Sashe 16
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana kuka tana rokonsa ya bata file din don Allah. Da ta so ta kyale shi ta tafi tasan idan sagir ya dawo dole ya bashi, to amma tana tsoron me zai faru idan ta koma gida babu shi, dole idan abu yayi nisa a san a dakinsu sagir ta bar file din. Da kyar ya dauko ya bata da sassarfa ta fita a dakin tayi saurin ta bar harabar gurin... 76) Gidan Hajiya ta fara shiga saboda ta dan gyara fuskarta ko wanketa ne tayi, dalilin kukan da ta sha. Hajiya na ganin idanunta jajaye ta soma tambayar. Kin koma gida ne? Tace ban koma ba, yanzun na dawo, wani abu ya faru ne? Tace na dauka ko yayanki ya kira ta wayar Abbanku ne yayi magana da ke. Tace meye ya faru? Yanzun ne yayi min waya wai an kwantar da sultan a asibiti, ciwo sosai yakeyi Typhoid n Malaria, Tace subhanallahi! Ban shiga gidan kilan ya kira, Allah sarki sultan ikon Allah kenan gadonsu fah lullube yake da net, ruwa ma na gora suke sha, lallai na yarda duk kariyar mutum sai in Allah yin ikonsa, shiga cikin gidan sauro ko shan ruwan gora bai isa ya hana mutum kamuwa da ciwo ba, idan Allah ya nufa ciwon zai kama mutum kamuwa da ciwo ba idan Allah ya nufa ciwon zai kama mutum, in har kuwa mutum yayi taka tsan-tsan da lafiyarsa yaga cuta bata sameshi ba, ba to kada ya dauka daga gare shi ne, a'a daga Allah ne wannan. Kin amso file din? Ta nuna mata, gashi na ganshi Allah ya taimake ni. Tace, to maza ki kai masa kada kuma kiyi wani laifin. Tace Hajiya zaki duba jikin sultan din ne? Tace zanje gobe Insha Allahu, ina jin ma dake zamu tafi don sultan din ni dake yake ta kira, shi ya sa ma Ishaq yace zai kira Abbanku ya roke shi goben in tafi da ke. Tace, Allah ya sa ya barni, don nima naji ina son ganin Sultan din. Washe gari driver ya dauke Hajiya da Aneesa ya kaisu Abuja, kai tsaye asibitin suka wuce saboda Aneesa tasan asibitin sun taba zuwa da safeena. Yanayin yadda suka ga jikin sultan din abin ya basu tsoro don yana jin jiki sosai. Yana ganin shigowarsu ya miko wa Hajiya hannu ta matsa ta rike shi tace sannu Hassan, Allah ya baka lfy. Ashe haka ciwon ya kamaka sosai. Ya sake mika hannun gurin Aneesa ta matsa ta rike shi, tana masa sannu. Safeena ta matso suka gaisa, suka tambayi mai jiki. 77) Hajiya tace ina su Husaini, yace yanzun dukkansu dadynsu ya wuce da su gida yau duk rigima suke jin tunda muka zo da safe suke kuka, da yake dadynsu ne yake kwana da Sultan din ni sai in koma fida. Bari in sanar masa isowarku, ta dauko wayarta ta kira shi ta gaya masa zuwansu Hajiya yace gashi nan zuwa. Lokacin da ya shig Aneesa zaune take gefen gadon tana ba sultan tea, ya dube su yace, kai! Kai! Aneesa anyi sa'a yau sam yaki cin komai lallai zuwanki yayi kyau, dama tunda ya fara ciwon yake kiran Auntyn zariya da Hajiyan Zariya. Hajiya tace ai gamu munzo ashe haka jikin yayi? To Allah ya bashi lfy. Yace ameen... Sannan ya matsa gefen Hajiyar suka gaisa, yace ina ga tunda kunga jikin nasa sai muje in kaiku gida ku huta, ko da yamma ne sai in dawo da ku. Ya