← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 51

Sashe 9

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk wanda kika gani yana zaune a cikin garin Abuja, to ya ci ya tada kai ne. 39) Da wuri suka baro abuja saboda ranar Ishaq zai dawo shi da su Suhail akayo tafiyar saboda rigimarsu. Sai sun biyo shi, ba arziki ishaq ya sha Safeena ya shirya su tunda ba kwana zaiyi ba, ko ma kwana ne ya kama shi ba damuwa zaiyi ba. Jikin safeena har yanxu laulayi take sosai, tunda har karin ruwan anyi mata agida, saboda yawan Amai. Aneesa a tsaitsaye ta gaida Hajiya tace bari taje ta duba jikin Mama zata dawo anjima. Ishaq ya dubeta yace ku tafi da su sultan nima gani nan shigowa, ku gaidata. Sadiya ta taya ta diban kayanta har sabon troley da Ishaq ya saya masu kowa babba, aciki suka xubo kayansu. Shara suka iske Maman nayi a dakinta Aneesa nayin sallama tayi sauri ta amsa tsintsinyar tana cewa Mama kece da shara har kin warware ina Aisha fah? Tace na aiketa sannun ku da zuwa, sannu sadiya kun sha abuja, ashe har da mazajena aka zo. An zo mana da cefane ko ni da Hajiya? Ta kamo su tana tambayrsu, sultan ya laluba Aljihuns ya dauko sabon kudi ya mika mata, yace gashi kudin cefanen. Da Mama da su Aneesa me zasuyi ba dariya ba. Shi ma Suhail ya kwaso nasa kudin ya ba mama akayi ta musu dariya. Su Aneesa suka gaida Mama da jiki. Aneesa ta kara da cewa ai ranar da Yaya ya fada mana kin haihu dan baizo da rai ba nayi ta kuka nace gobe gida zan dawo, maman tace ai kuka? To idan kika dawo me zaki yi mini? Tace abubuwa da yawa zanyi miki mama tunda na san baki da mai taimaka miki sai Allah, yanzun baga irinta nan ba sha naga tarar kinayi. 41) Ji dadi wai duk wanda Ya Ishaq yake sayo musu a Abuja ita baya mata dadin na zaria. Da yamma Aneesa ta fidda tsarabar jama'ar cikin gida ta tafi kai musu, ta shiga dakin Hanne ta durkusa ta bata su subulai da mayuka da turare, en matan dakin sun cikin dakin, uwar ta kada baki tace. Ai fa ansha abuja dole kuyo tsaraba, balle ana tayi musu dawainiyya da 'ya'ya ba dangin iya bana baba. Aneesa na jin haka ta yi saurin mikewa zata fice taji babbar diyar Hanne na cewa, ke ko mama ba dole ba gidan maiko, tafi tafi ma sai kiji wata babbar magana ta bullo hadin zaumuntar dole, ba dangin iya ba na baba. 'Ya'yan suka sheke da dariya. Aneesa da sauri har tana tuntube ta afka dakin Halima, 'ya ta mutanen Abuja tlfy na ganki a hargitse? Aneesa sarkin saurin kuka nan da manyan fararen idanunta suka antayo da hawaye. Halima tace gidanmu ko? Ai shikenan kin dawo za su fara halinsu da kina can abinki kamar kada ki dawo, dibi yadda kika yi kyau kamar wata baturiya, hankalinki kwamce a can, nan ko tsegumi da gulmace2 kadai za su tsangwami zuciyar mutum, kai wannan musibaa Allah ka kawo mana iyakarta $ yanzun me ya faru kuma? Aneesa ta share hawayenta da agefen hannunta ta gayawa Halima cin fuskar da sukai mata daga abin arziki. Halima tayi murmushi tace kai aneesa. Wlh kinso zubda hawayenki a banza ne, yanzun meye sabo a wajenki cikin halayyar