata fiya hayaniya da surutu ba sai ta ƙara jinjina kan ta cikin siririyar muryarta ta ce "E, ba kiga cikinta ya yi ƙato ba? Zan je na ga baby kuma na ce mata na kammala hadda ta yi mini sadaƙa inji Ya mu'alim" farin ciki ya kama Latifa sosai ta ce "Ai nima zani na ga baby kuma ni ma zan ce na kusa gama haddata" Murmushi kawai Majeederh ta sake yi har ranta farin ciki take na ganin ta riga kowa kammala haddar Alkur'ani ga Mima zata haifa mata ƙanwa. Tuna haka sai ya sa ta lumshe idanu tare da rungume Alkur'an ta na ji tamkar ta yi tsuntsuwa zuwa gida. Amma kamar wacce ake ƙara bayar da ita baya sbd yadda take tafiya a nutse da tarin kamala nutsuwarta ta fi ta wata cikakkiyar budurwar. Tunda kuma ta fara girma Abu ya siya mata Liƙab kamar yadda Ya mu'alim ya bashi shawara sbd kyan da Allah ya yi mata na musamman ne tamkar zara ce a cikin sauran taurari ga sai dai ƴar firit take karatu ya sata gaba Islamiyya da boko ga tarin hadisan da Abu yake ƙara mata idan ta dawo, bata barci sai wajan ƙarfe 1 asuba na yi take tashi ta fara karatu.
Sun zo dai-dai wajan wa su matasa wani ya kalleta ya ce "Yarinyar nan daga gani munin ya yi mata yawa, tunda nake ban taɓa ganin fuskarta ba" Wani ya ce "Kuma dai gata kamar fara ce"
"Ahhab, waya faɗa maka fari kyau ne?" Suka dinga surutu ɗaya ne ya ce "Ni kuma nutsuwarta ke birgeni, idan ba makaranta ba ko aike bata fitowa mahaifinta ya gwammace ya je da kansa, amma sauran ƴan uwanta ga su nan kullum suna fitowa" Latifa za ta yi magana Majeederh ta yi saurin riƙe hannunta tana ƙarawa tafiyarta sauri. Burinta bai shige tayi tuzali da Mima ba tana son jin labarin da a kullum take ce mata yana da muhimmanci a rayuwarta. Yau kuma ta yi alƙawarin bata wannan labarin. Farin ciki ya danne yunwar da ta ke ji.

Tazarar gida ɗaya ne tsakanin gidansu Majeederh da na su Latifa, wannan dalilin ya sa ƙawancan su ya ƙara ƙarfi duk da girmewa Latifa da Majeederh ta yi kuma suka samu nasarar shiga makaranta ɗaya daga ta boko har Islamiyya akwai bambancin fahimta tsakanin su, wanda ya sa Majeederh ta fi Latifa gane komai. Tun da ga nesa Majeederh ta hango Yaya Bilkisu tana zuba uban sauri tare da share hawayen da ke bin idanunta. Cak! Ta tsaya sbd mummunar faɗuwar gaban daya risketa Kur'anin hannunta ya nemi faɗuwa ta riƙe sosai fararen Idanunta masu tsari kwance akan fuskar Yaya Bilkisu har zuwa lokacin data riski tsaiwar ta su.
"Allhamdu lillahi, maza zo muje ƴar albarka" Majeederh ta ƙurawa Yaya Bilkisu Idanu domin Allah ya yi mata baiwar fahimtar abu dalilin da ya sa Abu ya ce psychologist zata karanta bayan nan sai ta koma Islamic studies. "Haba Kulun Majade mu je mana" Kamar wacce take karantar zuciyar Yaya Bilkisu ta ce "Mimana? Mene ya sameta? Ta ce zata bani labarin abu mai muhimmanci, ta ce kafin na dawo zata kawo baby, ta haihu?" Tsoron ya kama Yaya Bilkisu ganin tafarar ɗaya Majeederh ta kasance abin da ke shimfiɗe a fuskarta lallai tunani da kaifin basirar Majeederh ya shige shekarunta. Ta ce "Eh, yanzu ma cewa tayi muje ta faɗa miki wani abu" ta tsorawa mata Idanu sai kuma ta sauke ajjiyar zuciya mai nauyi tana jinjina kai. Sauran ƙannenta Ruma da ɗayar kana ta kama hannun Yaya Bilkisu suka nufi cikin gidan domin suna gab da ƙofar dama. Malam ya dinga girgiza Fulani yana faɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, Fulani faɗa mini abinda ki ke son faɗawa ƴarki Majeederh" Ta ja numfashi da ƙyar tana karanta kalmar shahada ta ce "Malam kayi mini wannan alfarmar kamar yadda aka baka ni ina shekara 15, to ka aurar da Hawwa'u a wannan shekarun domin akwai ɓoyayyiyen abu tare da ita don Allah, don Allah..." Kalamanta suka tsaya sbd ajjiyar zuciya da tayi tana ɗaga idanu sama daidai shigowar Majeederh ya yi daidai da wa'adinin rasuwar Fulani........ The destiny was just begun!

