← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 51

Sashe 43

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kar inji an tuna baya to nima haka name so tunda kin dora laifin akaina to na na da gammo na dauka sai a yafemin...ita dai bata ce komai ba ta janyo filet ta fara zuba masa farfesu yace farfesu zanci ba abinci ba? Tace zaka ci abincin amma sai ka bude cikinka a farfesun ga ma irin lemon keakwar da kake so ta zuba ta mika masa ya karba ya sha yace lallai fa ashe ni dan gata ne amma ake mun yanga ansa ina rawar jiki gaban yar tsohuwa na lura so kike inyi kiba in aje tumbe idan nayi nauyi ke zaki wahala gaki yar lange lange.gara... Aneesa ta boye fuskarta cikin gyale tace, ni dai don Allah ka daina min wannan maganar ba ruwana. Ya sa hannu yana kokarin hade fuskar ta yace, ki bude min fuskarki in ba haka ba zan daina gaya miki irin wadannan maganganun ba. Dole ta bude fuskar suka ci gaba da hira tana bashi abincin a abki don shagwabe mata yayi ya zama kamar yaron goye. Hira sosai ya donga janta da shi, yayi kwance shame2 a jikinta har 11pm yayi. Hajiya ta kira wayarsa yana ganin kiranta ranshi ya sosu don ya san ma'anar kiran rabashi da matarsa za'ayi wadda yake jin tsananin so da bagenta ga matsananciyar sha'awarta da ke damunsa, don ko a abuja ya kasa sukuni har safeena ta so ta gano shi. Yana kara wayar a kunnensa yaji tace ka sallamomin yarinya zamu kwanta in kai baka san dare yayi ba. Ya marairaice hajiya na dauka anan zata kwana da nan da gurinki ai daya ne, tace kaga bana son dogon turanci na baka 3mins ina jiran Aneesa, cutar da take fama da ita ai bata warke ba, sai ka jira ranar warkewarta dan ta samu yadda kake so sai baka ita, amma ba yanzun ba, yace ni wlh hajiya bance 'yarki na da ciwo ba, don Allah ki daina wannan maganar ayi min afuwa, ki barta a..... Bai gama maganar ba ta kashe wayar. Ya tsaya kawai yana kallon wayar yana kallon Aneesa dake saurarensu, da taga ya kasa magana kuma taji hirarsu da Hajiya nemanta take sai ta sauke kansa da yayi matashi da cinyarta ta mike tace, ni zanje na kwanta sai da safe kenan. Ya zura mata idanunsa da suka sauya launi zuwa ja mai duhu yace, yanzun haka zaki tafi ki barni? Kwarai ta lura ya shiga wani yanayin na tsananin bukatar ta a kusa da shi dolensa ya dauki hkr, hajiyarsa ta murda kambunta ta sha alwashin kwatar mata yancinta da suka wulakantar sai ya gano lallai ita ma tana da DARAJA NA DIYA MACE tace kayi hkr ba laifina bane umarnin hajiya nake bi yace shikenan gara ki bi umaarnin hajiya, amma ki sani idan wani abu yayi ajalina a daren nan kece sila kuma sai Allah ya tambayeki don wlh zan iya rasa raina ayadda nake jin wani abu na taso min. 106) Ya ja filon kujera ya dafe kansa ya rintse idanu yana fidda zufa nan da nan Aneesa ta rude jikinta ya dau rawa saboda gani take kilama yanzu zai mutu, ita kam ta shiga 3 ta durkusa gabansa ta tallabo kansa ta dora akirjinta ta shafa sumarsa a hanakali, tanaji ya na sauke numfashi tare da ajiyar zuciya ahankali. Ya sauko daga kujera ya dawo kasa inda take yabi ya kwakumeta ya kwanta a cinyoyinta, tana son ta tafi amma ta rasa yadda zata bullo wa wannan rikicin nasa. Yaji alamun tana son tashi ya riketa gam yace Aneesa kina son ki tafi ko? Tayi shiru ya sake cewa na yarda ki tafi amma sai kinyi min abinda zan kwana ina farin ciki, ki dan rage min radadin sha'awarki dake damuna tace, ni dai kunya nake ji don Allah kayi hkr mu bar gidan nan idan muka koma gidanmu komai zan iya yi maka. Tana kallonsa ya tashi ya kashe fitila falon duhu ya gauraye, ya haska wayarsa ya iskota sannan ya kashe fitalar wayar, ya jata zuwa jikinsa, duk wani abu da yasan zai yi mata ya ya sami gamsuwa sai da yayi mata ita ma ta taimaka masa, ta yadda ta gusar masa da sha'awar ta hanyar wasanni, har mamakinta ya dinga yi. Ko da yake tana karance2 dole ta sami wayewa. Sai da taji ya soma bacci sannan ta rada masa a kunne zan tafi nasan hajiya tayi bacci. Ya sumbaci labbanta yace nagode Aneesa Allah yayi miki sakayyar aljanna, kin zama mata tagari. Ta tashi ta saka rigarta da ya cire ta daura dankwalinta ya yafa gyalenta ta fita ta ja masa kofarsa sannan ta isa cikin gidan. Babu motsin komai a falon ta na shiga ta iske Hajiya ta dade da bacci, ta kulle duk kofofin sannan ta shiga bayi tayi wanka. 