← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 51

Sashe 2

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya baci,, ni tun da na shigo nake jin ihu na dauka nmakwabta ne ashe a cikin gida ne. miko mmiko min bulalan. ya mika masa yana huci tamkar wadda yayi tseren mil dari. aa asa ydb hi aharzuke yace, kg ta ko dubi jkin yarinyar nan sai fidda jini yake tamkar ba kai ka kawo ta duniya ba, wannan zuciyar taka babu inda zata kaika Wata rana sai kayai da na sanin don irin wannan dukan wata ran zaka nakasa ta, babu gaira babu dalili, Allah ya azurtaka da yarinya mai ladabi da biyayya amma baka gani, wlh ka sani 'ya'ya amanr Allah ne, kuma ranar kiyama sai ya tambaye mu. Abban Aneesa ya nunata da yatsa yace wannan yarinyar kome nace kada tayi sai tayi mai taurin kan tsiya ni kuma nine maganinta, baban sassa yace ni ai har yanxun baka fadan laifinta ba, yace aiki na hanata yarinya duk tabi ta tsotse ta kwandare saboda bauta, idan subahi yayi ta soma aiki bata hutawa sai ta tafi mkrnta, idan ta dawo ko kayanta bata cirewa take fara aiki, ita uwar da yakamata tayi, sai ta kiyi ta kyale er haka, ko wace mace ai ita ke aikin gidan mijinta. Baban sassa ya hau salati ni ban taba ganin Uban da yake hana 'ya taimakawa uwarta ba, mu ga su can kullum fama muke da su taimakawa iyayensu sunki, kullum sun gwammace su yi wanka su nade a gado suna kallon iyayen na aiki. kai haka kake so Aneesa itama ta haye gado ta kwanta tana kallon uwarta tana aiki taki taimaka mata? haba Ali? to lallai ka sake tunani dan hakan sam ba zai yiwu ba, har ya sa kai zai fita sai ya dawo ya dubi Aneesa yace, ta so muje in sa a gasa miki jikinki nan da ruwan zafi, sai ki sha magani ki kwanta. Ya dubi dan uwansa rai bace yace kuma wlh kada ka sake taba lafiyar jikin yarinyar nan. Aiki kuma dole ta taya uwarta shi, tunda nau'I ne na koyi da akwa yara su horu kafin suje gidan aurensu.... 10) Baban sassa(Haka suke kiransa) ya damki hannun Aneesa suka nufi can sassansa zuciyarsa a kufule. yana kwalawa uwar gidansa kira. ke haanne! Hanne! ina kika ne? ban san me kike yi ba ina ta kira kinyi kunnen uwar shegu da ni. da saurinta ta fito daga ban daki hannunta rike da bokiti da kwandon wanka, daga wanka take amma duk ga kumfa nan ajikinta tabbacin bata gama wankan ba ta sheka ruwa ta fito saboda irin mafarutar da taji maigidan na kwala mata. tasan idan bata fito ba to fadan da ta tinxiro shi daga inda ya fito a kanta zai kare. ganin shi rike da hannun Aneesa ya sa ta gintse fuska. ai fa an tabo 'yar dan uwa, shi a dole sarkin zumunci. ita ta rasa wannan jarabar son 'ya'yan 'yan uwansa gara ka taba dansa, su kuwa 'yan uwa kowa kowa nasa ya sani, amma shi banda shi, balle Aneesa da uwarta da yake ji da su kamar me. a cewarsa in ba ayi zumunci a duniya ba dole za ayi a kiyama ita kam duk wanda baibi da zumuncinsa ta kanta da 'ya'yanta ba to ma'asalam ayi alahira, amma a duniya kowa ya ja 'ya'yansa yayi zumunci da su. Ya dubeta yace duba min nan ki ga aikin Ali na rashin hankali ace dan ka haifa ne za kayi wa wannan dukan kawo wukan, ina ga dan wani kuma, shi dai ya daki 'ya'ya tamkar jakai duka ai ba ya gyara tarbiya yaro, illa ma ya kangara shi. yanzun Aneesa guda nawa take? sannan meye laifin yarinyar nan? duk gidan nan ai ba da mai bin iyaye da jin magana irinta, amma shi baya gani. hanne ta dada tunzura abinda bata kaunar afada shi kuma kullum sai ya fada babu mai tarbiyar Aneesa duk cikin yaran gidan nan, wato na su 'ya'yan basu da tarbiyya. ta tabe baki tace, ai fa babu mai jin maganar iyaye irinta shi yasa naga tambarin dukan iyaye a jikinta, in da mai jin magana ce ai da kullum ba za a dinga jibgarta tamkar jaka har aje kwatarta ba. ya ja tsaki twiwwww! ni ba wannan na tambayeki ba, yanzun dai ruwan zafi nake so ki dibo ki gasa mata jikin nan. dubi shaidar bulala sai kace ba dan mutum aka daka ba, in banda rashin yi wa kai adalci, yaushe za'a ce yarinya ba zata yiwa uwarta bauta ba, sai dai tayi kwance tana kallon uwarta na aiki. 11) Ni gasu nan ina fama bamai yin cangal kodayake ba laifinsu bane ko yi akayi musu. hanne abin ya sake tinxurata tayi janyar dakinta tana cewa, bani da ruwan zafi kasan yaran sasan nan ko ruwan tea ba sa azawa a wuta balle a sami rahiwa, ga su can kwance. martani ta mayar masa jin haka yasa ya bar ta kanta ya kwalawa amaryarsa kira, ke Halima? hala barci kikeyi? ta fita daga dakinta sanye da hijab tace, gani sallaj nakeyi me ya faru? Tana kai ganinta