Duk wata mace yana da kyau ta nutsu ta bi labarin nan.

MIJIN MALAMA
Paid book
1 and 2 pay 1k to join us 0811923761615
She is too young a lokacin da Ubangiji ya amshi ran mahaifiyarta Fulani. Majeederh ba zata iya cewa ta shiga maraici ba sbd Abbu ya ɗauke mata dukkan wani nauyin na uwa ya haɗa da na shi na uba. Yarinyar da aka haifa lokacin mutuwar Fulani wacce take bin Majeederh ta amsa sunan Aaliyah, motsin kaɗan Aaliyyah zata ce Anty Jeederh domin ita ta kewa kallon uwa mahaifiya, Albarkaci kyauttukan da Majeederh ke samu tun lokacin ƙuruciya har zuwa matakin girma ya taimakawa Abbu wajan rushe gidan shi tare da gina wani sabo rayuwar ta fara sauya musu, ba sauyi mai yawa ba.
After 20yrs
Shekaru sun ja a lokacin da ta kammala karatun secondary wanda ya yi daidai da ƙara yin saukarta ta uku, lokacin tana da Shekaru Ashirin, Ruma kuma Sha Takwas, Raihana nada shekaru Sha Bakwai. Sai Aaliyyah mai shekara Sha biyar. Filin taron cike yake tab, da manya da ƙana nan mutane, sarakuna da ƴan siyasa, sai kuma masu kuɗin jiyar da suka ƙara sawa taron ya yi armashi. Zazzafar Musabaƙa ake gabatarwa tsakanin makarantar su Majeederh Ahlul Madar, sai Nurul huda, a lokacin ne duk wacce ta lashe zata amsa sunan Gwarzuwar Jiha kuma babbar malama wacce zata dinga wakiltar Ƙasar jihar bakiɗaya.
A hankali ta ɗago kanta inda take tsaye tana bin tarin tarin jama'ar da suke wajan da kallo, ta na jin idanunsu a kan ta. Ta samu kanta cikin wani irin faɗuwar gaba, wacce bata taɓa jin irinta ba. "Malama Majeederh, ke muke saurare" aka ƙara maimaita sunanta a karo na babu adadi. Ta rufe ido tare da mai da kanta ƙasa cikin nutsuwa da kamala ta shiga rera karatun Alkur'ani mai tsarki wajan ya ɗauki shiru sai sautin muryarta dake ta shi. Wannan shi ne karo na uku da Malama Majeederh ke jan ragamar musabaƙar makarantar su, wacce ta zame abin alfahari wannan gaɓar ne kuma idan ta samu nasarar lashe wa zata samu zarafin zama gwarzuwa a garin su, kuma ta zama cikakkiyar Malama.
Kammala karatun na ta mai cike da Tajwid da makarujil-huruf ba tare da gyara ko tini ba ya sanya wajan ya ɗaukar kabbara. Ta lumshe idanunta hawaye ma su zafi tun bayan rasuwar Fulani ya samu damar fitowa daga cikin kyakkyawan Idanunta. Gabaɗaya ta cika burikan mahaifiyarta aure kawai ya rage mata a yanzu. Kyaututtuka ta samu hadda kujerar makka Governor dake mulki a lokacin ya amshi sunanta tare da yi mata al'ƙawarin samar mata da scholarship a ƙasar waje. Ba ta yi wata murna ba har suka isa. Mami ce ta riga kowa shiga gida, hakan ya sa ta shiga har ta cire mayafin jikinta ta ajjiye ƴar fos ɗin tata tare da dawowa parlour ta zauna. Tana zama sassanyar muryar Majeederh mai cike da nutsuwa da kamala babu hayaniya a cikinta ta ratsa kunnen Mami. Sauran ƴan-uwanta na biye da ita. Aaliyyah, Ruma, Raihana.
Mami ta dubi Majeederh dake ƙoƙarin shigewa bedroom ɗinta ta ce.
Chapter 24 · 0% Book details