kwashe su ya kaisu gida, suka ci abinci sukayi sallah, sannan suka dankwanta, bayan la'asar sannan suka sake koma. Kwanansu daya a abuja a washe garin na biyunne zasu koma saboda jkin sultan din ya fara sauki, don daren da za su koma gida cewa yayi sai su Hajiyan su tafi dashi gida, ba zai zauna asibitin ba, tace to su tafi ita sai ta kwana da shi, ishaq yace ai ba zata iya rigimar sultan ba, don sam basa bacci ciwon yafi matsa masa cikin dare, da kyar aka lallashe shi suka tafi, sai kuka yake shi dai akai shi gida. Sun idar da sallah subahi kenan, hajiya taji an kirata a waya, Aneesa dake kusa da wayar tayi saurin miko mata tana cewa Ya Ishaq ne. Hajiya ta amsa tana cewa, kila har yanzun rigimar Hassan yakeyi, ina ganin yanzun zan shirya in iso asibitin jira har mafarkinsa nayi. Ta kara wayar a kunne suka gaisa da Ishaq ta tambaye shi mai jki, yace jiki kam Allah ya kawo iyakar ciwo, don gabanin kiran subahi ya amsa kiran Ubangiji, yanzun haka gamu nan tahowa gida. 78) Salati Hajiya ta sa, Aneesa ta matso tana tambayarta abinda ya faru duk da yake ta sha jinin jikinta, saboda yadda taji Hajiya ta saki salati. Hajiya tace Aneesa Hassan ya amsa kiran Ubangiji, Allah yayi masa rasuwa da subahin nan. Aneesa rudewa tayi, ta mike tsaye tana tafa hannuwa tana salati. Hajiya ta riketa tace, zauna ina zaki je? Inda ya tafi muma muna nan zuwa mu same shi, yanzu ko anjima, yau ne ko gobe ne ba sani ba. Tace mominsu ta sani? Tace ban sani ba ko ya kirata ya gaya mata, bari in sameta. Ke kika zauna nan dan ganinki da hawayen nan ita zata rude. Hajiya ta kwankwasa dakin safeena tare da yin sallama, daga ciki safeena ta zo ta bude kofar, tana ganin Hajiya jikinta yayi sanyi, ta bata hanya ta shiga dakin taga su Yautsa bisa kujera an har anyi musu wanka mai ake shafa musu. Duk suka haye jikin Hajiya. Safeena ta gaida Hajiya sannan hajiyan tace hassana har kunyi wanka ne? Yau dai ba sch. Tace, eh asibiti nake son mu tafi da wuri don kwana nayi ina mafarkin Sultan din yana ta bina yana kuka wai shi gida zai je akai shi gida, ni kuma tunda naga ya sami sauki, ko za'a salleme shi ne mu dawo gida tunda yafi son gidan. Tausayin ta ya kama Hajiya lallai safeena bata san danta ya rasu ba, mafarkin da tayi kuma dama tunda taji yana kuka zaije gida zuciyarta ta bata anya yarin nan ba gidansa na gaskiyya yake kuka zashi ba, ita dai tun jiya ta tsinke da al'amarin yaron shiru kawai tayi, ashe tunaninta zai zama gaskiyya. Hajiya tace yayi min waya yanzu an sallame su gasu nan ma tahiwa gida. Tace, an sallame su? Sallama da asussuba? Ko dai sultan din ya mutu ne ya boye miki yace, an sallamesu? Hajiya tace, haba mutuwa, in ma mutuwarce idan yagaya mana mai zamuyi inba hkr ba, tunda ba mu muka ba kanmu shi ba. Allah ne ya bamu aronsa, don ya amshi abinsa saimuyi masa butulci ko waye? Ai kuwa mutwa na sabon da akayi da mutum shi ake wa kuka ba mutuwar ba, da bata tsallake kan kowa, duk zaman ta mukeyi, kinga ki kwantar da hankalinki mu tsaimayi isoawarsu, ki sa aranki abinda