Sashe 34
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kishinta. Yace muna can asibitin ne anyi wasu gwaje gwaje ne shiyasa muka dade. Ya juyo ya mikawa aneesa daya cikin ledojin dake hannunsa yace,gashi magungunan na ciki,ki sha kafin ki kwanta,zan shigo in gani in ma baki sha ba. Ta amsa tayi musu sai da safe ta wuce daki. Tana wucewa safeena ta dubi ishaq tace,amma dai ba asibitin nan kuka tsaya har sha dayan dare ba kun biya wani guri ban yarda kuna asibiti ba yace,to ina zamu biya? Ta tabe baki,ina zan sa ni tunda bana tare daku shiyasa ka qi yarda na biku. Yayi murmushi yace,to ina kike tunanin zanje da yarinyar nan? Ki tuna fa sbda in faranta miki na sagalar da lamarin yarinyar nan,yau kadai don na tausaya mata na bata er kankanuwar kulawa shine abin damuwarki kin dai san babu yadda za ayi yarinyar nan tasha gabanki balle har ta kamo matsayinki,ko me ye naki na damuwa. Haka dai yayi ta lallabata har suka kwanta. Can wajen karfe daya na dare ya lura baccinta yayi nisa,sai ya tashi a hankali ya bude kofa ya fita ya nufi dakin aneesa sbda ya kasa bacci zuciyarsa na gurinta,yana son ya san wane hali take yanzu. 68) Sha daya da minti biyar daidasi suka shiga gida,a falo suka iske safeena ta zubawa kofar falon idanu,tana ganinsu ta sauke ajiyar zuciya tace,haba captain kasa na gaza barci ina nan ina tunanin ina kuka shiga daga zuwa ganin likita,na kira wayarka tana ta ringing baka dauka ba me ya faru ne? Hakika yaji ana ta kiran wayarsa amma a lokacin yana can a duniyar aneesa shiyasa ya share wayar bai ma duba ba balle yasan ko waye ya kira ashe ita ce,lallai da ta san me yake yi a lokacin kila da ya dawo ya tarar ta kusa hadiyar zuciya sbda ya san kishinta. Yace muna can asibitin ne anyi wasu gwaje gwaje ne shiyasa muka dade. Ya juyo ya mikawa aneesa daya cikin ledojin dake hannunsa yace,gashi magungunan na ciki,ki sha kafin ki kwanta,zan shigo in gani in ma baki sha ba. Ta amsa tayi musu sai da safe ta wuce daki. Tana wucewa safeena ta dubi ishaq tace,amma dai ba asibitin nan kuka tsaya har sha dayan dare ba kun biya wani guri ban yarda kuna asibiti ba yace,to ina zamu biya? Ta tabe baki,ina zan sa ni tunda bana tare daku shiyasa ka qi yarda na biku. Yayi murmushi yace,to ina kike tunanin zanje da yarinyar nan? Ki tuna fa sbda in faranta miki na sagalar da lamarin yarinyar nan,yau kadai don na tausaya mata na bata er kankanuwar kulawa shine abin damuwarki kin dai san babu yadda za ayi yarinyar nan tasha gabanki balle har ta kamo matsayinki,ko me ye naki na damuwa. Haka dai yayi ta lallabata har suka kwanta. Can wajen karfe daya na dare ya lura baccinta yayi nisa,sai ya tashi a hankali ya bude kofa ya fita ya nufi dakin aneesa sbda ya kasa bacci zuciyarsa na gurinta,yana son ya san wane hali take yanzu. 