jikin Aneesa ta saki salati, Lah ila ha illahu, me ya sami Aneesa? ya fada mata abinda ya faru ya kara da cewa in akwai ruwan zafi gasa mata jikinta dan Allah. Tace bari in duba kicin din in ma babu sai in dora. ta nufi kicin din wuf Hanne tayi ta fito daga daki ta nufi kicin din tana ce mata. kada ki kuskura ki debi ruwan zafin da na dora yara zanyi wa wanka, sai dai ki sa wani tunda ke wahalallace mai neman suna, ni kam ba zai yiwu ana aibunta mini 'ya'ya akan wannan mai tsayayyen idon ba ni kuma ni tausaya mata. Halima bata ce mata komai ba saboda tasan idonta tanka ta yanzun z aji kansu sai ta koma, ta hada wuta nan danan ta dora ruwan da zafinsa sosai ta juye suk je bayi ta gasa wa Aneesa jikinta sannan tace ta tube kayan ta tati wanka da sauran ita kuma ta fito. Halima halayyarta daya da na mai gidan tana da kirki da son zumunci, duk fadin gidan nan ita da maigidan ne masu kaunar Aneesa da mamanta kuma suna tausaya musu halin da suke ciki$ in dai Aneesa tayi ba dai2 ba ro kyas Hanne ke jira ta zayyanewa Mahifin Naeesa. idan ya shigo sasansu, shi ya sa tasu ta zo daya. asalain iyayen Aneesa Haifaffun zaria ne gaba da baya, unguwar alkali dake birnin zazzau. gidansu babban gida ne m- umheda ssa3, na farko shine nasu Aneesa, mai binsa na Baban sasa shine wasu ke cewa Baba amadu, sai na can kurya gidan kankkaninsu mahaifan iyayensu, wanda Alla yayi wa rasuwa shi kakkan nasu da uwar gidan sai mai binta ke raye a sasan tare da autan gidan Baba adamu da matarsa. 12) Sauran duk suna wasu gidajen nan kusa. Maihafin Aneesa shi kadai mahaifiyarsa ta haifa sai ta fita a gidan taje ta haifi wasu 'ya'yan a wani gidan. shi ya sa tun a wancan tym din ya taso cikin en uba wadanda baiki dadin su ba ko kadan kuma shi kadai ne yafi dagewa wajen yin karatun boko tare da taimakon dangin uwarsa wanda idan larurorin makarantarsa ya tashi can wurin kakkaninsa yake xuwa su tallafa masa. A haka har ya kammala secondary aka zo cuku2 shiga jami'a wadda a wancan tym din ba wuyar samu gareta ba dan ba zancen JAMB KO POST UME indai sakamakon yayi kyau to sai shiga jani'a tunda ba kowa keyi ba tym din ba. Allah ya taimake shi yayi jami'ar har ya kare wanda kafin ya kare Allah hada shi da Fatima wato mahaifiyar Aneesa da suke tudun wadan zaria. ko da zai tafi bautar kasa a calaba, magana ta soma yin karfi duk da dai an sami takun saka daga marikiyarsa mahaifiyar baban Sasa. tace wai ga 'yan mata nan birjiki a cikin zaria ga su ba zai zaba ba sai ya tsallake tudun ya dauko musu gogaggu. saboda tym din gani ake haifaffen cikin city iyayensa basa lamuntar ya auro 'ya daga tudun wada sai dai anan zarian. tsiarrau daga cikin dangi ne suka bada goyon baya tunda an bincika Fatima 'yar babban gida ce kuma gidan dattako. shi yasa aka yi baiko da sa rana amma sai ya kammalo bautar kasa ya dawo za ayi bikin ko da bai fara aiki ba. cikin yardar Allah yana kammala bautar kasarsa ya samu aiki da gurin da aka tura shi bautar kasar. a son samun mahifinsu ya dawo ya sami aiki nan zaria in an kai da nisa ko kaduna.amma sai ga yadda Allah tsara lamarinsa haka nan ya dawo calaba ya soma aikinsa har zuwa tym da akayi bikinsu. MIJIN ARO 1**3 Iyaye sunki yarda ya tafi da ita can cala dole anan gida zaria ya barta aka kbe musu sasansu daban. aure ne na soyayya akayi. shi ya sa duk da kunya da kawai na wancan tym din amma bai hana ma'auratan gudanar da soyayyar mai karfi cikin zamantakewar auren su ba, wanda ko yaron goye ya zauna da su na 'yan dakikai zai gano hakan. ya kasance komai mahaifin Aneesa ya samu gida yake kawowa, shiyasa Fatima ta wadatu da komai najin dadi. duk da yana can calaba sai karshe wata yake xuwa, amma bata rasa komai, sai ya kasance duk yafi 'yan wuwansa samu matan yayyinsa na jin dadi wannan ne dalilin da ta samo kiyayya a zuciyar narikiyarsa da sauran matan gidan irin su Hanne. Halima ce kawai jininsu ya zo daya. kuma bai ga za da hidimta musu ba. amma sam ba su gani wanda yake mata ne kadai ya tsole musu ido suke hassada. kwatsam laulayin ciki ya saka Fatima agaba. atym din kuma Ali yana Calaba gashi ba wayar hannu balle gaya masa, hakan nan tayi ta fama da ciwo babu mai taimakata mata sai Halima itama a boye saobda sarakuwarta ta sa musu ido har da gori wai don ta sami abin lasawa ne take xuwa ckin amai. ita kam don zumunci takeyi kuma mijinya ke turata aboyr saboda kada ran mamansa ya baci, amma a zahiri yana son a dinga shiga ana taimakwa
Chapter 2 · 0% Book details