107) tayi wanka ta fito daure da alwala tazo tayi nafila sannan ta kwanta, duk Hajiya na bacci. Da safe ta dauka Hajiya zata yi mata magana sai ta ga bata ce mata komai ba, har Ishaq da ya shigo ba ta ji tayi masa magana ba, sai ma hira da suka dinga yi. Aneesa wajen karfe goma tayi wanka tana shiryawa sai Hajiya ta shiga dakin ta dubeta tace , "yawwa gara kiyi shiri gaba daya zaki bi mijinki," Aneesa ta juyo da sauri tana duban Hajiya tace " In bishi fa kika ce? Gaskiya ni ba yanzun ba sai na gama shan magunguna na." Tayi murmushi tace wane magani kuma? Ai kin warke kyaje can gidanki ki sha maganin tunda kin nuna alama." Tace "Hajiya wace alama na nuna?" Tace, "Au baki sani ba?" Ina ce jiya gurin mijinki kika kwana, kinga gara ki bishi kada ya zamo ina takura masa tun da na lura Ishaq bai da kunya ko kankani." Aneesa ta soma kuka , "Hjiya wallahi ni ba a wurin sa na kwana ba, lokacin dana shigo na iske kinyi bacci sai ban tashe ki ba. amma wallahi a nan na kwana.." Tace ." To ni dai gara ki bishi, yanzun ne dai da na ke son in kwatar in nuna masa kema mai daraja ce naga abin ba zai yiwu ba. gara ku koma gidan ku tun kafin ban sani ba ya dauke ki ya tafi dake.” Kuka sosai Aneesa ta dinga yi tana ba Hajiya hakuri, “ Don Allah hajiya kiyi hakuri ki yafe mani, ni ba zan bishi ba kuma b azan sa ke zuwa sassanshi ba koya kira ni, jiya da naki zuwa don kince inje ne na je, amma b azan sa ke zuwa ba.” Hajiya tace, “ni ban hana ki zuwa gurin mijin ki ba,amma yadda da sanin sa matarsa ta tozarki ta tozarki shine nake son ki nuna masa kin san martabar kankki in ba haka ba zasuci gaba da taka ki yadda suke so, in kin yarda ni dinnan sai ya zubda hawaye ya nuna kina da daraja sannan zan bashi ke ku tafi.” Cikin kuka Aneesa tace “ Wallahi zan bi umarninki ko kula sshi ma sai kin ce inyi zanyi.” Tun daga lokacin ishaq da ya shigo ya rasa gane kan Aneesa, yayi tambayar duniya ta gaya masa me ke damunta 108) ya ganta sukuku ba walwala sai tace masa ba komai. Gurin hajiya ma ya danga sauyin fuska, duk sai ya damu gashi ya so su tafi yau amma sai ya ga ba fuskar da zai tambayi Hajiya,itama gimbiyar bai gane kanta ba, doe ya fasa tafiyar zuwa washegari. Da dare ko abincin da tayi masa aika masa dashi tayi, day a kira ta a waya sai tace ya tambayi Hajiya, ya dauka abin na sauki ne sai ya ji Hajiyan tace, “ Kaga Ishaq ka rabu da ni, Aneesa dai ka kawo mini ita bata da lafiya to karka dame ni a kanta sai ta warke zaka ga nace ka zo ka dauki matarka ko kana Abj ne, gara ma in zaka shirya ka koma bakin aikinka gobe ka koma, amma Aneesa ba yanzu ba. “ Gaskiyar Hajiyace da tace sai yayi kuka don kuwa a wannan dare kurmussu ya dinga yi na rashn Aneesa kusa da sh, ya zubda hawaye ta re da kewarta na irin faranta masa raid a ta yi a daren jiya, yauma yana da burin hakan amma an gindaya musu shamaki. Da safe yayi shirinsa tsaf na barin birnin Zazzau, ya sami Hajiya a daki ya zauna gefenta suka gaisa sannan ya danyi shiru zuwa can dai ya gaji da shirun yace, “ Ni zan wuce , kina ganin sati mai zuwa in zo zamu wuce da Aneesa?” Tace, “ Bance haka ba, kuma ban daukar maka alkawari ba, ka dai saurari waya ta kawai.” Ya aje mata rafar dubu hamsin ya mike jiki a salube yace, “ Shike nan zan tafi, Aneesa fa zamu yi sallama.” Ta kwalawa Aneesa kira da ke can dakin Hajiya suna mata gyara ita da ladidi, Tazo tace dama zaku yi Sallama da mijinki ne zai tafi.” Ta dube shi tace “Allah ya kiyaye hanya a gaida su Suhail,” Wani abu ne ya tokare masa a kahon zucci saboda takaicin wannan halin ko in kula da Aneesa ta tsiri yi masa, in ma gara shi ake yi ai ya garu, in ma kurensa suke nuna masa ai ya kuru ya gane kurensa kuma ya shiga taitayinsa, to ba sai akyale shi aka ba koko hawaye suke son suga ya zubda, tunda ko can Abujan Safeena bat a masa ta dadi zafi take hada masa, gashi nan ma yana tunanin ya zo ya sami sassauci amma abin ya faskara. Yana jin kasar zai bari ko ya sami sassauci tunda kasarsa ta gagara shi tayi masa zafi. 109`) Tana gama gaya masa haka kawai ta juya zata tafi, yayi mata Magana a kasalance, Ga wannan ki rike kafin in dawo, “ Rafar dubu ashirin ce. Tasa hannu biyu ta amsa tare da yin godiya. Ta mikawa Hajiya kudin ta wuce abinta, ya bi bayanta da kallo da wutsiyar ido, hart a bace sannan ya sake yiwa hajiya wata sallamar ya fito ya shiga motarsa. Ya fi minti talatin cikin motar a zaune amma ya kasa tada motar ya afi. Yaron gidan Hajiya
Chapter 43 · 0% Book details