Sashe 23
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dauka yayi kasa da murya, Haba gimbiyata kiranki fa nakeyi kinki zuwa. Ta dan ja karamin tsaki, ya za'ayi na soma bacci ka dameni da kira me zanyi maka, ni fa na barwa amarya wannan filin. Ya kyalkyale da dariya, kiyi hkr wannan filin ai yafi karfin amarya yarinya irinta, ke dinma ba iya barin mata zakiyi ba kiyi hkr ki zo babu abinda zanyi miki, wani abi zan nuna miki. Da kyar ta zo sai da taja tym. 10) ' Kunga wannan abin da tayi, to anan mata muke barin damar mu, idan za'ayi miki abokiyar zama, miji yana lallabaki, kina botsarewa kina ma sa wulakanci, har ki budi baki kice kin bar mata fagenki na kula da miji. Idan kikayi haka kin fadi warwas, don kuwa idan ta zo taga ke kinja baya to tasan kishine ya sa kika bar mata shi. Idan wayyaya ce wlh sai kin raina kanki don sai ta saye miki zuciyar mijin tsab! Ta yadda da wuya ya dawo miki irin da tunda kinyi sake wata ta maye gurbinki. Ai in kin so kici riba to kada ki fasa abu daya da kike ma na kyautatawa ta yadda idan tazo kin kankane komai na sa har sai ta dinga kokwanto shin wai me ma ya sa ya auro ta ne, alhalin ya san matarsa, in bata kai zuciyarta nesa ba ma ba zata iya hkr ba sai ta furta masa, ki kiga zaman gidan ya gagareta tunda a tsakaninki da mijinko babu baraka ko kankani, saboda haka mata mu kula.' Ta shiga dakin baccinsa tayi tozali da akwatuna a jere, sai ta gintse fuska ta tsaya tace, gani wlh bacci nakeji. Yayi murmushi, amma nan ne gurim baccinki yanzun haka kurum kin canza tsari why feena? Tace haka naga nafi so don banga anfanin zuwan nawa ba. Yace shikenan ni ai na san anfanin kasancewarmu tare, ko ba komai muna kara shakuwa da juna da dankon luv. Kaya ne gasu nan siyo miki. Ki kara dai da hkr, rana irinta yau ne za'a daura auren. Ta sauke ajiyar hrt tace, rana irin ta yau? Lallai Allah ya bada sa'a ya nuna mana ranar. Kayan kam nagode banso ka kara mata don na lura ba wasu ishasshun kaya gareta ba, dama kaine kake mata, er gidan Hajiya da Ishaq. Tana gama fadin haka ta fice a dakinta bugo masa kofar ji kake bam! Ya kurawa kofar idanu tamkar itace ta rikide ita. 11) Ya tashi ya dauki akwatunan daya bayan daya ya kai mata dakinta, tana kwance bisa gado tana jinsa har ya gama sai tayi tamkar bata ganshi ba. Da safe yana kwance a adakinsa ta windo ya hango ta tafita da akwatunan ta compound din gidan ta cinna musu wuta, da sauri ya diro daga gado ya shiga kicin ya sungumi bokitin ruwa ya fita ya shekawa akwatunan. Wadansu har sun soma kamawa da wuta. Ya dubeta yace, safeena ke wace irin mahaukaciya ce? Wlh kiyi hankali da rayuwarki. Don wata rana suturun nan da kika kona su za'a iya wayan gari su gagareki daurawa, kamar yadda kika samu kika wulakanta suke ma ki wulakanta. Aure ne ko ki amshi kayan nan ko kada ki amsa ba zai fasu ba. Sai da duk abinda kika ga zakiyi to ga fili nan. Tace au haka kace ko? To zaka ga kuwa abinda zanyi. Ta wuce fuwww! Cikin gidan ya bita ya sameta daki, yace safeena wane irin lallashi ne a duniya banyi miki ba game da aurenan amma sai botsare min kikeyi, kuma babu abinda ban sanar miki ba game da auren nan yarinyar nan ban furta ina sonta ba. Bani ita akace anyi, kuma wlh ba zan iya cewa bana sonta ba, saboda bani da abokiyar shawara da duk wani lamarina na neman rufin asiri irin mahaifiyar yarinyar nan, ko tym din aurenki kowa yaki bani goyon baya akan aurenki saboda ke ba yareena bace, kuma mu iyayenmu sun fi son duk inda muke mu koma gida mu nemi aure. Ni da na ganki na like sai ke babu wadda tayi min tsayin da ka ta donga bin en uwana da iyayena tana lallashin su. Ita ta shawo min kan su suka yarda na aureki don su basu yarda dansu ya nemo aure a bariki irin abuja ba garin kazo na zo. To ni ko ya za'ayi in guji jinin wannan baiwar Allah, mai kaunata tsakani da Allah kawai don bata raye, tunda idan tana raye wlh ido da kunya ince bana son diyar cikinta, ki kwantar da hankalinki wlh Aneesa ba wata kishiyar da zaki tada hankalinki akan zuwata bane, gidan nan fa sai yadda kike so kikeyi, abinda kika ga dama kikeyi, 'ya'yanki ne kan gaba, to meye damuwarki? Ya tsura mata idanu, ta wani tabe baki, damuwata daya idan ka kawo min yarinyar nan gidan nan. Shine ba zai yiwu ba, indai kana son kwanciyar hankalimnu dukkanmu to ka barta zaria, don ba ajina bace ita da zaka hada mana matsayi. Bata jira mai zai ce ba ta fice a dakin. MIJIN ARO 2**1 **********12) Tunda Ishaq ya bar zaria bai sami komawa ba, saboda yayi tafiya, da ya