Sashe 42
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayani komai ran hajia yai mugin baci na wannan tozarcin da yasa matarsa tayiwa aneesa don ita a cewarta shi yasa ta..in ba shi uasa ta ba ya akai ta san sirrin miji da matarsa..Hannatu tace hajia sai ta yiwu bai gaya mata ba makirci ne irin na kishiya ke baki san sharrin kishiyoyi ba ne mu da muke da su mu zamu baki labarin tunda ke baki taba zama da kishiya ba gashi ma aneesan tace yayi.mata rantsuwa shi bai fa mata ba 100) yayi mata rantsuwa bai taba gayawa safeena komai tsakaninsu ba karya take masa ke dai ynzu hajia gyara yarki zaki yi yanzu ki nema mata tsarin jiki kafin ta koma ran hajia a bace tace ba inda zata koma in ma zata koma sai ya dandana kudarsa ya gano.kurensa amma ba yanzu ba ki barni dashi basu isa su wulakanta mini aneesa ba in kyalesu daga shi har matarsa hannath tace..dama ai dole a kwatar mata yancinta a gidan na amma maganar ta zauna anan gurin ki ba zata yuwu ba shi da matarsa suna can ai murna zatayi dama haka take.so bata son kowa ya rabar mata gida kamar nata...bama aneesan ba har shi ma sai an ta masa rokon Allah ana nema masa tsarin jikinsa don matarsa makirar gaske ce hqnnatu ta dade suna shwarwarin da hajia sannan ta tafi da sharadin zata dawo washe gari don tana skn ganon kanin nata kafin ya koma. Washe gari tun misalin goma na safe hannatu ta isobgidan tana gaida hajia ta wuce sassan kaninta inda ta iske aneesan.na can tana hada masa abin karyawa yana zaune gaban aneesan tamakar ya shige cikin.jikinta aneesa na ganin hannatu duk sai ta rude kunya ta kamata dama tun kafin yaba hannatu izinin shigiwa aneesa ta so.matsawa yasa hannu ya tokareta ya hanata motsi shine har ta shigo ta gansu a haka...a kunyace aneesa ta gaida ita tayi saurin mikewa zata bar dakin ya rikota yace ina zaki baki bani abincinba? Zan.bar miki abinki ta sunkuyar da kai cike da kunya tayi shru yace ina ruwan yaya hannatu da sabgarmu yadda kika saba bani a baki a gida yanzu ma haka zaki.mun...yaya hannatu wayyaya ce yae boko ita ma da kike aninta soyayyarsu suje a tsihon mijinta ballae mu yan yara....hannatu tace amma wlh ishaq baka da kunya ko a yake hajia ce ta sangarya ka ta kyale ka ko agabanta kana zuba rashin kunya kinji aneesa wuce ki tafi kada Allah yasa yaci abincin shi zai.kwari.kansa...aneesa da saurinta ta fice. 101) suna dan hirarsu har ya gama karyawa sannan hannatu ta sako masa zancen gidansa da ya kwana yana ci.masa zuciya yayi.mata rantsuwa shi bai taba gauawa safeena irin wannan maganar ba shi ai ba jahili bane da zai zauna yana gaya mata sirrin mace er uwarta kitifi ne kawai na safeena ta hada don taga aneesan yarinya ce anan ne ya gaya mata abu daya a ya sani yace wani likita aboki na ya bani shawarar in hada mata zuma da zam zam a kayan marmari to ina hadawa a dakina ta shogo ta gani ina jin hasken a ta samu kenan tayi wannan karyar hannatu tace shikenan yanzu hajia tace ka bar mata ita aneesan anan sai ta kwana biyu sai kazo ka tafi a ita...yace gsky nafi so mu tafi tare da ita na riga na saba a yarinyar rashinta kusa ani zai zame min wani gibi nifa in ba da wannan matsakar ba dari bisa dari aneesa bata da aibu aguna idan ma kuka barta agurina ina bin shawarar abokina likita matsalarta zata zamo tarihi tace wannan maysalar bata likita bace ni nan bisa ga bayanan da kamun na gano inda matsalar take nan a sati da izinin Allah komai zaiyi ai dai. Hannatu ta sami hajia tai mata bayanin yanda sukai dashi ta ce ita yanzun zata wuce a ita gurin yaya balarbe ya ganta in ma sihiri akayi mata zai gaya mana kuma in sha Allahu zai karya shi...in kuma bashi bane zai gaya mana sai mu san mataki na gaba da zamu dauka in haka halittar take ai akwai kayan gyara na zamani a na addini. Malam balarave yayan mijin hannatu ne gudansa na mkwabtaka da na hannatu...ko gidan hannatu basu shiga ba suka isje shi a gidansa..hannatu tayi masa bayanin kadan na matsalar aneesa ya dabyi shru sannan yace gsky akwai sihiri sisai ajikin yarinyar nan amma in sha Allah zan karya shi...yanzu bari in bata magani tasha tayi wanka dashi na sati daya a izinin Allah sigirin jikinta zai karye kuma ba dai sharrin mutum ko aljan ba sai kadarar Allah. MIJIN ARO 2***11 102) Hannatu tace yaya shima ishaq ka bashi maganin karya sihirin in bashi don shima ba garau yake ba..malam balarabe ya hada musu magunguna sanna suka awo ba tare da ya karbi ko sisi ba don yace da hannatu da ishaq dik kannensa ne zai iya masu abu tamkar yadda zai ma jininsa. A ranar lahadi ishaq yai niyyar komawa Abj