Hanne da yaranta? Sharri ko bakin cikinsu wanenen baki sani ba. Ishaq dai abin arziki ya hada uwarsa da taki, har suka zama tamkar sun fito ciki daya, kuma 'ya'yansu dole kuyi zumunci. Har gashi muma muna cin tubarrakinku, ko da yake alheri halinsune, amma ai babu abinda da ba sayi mana na alheri kuma suna amshewa suna jin dadi, amma don butulci irin na mutumin yau, sai kuma sune za ayi wa hassada a bi su da kulli. Shi don Allah ina laifin wanda ke kaunar naka? Mu kam babu abinda zamu ce musu sai san barka. Allah ya ninnunka ma ishaq arzikinsa ya kara budo masa hanyoyin alheri, ki rabu da su ki share hawayenki, kada ma fatima taji wannan maganar ki barsu da sharrinsu. 42) Da dare ne Maman Aneesa ke gaya wa Aneesa wani labari da ya razanar na da ita, Karama yau fa saura sati daya a daurawa Abbanku aure da wata bazawara anan cikin zariya take can bakin kasuwa take. Aneesaa ta dafe kirji tace mama aure? Yanzun abinda. Abba zai yi miki kenan? Alhalin ke da shi ba wata jituwa kuke ba, sannan zai karo wata a tsakaninku, me kika yi masa dai yi miki sakayyar kishiya? Mama tace, kash! Karama ban son jin haka daga bakinki ba, Abbanku yana da halin auren mace uku yanzun ya hadamu, ba shi da rashin wadata, kuma ni banyi bakin cikin aurensa ba, addu'ata dai Allah ya daidaita tsakaninmu, ya sa hakan zai zamo alheri a garemu dukkanmu. Ina fatan idan ta zo zaku riketa a matsayin uwa da kowane irin hali ta zo mu dogara ga Allah don shine shahidi. Dakins Aneesa ciki da falo ne, sai yace su koma dakin mamansu anan ne zai saka amaryarsa, Allah ya sa dakin maman falo ne da dakuna biyu ciki, sai tace su Aneesa su gyara daya dakin, ita ta dauka daya. Gaba daya gidan Abbansu ya saka akayi fenti har da dakin maman sai dai ko tsinke bai bata ba, ko ya canza mata na fadar kishiya ba. Hajiya Ishaq itace ta dinga tausar zuciyar maman duk da dai dama ba wai ta tada hankalinta bane. Hajiya ta bata kyautar wasu lafiyayyun kujeru sets da take ajiye da su awani daki a gidan. Wadanda masu ne kila ko amaryar ba zata zo da irinsu ba, nan da nan Halima ta taya su Aneesa aka fidda tsoffin kujerun mama aka zuba sabbin, ga leda da labule ta siya komai yayi sabo a falon. Da abbansu Aneesa ya dawo ya shigo dakin sai yayi sororo yana kallon dakin tayi saurin gaya masa inda kujerun suka fito labulai da leda ita kuma ta siya da kudin da Ishaq ya bata. 43) Tabe baki yayi yace, ai bansan ke 'yar gatan zuriar Hajiya ce ban tada hankalina inyi miki komai ba, nasan ba zata kyaleki haka ba. Murmushi kawai Mama tayi don ya san ita mai hkr ce, shi yasa ya fadi haka, kuma ya ma riga ya san ko da bata masa hankali ba, amma a zuciyarta sai da tace, oh Allah mutum bai rasa abinda zai kyautata mini inji dadi ba, amma don bai min hidima ba, ko ajikinsa, alhali shine ya cancanci yayi fiye da abinda Hajiya ke mini, amma babu ruwansa tamkar zaman Hajiya da zuri'arta nakeyi. Ranar asabar aka daurawa Abbansu Aneesa aure, kuma aranar ne da dare matar ta tare, wadda a yadda ya gaya wa maman cewa 'ya'yanta 3 mijinta