69) yayi sa'a duka kofofinta a bude suke,ya same ta zaune bisa sallaya tayi sallar nafila tana ta addua,sai ya zauna a gefenta,dadi yaji a ransa oh ashe dai matarsa mai tsayuwar dare ce wadda ciwo ma baya hana ta yin ibada? Shi bai taba ganin safeena tayi wata sallah in ba ta farilla ba itama a kurarren lokaci ta kanyi wasu. Tare suka shafa adduar da tayi ya dubeta yace,ashe baki yi bacci ba? Tace, eh banyi ba yanzu dai zanyi, yace kin sha magungunan ko? Tace,nasha ai bana kin magani nagi tsoron allura. Yace ashe yau da ance zaa miki allurar da na sha kukan shagwaba. Tayi murmushi ta mike ta cire hijabin jikinta ta dauki rigar baccinta ta shiga bayi ta saka sannan ta fito,ya dubeta yana dariya yace,ni kike gudu kada in ganki?lallai yarinya kina da aiki. Tayi murmushi kawai ta cire ribbon din da ta kama kalaban kanta suka sauka a gadon bayanta ta haye gado ta ja bargo ta kwanta sannan tace masa, bacci nake ji sosai ina ji har da maganin da ke sa mutum bacci cikin magungunan nan. Sai da safe kenan idan ka fita ka ja min kofofin. Yace, nace miki fita zanyi? Kwana na zo taya ki. Gabanta ne ya fadi, wane irin taya kwana sai da bata da lafia ne zai ce zai taya ta kwana, ya dai zo ne ya kara mata ciwo don ba kwana kadai ya zo yi ba. Sauri tayi ta rufe idanunta alamun har ta fara bacci, ya mike yana murmushi ya nufo gadon,ta dan kyala idonta tana ganinsa sai gabanta ya cigaba da bugu fat! Fat!! Har yazo gabanta ya tsuguna ya sumbaci lebenta da kuncinta yace,zan tafi tunda tsoro na kike ji har kina rufe idanu sai da safe, Allah ya qara lafia sai da taga fitarsa taji ya ja mata kofofin dakinta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta soma bacci. Cikin dare wajen karfe uku bacci ya gagari idanun aneesa tunani da damuwa suka baibayeta na irin wannan zaman aure da take yi,kai da mijinka amma babu halin kuyi rayuwa irin ta maaurata sai dai yayi maka komai a boye sbda yana shakkar matarsa yana gudun bacin ranta 70) ko asibitin daya kaita yau ta san karfin hali kawai yayi ya kaita amma shi san bacin ran da zai tadda idan suka hadu,don ta gano hakan a idanun safeenan,ynzu ma wannan shigowar ta san satar hanya yayo ya fito tnda ko da mantuwa kafarsa bata taba tako dakinta ba ko da rana balle da dare irin wannan. Ta tashi ta dauro alwala tayi wata nafilar rakaa biyu bayan ta idat tayi salatin Annabi tare da yin istigfari,sannan ta karanta wannan adduat,tana yaye damuwa da bacin rai,ta saukarwa da mutum sauki cikin lamarin da ya shiga mai tsanani,ga adduar ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZANI,WAL AJZI,WAL KASALI,WAL BUKHLI WAL JUBNI,WA DHALA'IDAINI.................. ........... bai fito ba karshen da kyau sai da onga ta rubuta muku. Cikin ikon Allah albarkacin adduar data kwana tana yi,ga magunguna masu kyau ta sha,da gari ya waye sai ta ji tayi garau, don tun tashin asuba da zata yi sallah sai tayi wanka ta zauna ta tsara kwalliya ta daukar hankali cikin wasu riga da siket en malasia har da gyalensu,kasancewar aneesa ba maabociyar daura dankwali ba sai ta zauna ta gyara gashin kanta tamkar taje saloon ta shafe gashin da mayuka masu kamshi,kai hatta bakin aneesa idan tayi magana dadadan kamshi yake yi,ko wace kafa da lungu da sako na jikinta da zaka shinshina kamshi yake fiddawa,wannan wani sirrine da ba kowa ya sani ba amma ga kadan daga cikin sirrin sam! Aneesa ba ta yarda ta bar wata matsurar gashi ta fiddo gashi a jikin ta ba tare da ta aske