ya faru daga Allane, ba wain don baya so Bawan sa bane jarabartasa mu da ta rashi, a'a jarabawace, bawa baya tawakkali to ya ci jarabarwar ubangiji, shi yasa muke addu'a Allah ya sa mu daga cikin musu juriya da dukkan da dukkan abinda Allah zai dora masa. 79) Kuka safeena ta somayi, ta zauna daf da hajiya tace dan Allah hajiya idan ya mutu ne ki gaya min wlh nayi miki alkwarin zanyi tawakkali kamar yadda kika tunasheni yanzun, tunda nasan duk son da nake masa bai kai wanda Allah ke masa ba, fata na Allah ya bamu hkrn jure rashinsa. Da taga Hajiya ta soma zubda kwalla sai ta shiga jero salati, Hajiya ta riko ta tace, kiyi hkr, kiyi juriya, ki yiwa Allah godiya shi ya baki Hassa yau ya amshi abinsa, kiyi masa addu'a rahamar Allah, bashi da hakkin kowa sai dai Allah ya sa mai cetonmu ne. Hajiya ce ta sa wa su Yusra kaya ita kuma safeena tana zaune tana sharar kwalla, har suka ji isowar su Ishaq fargaba ya dinga yi na yadda zai shigo yace ya tunkari Safeena da rasuwar sultan, saboda ya santa yanzun zata hargitsa kanta, bai san Allah ya taimakeshi Hajiyarsa ta sanar mata ba, ta hanyar nasiha da lumana, kuma har tayi tawakkali. Yana shiga dakinta yayi mamakin ganinta a nutse da Hajabi da Casbaha a hannunta tana ja, sai hawaye sa suka ki tsayawa sai sharewa take. Sanyi yaji a ransa lallai kasancewar Babba a guri ma rahma ne don zai aiwatar da abinda tunaninka da hikimarka ba za suyi ba, Hakika ya tabbatar duk iya lallashinsa da dabarunsa, zai yi wuya ya iya shawo kanta har tayi tawakkali haka, mutum daya ce zata ladaftar masa da ita farat daya, itace mahaifiyarta idan ta iso. Ya zauna wajen hajiya suka sake gaisawa, yace zamu shigo da shi a ina zaki yi masa wanka ga mamansu safeena nan isowa da en gidansu. Tace, ka kawo shi nan dakin mahaifiyarsa. Ba'a dade ba iyayen Safeena suka iso da yake tsakanin Unguwanninsu babu nisa, Mamansu safeena da hajiya ne suka yi masa wanka suka gyara shi, aka sallace shi akaje aka binne. Sai da akayi kwana 7 da rasuwar sannan Hajiya da Aneesa suka koma zaria cike da kewar rashin sultan, yaro ne hakurarre mai shiga rai ba shi da hayaniya irin dan uwansa. ********************************************80) A halin yanzun karatun Aneesa ya zo karshe, saboda har sun fara zana jarabawar su ta WAEC, hakan ne ya sa maganar auren Aneesan ta taso gadan2, shi kanshi sagir duk ya kagara ayi wannan auren ko don saboda en tsegumi irin su Hanne da suke ta kai kawo da sukar wannan auren. Kamar yadda mahaifin Aneesa suka sa tym da zarar ta kammala jarabawa, shi yasa sagir yaje ya sami mahaifinsu don a sake komawa a tsayar da takamaimai rana tun da yanzu an riga an sa ranar da zata kammala duka jarabawarta. Sagir ya sami mahaifinsa da maganar, shi kuma sai ya kira iyayensu sagir din don ayi shawara, ashe Hanne na gidan dama tsegumi ya kawota, ita ma matsayinta na babbar yayarsu, sai duka aka kira har da ita, alhajinsu ya gaya musu dalilin kiran nasu suka nuna zahirin murnarsu, aka fara shawarwarin wace rana za'a fitar cikin watan biki, ana