ransa duk a bace sbd hajia ta hanashi tfy da matarsa Hannatu ta bashi magungunan nan cikin hikina ta nuna mai yayi komai a sirrance tunda komai yana son sirri anufinta kada matarsa yta gani ta hana shi amfani dashi ki ta salwantar dashi. Kwana 7 da Aneesa tayi tana amfani da maganin nan da yin wanka ita kanta taji wasu canje canje ajikinta sai tana jinta garau begen mijinta na damunta wani abu ma da bata taba jiba na sin.kasancewa da mijinta duk yanzu tana jinsu balle da ya kasance kullum suna.manne da juna a waya sai abin.yafi damunta amma bata taba gaya.masaba ko sunyi waya nuna masa take yi ita ba yanzu zata koma Abj ba. Sati dayan na cika ishaq ya iso.zaria a ranar asabar a rana wani irin kyua aneesa ya ga tayi masa jiyayi kamar ya sure ta ya gudu ko.kuma ya sanyata cikin cikinsa dama ta riga ta san a zuwansa yayi.mata waya shi yasa da kanta ta shiga kicin da kanta ta shirya masa lafiyayyen abinci a abubuwan sha...ita dai hajia na kallonta duk ddi ne ya cikata ganin duk wannan rawar jikin da aneesa keyi tun wayewar gari domin danta take yi don ta faranta masa ransa sai dai hajia tasha alwashin sai ta gara dan nata kafin ta bashi matarsa balle yadda ta kashe kudi ta gyara diyarta ta yadda mijinta ba zai sake.ganin wata tawaya a tare da ita ba balle har ya goranta mata ko yayi wani nuni da kishiya zata sami abin kararwa tana yin kisisina akansa. A falin hajia yaci abinci har ya dan kwanta ya huta daga bisani ya fita sallar laasar daga can yace zaije......... 103) zaije ya jwanta Aneesa ta tmbyeshi mai za adaa yace na baki zabi ki dafamun duk abinda kika san zai faranta raina ina so...ira a ladidi suka shiga kicun din suka yi sakwara sukayi masa miyar zallar agushi wadda ake yi da busashen kifi a jada a nama...rayi masa lemin kwakwa...tayi masa farfesun kifi mai rai a lafia(kina iya fuba luttafina da ya fito ksw...Sirrin girke girke) a falinsa yace ta shirya masa komai sbd haka umarninsa tabi ta shirya kayan yadda ya kamata tazo tayi kwalliya irin wada yake so duk da tana jin kunyar hajia hakan bai hanata yiwa mijinta abinda tasan yana so ba bai shigo gudan va sai bayan sallar ishai ya iske su a falon hajian suna kallon tauraron dan adam (saudi one) dawafi suke kallo ya dan zauna suna hira bai dde ba ya tashi ya dubi aneesa yace abincina fa tace yana can sassanka tun dazu na kai maka yace ok..bari inje inci yunwa nake ji na sha zirga zirga ya wuce ya barta a hajia bai de ba ya kira aneesa a waya yace ni kaai zanci abincin ta dan dubi hajia ta rage muryarta tace na riga naci nawa...yace to ni kizo ki bani in ba haka ba ba zanci abincin ba...tayi kasa a murua tace kayi hkr to ka fara ci yace to ai ban iya zubawa ba kizo kawai tace to ganinan (oh su ishaq an iya shagwaba) ashe duk wannan boyon da kasa da muryan a take hajia na lura da ita ba dai ta jin abinda take cewa ne. Tana nan zaune ta rasa yadda zatayi taje gurin mijnta kuma tasan halinsa idan bataje ba ba zaici abincin ba can ya dameta da kira a waya taki dauka tasan ai zancen guda daya ne...hajia ta dubeta tace ba kiranki ake awaya ba tace Flashing ne da yaga bata daga ba sai ya kira wayar hajia yace dan Allah hajia ki turo mun diyarki ina kiranta awaya taki amsawa nasan umarninki take jira ya kashe wayar...murmudhi kawai hajia take tana girgiza kai..... ta dubi aneesa tace ki tashi kije mijinki yana kiranki dama shi ya addabeki da kira to ki kula kada dai ki biye masa kin san baki gama shan naganinki ba ki bar ni dashi sai ya gane martabarki ta diya mace karyar tsiya yake...ita dai aneesa ba tace komai ba a zuciarta tace ai hajia ko baki gargade ta ba ita ba sakarya bace bayan ya gama kwance mata zani a kasuwa kishia ta gama sanin ita bakomai bace ba sannan yanzu zai zo yana mata rawar kafa duk da dai ance sihiri akai mata ai da bata tozarta haka ba har ta nuna ta fita. Ta shiga daki ta yafo gyalenta tabi ta kofar kicin ta fice dan bta son ta kara hada ido da hajia. A aaune ta sameshi ya tasa abincin agaba ya zubawa kofa idanu...yana ganinta ya sauke ajiyar zuciya yacr aneesa dan kinga na damu dake shiyasa kike gara ni...lokacinki ne zoki zauna ki bani abincin in kuma baki gama yangar ba sai na hakura...ta zauna tana murmudhi.Tace Allah ya huci zuciyar yayana...ni na isa na maka yanga...ni wacece yace wlh ke komai na ce a rayuwata kina kokwanto ne tace kai dai ayi shru a inda ba kowa anan nake komai a gurinka amma masu mulkin zuciyrka su suke a komai...ya dan rage faraa yace aneesa abar tuna baya wai gyartai yaci sarauta yana kan kujerar mulki ya dubi jamaa yace to