ba,don barin gashin hammata dana gaba yana haddasa wari idan mutum jikinsa ya fidda zufa komai tsabtar mutum wannan halitta ne daga Allah,balle ma wasu sam basu iya tsabtace wadannan guraren ba sai mu kula. Ta yafa gyalen bisa kanta ta koma gefen gadonta ta kashingide tana sauraron kiraar abdurrahman sudais da ke tashi a hankali cikin dvd,idanunta a rintse tana tunanin halin rayuwat duniya. Gari yayi haske ta jiyo sallama tare da motsi a falonta alamun an shigo,ta zurawa kofa idanu sbda ta gano muryar mai sallamar 71) Ya karaso dakin baccin nata ya zo ya zauna daf da ita. Ishaq ne cikin jallabiya mai ruwan madara hannunsa rike da carbi yana ja,ga alamu daga masallaci yake dama ya taba gaya mata yana tsayawa daukan karatu bayan sallar subuhi. Ita ta fara gaishe shi,ya shafi gefen kumatunta yace,ya jikin? Ko da yake alamu ya nuna kinyi garau gashi har an tsantsara mini kwalliya. Tayi murmushi ta sadda kanta kasa,yasa hannu ya dago habarta suka kalli juna yace, wai ni har ynzu baki daina jin kunyata ba? Ko da yake laifi na ne da har yau na kasa rabaki da ita,bari zan yi maganin abin. Nan ma shiru tayi ya sake shafar gashinta na gaban goshi data gyara shi ya kwanta lamlam a gaban goshin ya soma shinshinar kan nata, ya ja numfashi ya saukar a hankali yace,wane mayuka kike amfani dasu a kanki da jikin ki har ma turaren ki duk kwaso mini in gani, kin iya zabe don kamshinsu akwai niimar dadi,ga jikinki yayi taushi da santsi, ta mike taje gaban madubinta ta debo masa kayan shafarta ta zuba a gado a gabansa,ya soma dubawa daya bayan daya sannan yace,cikin satin nan zanje england zan dubo miki irin su a can. Tace wadannan ma kai ka sayo su na cikin lefe ne. Yace okey na manta gaskia sun amshi fatarki,kina duba madubi kuwa? Ta amsa da kyar sbda yana maganar ne yana shafar fatar jikinta,ita kuma sai taji wani abu na mata yawo a jinin jikinta. Ya lura sarai ta shiga cikin wani hali amma sai bai daina abinda yake ba,sai ma ya canza salon wasan nasa, ya ja ta ya manne a jikinsa jinsa yake tamkar ya aiwatar da abnda zuciyarsa ke kwadaitar dashi amma sai wani sashe na shaidanin zuciyarsa yana kwabarsa. Ita dai aneesa tayi lamo a kirjinsa ta zama rakumi da akala sai yadda ya juyata duk da yake ya koya mata wasu wasanni amma sam ta kasa yi mai en abubuwan daya koya mata sbda ita wannan alamari ya dameta kullum sai dai yayi wasanni da ita har yau ya kasa raba ta da zullumi da fargabar dake zuciyarta,sannan sai ya gama dagula mata lissafi ya tattara ya kyaleta cikin bege da kewarsa 72) don kuwa gangar jikinta ta saba da wasaninsa,shin wai ina ya dosa ne? Me cece alkiblarsa dangane da wannan aure na su? Ita kam tana gane ta addua ba dare ba rana,ta zuba idanu ta ga shin ina ya dosa ne,kila kuma haka zasu yi ta zama,Allah dai yana gani ita kam!bata cutar da shi ko tauye mishi hakkinsa ba,Allah ba zai kama ta da laifin hakkinsa ba,ita nata hakkokin da yake tauyewa ta yafe masa tana adduar Allah ya karkato da zuciyarsa ya gane gaskia ya dawo hanya mai kyau IJIN ARO 2***8 Shinshinarta yake yana lasar fatar jikinta tamkar zai cinyeta, dadin kamashin turarukan jikinta