tsarain mota yayi ya mtu ya bar marayu. ************* Zaman su Ya faro abin sha'wa kasancewar Fatima( mama) ta kama girmanta na babban su kuma su Aneesa kanninta sun maida amaryar tamkar uwa kullum ta rugumesu tamkar 'ya'yanta. Addua fatima a kullum take kada Allah ya aiko da baraka, a tskanin wannan zama nasu da amarya ta z da ita ya saje cikin 'ya'yan gidan tamkat nan aka haifeshi. Ashe tsuge bata kare ba wai , an sai biri an sayi kura, en hana ruwa gudu suna nan sun sa idanu, ba haka ransu ya so ba, Hanne da yaranta sun so ne ai sanadin amarya wulakancin da akewa fatima da 'ya'yanta ya ninka na baya sai ga shi suka ga akasjin haka, wannan abu yayi wa Hanne ciwo shiyasa taci alwashin cikin ire2 amakircinta sai tayi kutungwila ta haddasa rikici a gidansu Aneesa, wannan 'ya'yanta take gayan mat, kaji shirme, wai yaranta take batawa. Allah ka ganar da wanda ya kauce hanya, rashin lfya ya samo asaline wata ranata da Fatima bata nan, su Aneesa sun tafi makaranta hadda da suke xuwa a tudun wada wato Nurul tilawa, duk ranar asabar da lahadi, idan suka tafi karfe 8am sai 6pm suke dawowa. MIJIN ARO 1**8 44) Gida ya rage da Basira amarya sai er diyarta, tana ta hidimat dora girkin rana saboda 1pm mai mashi zaizo ya dauko abincin da yake kawai su Aneesa makarantar. Hanne ta shigo gidan saboda taga abbansu Aneesa ma ya tada motarsa ya fita. Basira ta dubi hanne, tace lah sannu mamansu haula, hala en aike kike nema? Hanne ta tabe baki cike da iya haddasa husuma, tace yan aike? Ai 'ya'yan sasan nan basu aikuwa. Ai daga su sai uwarsu suke rayuwa, ko kin taba ganin yaran na shiga wani sasa balle a aike su? Ai gidan nan tsakanin ko da su ido, babu kamar mai kulu2 idon nan irin na uwarta. Mai hali irin uwarta da bata ganin kowa da kima, Basira tayi murmushi tace wa kenan? Hala aysha? Hanne tace wace aysha? Ai aysha ce tayo hali irin na ubanta ai tana shiga cikinmu, Wannan sumuma kashe din Aneesa miskila marar magana irin uwarta, cikinsu fal da mugun abu. Basira tayi murmushi tace, ni kam kinga kaf yaran nan ba wanda jinina ya hadu da shi irin Aneesa don tafi aysha hankali da nutsuwa ga ladabi da biyyaya, ko ubansu na fadin haka, aneesa bata da kwiuwa irin aysha. Nikam ita da uwarta basu da wani aibu bansani ba ko nan gaba ma gani tunda ban dade ba. Hanne tace ai kuwa nan gaba za su fito miki da halinsu na asali, amma yanzun ba zaki gane su ba, tunda ke xuwan yau ce, sai gaba zaki gane idan suka hadar miki kai su tasamma korarki cikin gidan. In banda ke wa aka bari ta shigo gidan, sai ya nemu abu kiji abu rigidi2 sai kuma kiji shiru, anbi dare an bi rana an hana auren kema Allah ne ya nufa ga rabo nan ma kila an samu, tunda jiya nake cema sa ina amarya, yace kina kwance massara ta rufe ki har ina masa tsiya yana dariya, kinga yanzun ko cikin gareki, idan baki sa'a ba sai an raba ki da shi. Ki bar ganin matar nan kamar ta Allah kullum cikin hijab zulum2 mugun abinda ke zuciyarta yafi karfin tunani. 45) Ita dai Basira shiru tayi bayan tace
Chapter 9 · 0% Book details