dawo kuma ayyuka a office sun cakude masa, a gida kuma ga fitinar safeena ta rana daban ta dare daban, duk da dai ita da uwar dakinta kuma Aminyarta Haj. Nuratu sun tako abin da suka taka, hakan bai sa tayi wa zuciyar Ishaq saussauci ba, kullum tsiro da sabuwar rigima takeyi a tsakaninsu, shi dai kullum cikin lallashinta yakeyi. Ana sauran sati guda daura auren ya aikowa da Hajiya katunan biki yace ta aikawa da su Baba sannan a rabawa duk wanda ya dace, itama hajiya da nata dana Aneesa da iyayenta, katunan ma har sunyi yawa, tare da sakon kufi ta account din Hajiya yace su soma duk hidimar da za suyi kafin yazo. Ba shi ya sami isowa zaria ba sai ranar juma'a ana gobe daurin auren. Ita kam Aneesa a wannan tym tana gidansu saboda ranar ne za'a sata alalle, shi ya sa ma bai ganta ba, kuma bai tambayi Hajiya ina take ba, don ya san in dai bata gidan Hajiya tana nasu gidan. Duk wannan ruguntsumin da akeyi Allah ya taimaki Aneesa ta gama zana jarabawarta duka, shi yasa take walwala da fatan samin nasara ita da sauran daliban. Kawayenta da abokan karatunta har party sukayi na murnan candy, ita kam tace ta zatayi ba, sai taga rslt din. To atym din ta gayyato jama'a su tayata murna. 13) Ranar Asabr, 28 august ne aka daura auren Aneesa da Ishaw a kofar gidansu da kenan unguwar alkali da misalin karfe 2 na rana. Daurin auren da ya sami albarkr manyan mutane. Isahq ya gudanar da liyafar cin abinci a congo conference hotel, bayan gama daurin auren. Itama Aneesa Hajiya ta shirya mata walima aharabar gidanta, inda aka kafa runfuna da kujeru, an gayyaci manyan malamai mata na zaria har ma da wasu daga kaduna don abin muhimmi ne. Anyi wa'a zi mai ratsa zukata da kashe gabobi, ita kam Aneesa kuka ta dinga yi. Ranar Aneesa ta sha ado, saboda mai gyarn jiki musamman Hajiya ta dauko aka gyara mata diyarta ciki da waje, saboda tace Aneesa karamar yarinyar ce, zata shiga gidan da aka fita wayau da wayewa, zatayi kishi da wadda tafi karfinta to dole ta kashe ko nawa ne a gyara mata ita, yadda ba zata wulakanta ba ko wanne fanni, don komai tasa an koya mata, ga litattafi na addini da ta bata ta tafi da su ta dinga duba yadda zata gyara zamantakewar aurenta, idan an zarce ta wani fanni wani fannin sai suyi kankan kan. 14) Kyan da Aneesa tayi aranar bata taba yin irinta ba, saboda ita tun asali ba mai son kwaliyyar fuska bace, ashe boye kyanta take sai ranar ne asalin zahirin kyanta ya bayyana. Ita kanta Hajiya duk inda Aneesa ta gilama binta takeyi da kallo saboda bata ga makusa ba a jikin yarinyar har ta zarta matar Ishaq din kyau da kyan jiki, ba irin safeena ba da jin dadi ya sa kiba tana nema tayi mata yawa, mazan yanzun kuma basu cika son mace mai kiba ba, ba sa son ramamma kuma, sun fi son mai fasali mai kyau, wadda jikinta baya boye shape dinta idan tayi kwaliyya. Wasu riga da skirt ne a jikinta anyi maata dinkin na birgewa, ta dora After dress ta yane kanta zuwa kafadanta da gyalen, shine shigar walimar, wadda aka tashi dai2 da kiran sallahr magriba. Aneesa ta shiga bayin Hajiyan saboda Alwala ta gabatar da sallah, a dakin baccin Hajiyan, saboda ganin da tayi babu kowa gidan sai yayar Ishaq Hannatu. Ishaq ya kira Hajiya a waya bayan an dawo masallaci, shi kadai ne a bangarensa sauran abokansa duk suna harabar gida bisa manyan daddumai da aka shimfida musu, Yace Hajiyata yunwa nakeji ko dan irin ruwan lipton din nan mai kayan kamshi ki sa Aneesa ta dafa min tunda ance tana nan dakinki. Tace gaskiyya Aneesa ta gaji bari insa ladidi ta dafa maka, yace yi hkr Hajiya wlh Aneesa Tafi ladidi iya dafa shayin, Ladidi bansan me take sawa ba, sai inji nata yana daci2, haba Hajiyata yau rowar diyar taki zaki min? Allah yunwa nakeji banci komai ba tun safe. Tace dan Anace zan sa ta dafa maka sai a kawo maka. Ta kashe wayar don bata son wani korafi nasa. Ta shiga dakin ta iske Aneesa har yanzu tana kan abin sallah tana aikin addu'o'I, ta dubeta tace rigimmammen mijinki yayo mini waya yanzu wai ki dafa masa ruwan lipton mai kayan kamshi, nace Ladidi tayi masa wai nata ba dadi bata iya ba, ko da can wa ke masa ba ladidin ba oho. Ni zai nunawa duniyanci to ni na haife shi ba shi ba. Tashi kije ki dafa masa ki ba Imrana ya kai masan suna harabar gidannan. 15) Aneesa tace to, ta tashi sum sum ta wuce kicin, ta dora ruwan bisa Gas kenan ya kirata a waya, Allah yasa wayar na hannunta ta dauka a kasalance tayi sallama, yace yanaji muryarki tayi sanyi ne? Kin gaji ne ko? Hala ma kin fara bacci? Tace banyi bacci ba,