Sashe 41
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kiyi hkr yau zakiji banbanci saboda ranannan itace ranar farkonki kuma nayi miki alkwarin wlh ba zan wahalar dake ba kinji sweety na. Ta girgiza kai tace, ni dai kawai bana so ne ka kyaleni, gara ma kaje gurin matarka na yafe mata. Yayi murmushi,a she kina da kishi haka? Ai bansan kishin ke damunki ba, to kiyi hkr na fi son naki ne kinji, zo nan kiji wata magana. Ya jata jikinsa ya soma rada mata wasu maganganun wadanda suka bata mamaki ko da yake ba abin mamaki bane cikin halayyar namiji mai fuskoki da yawa, duk gaurin wadda yaje da fuska daban yake zuwa mata. Duk yadda yayi lallashinta taki yarda da shi. Ya koma fada nan ma a banza ya juya wa'azi nan ne ma da ya fara fado tsinuwar Allah da mala'ikunsa hankalinta ya tashi ta soma kuka shi kuma kukan ne baya so dole yana ji yana gani ya hkr ya kyaleta ba don hara ransa ya so ba. Ita dolenta a cikin jikinshi ya nadeta tayi baccin dole duk a tsirace take, shima yayi mata alkwarin da bazaiyi mata komai ba. Tun Asuba Aneesa taci gaba da shirinta, da ya tashi ya ganta sai bai kula ta ba ya fice mosque da ya dawo ya wuce dakinsa ya kwanta. Kafin 9am Aneesa har tayi wanka ta gama shirinta shi kawai take jira, da taji shiru saai ta bishi dakinshi taga wayam ashe yafita, tun adakin ta fara kuka, ranar wuni guda cur a dakinta tayi shi har dare yayi, da ya dawo ya shiga iske wani sabon kukan take yace, wai ke har yanzu baki daina kukan nan ba? Ba zaki yi hkr da zuwa zarian nan ba sai karshen wata muje? Tace ni dai in bazaka kaini ba sai in je in shiga motar haya. Ya zaro mata ido yace, ke kina hauka ne zakije ki shiga motar haya? To kiyayeni kada ki kuskura ki gwada wannan gangancin. Tace to ni dai don Allah ka taimake keni ka kaini. Yace zan kaiki amma sai kin gaya min abinda akayi miki kike son zuwa wurin Hajiya. Tace zan gaua maka amma sai munje zaria ba'a gidan nan ba. Yace kinyi alkawarin idan muka isa ni zaki fara gayawa? Tace eh nayi. 96-Washe gari bai sake ja mata rai ba suka nufi zaria sammako sukayi don a ranar yake son dawowa abuja duk da dai sai da suka sami sabani da safeena,har tana mai korafin wai yarinya karama sai gara shi take yi haka kawai ba'ai mata komai ba ita ga shagwababbiya ta kama kuka wai ita gidan hajiya zataje,ba gidan hajiya ba in taso ya kaita makka ne shi dai bai tsaya kulata ba suka nufi zaria don ya gaji da kukan aneesa soya masa zuciya yake yi.kwatsam hajiya ta gansu,wannan shine zuwan Aneesa na farko tunda taje abuja garashi ya zazzo hajiya ta rungumi aneesa tana murna ko don yadda taga tayi kiba tayi kyau hakan ya nuna mata diyarta kuma surukarta ta sami kwanciyar hankali.ladidi ma murna ta dinga yi sai shiga da fice take yi tana aikin shirya musu abinci da abun sha,sai da suka ci abinci sannan ishaq ya fita masallaci ko da yake shi kadai yaci nasa Aneesa tana zuba nata sai ta shige dakin hajiya tana cin abinci tayi sallah ta kwanta suna hira da hajiya.ladidi tayi sallama ta shigo ta mikawa aneesa wata leda tace" ga sako inji yallabai yace ki dama masa fura ki kai masa zaije ya kwanta"ta dauki ledar taje kicin din hajiya dama masa furar daga (HABIB YOUGHORT)yazo da furar da yogot din dayake dayawa se ta dibar ma hajiya nata da ladidi ta dauki nashi ta wuce sasansa a kwance bisa (3seater) doguwar kujera ta same shi dagashi sai farar singileti da farin gajeran wando tayi sallama ya dago ya dubeta ya amsa sallamar ya tashi ya zauna ya amshi (jug)din hannunta ta zauna gefensa ta zuba masa fura a kofi ,ya amsa ya fara sha sannan yace "ina fatan baki gayama ma hajiya komai ba tace daga zuwa na sai in hau gaya mata wata magana,ni na fasa gaya ma kowa zan bar abin a cikina" yace kinsan Allah idan baki gayamun ba yanzu zan rufe dakin nan inyi miki abinda ba kyaso sai naga ba kya motsi sannan na kyaleki ta zumbura baki cikin shagwaba tace wlh kana taba ni zanyi maka ihu zaka kasheni tunda naji lallasani kake so kayi...yace bari in rufe tun yanzu dan kisan ko waye yazo bazan bude ba in taso na gama abinda nake na wuce Abj na barki da jin kunya..ko da yake ba mai zuwa idan yaji mace na daki ita da mijinta tana ihu...oya fara tun yanzu ta mike ta ruko hannunsa yi hakuri zan gaya maka..ya dawo ya zauna ta dde tana yan tunane tunane sannan ta gaya masa yadda suka yi da safeena a kicin ya dde yana mamaki yace wlh kinji na rantse miki ban taba gayamata komai ba...ni na na taba gaya miki haka? In baka gayamun ba ai ka nuna mun kuma duk yadda ta fada ya faru ai ya za ai bazan yarda ba in ma ta gaya miki kirkiranta ne...ni bana cikin wannan shirmen...ni da kin gaya mun tun agidan da ba muyi wahalar zuwa ba..ke yanzu wannan zancen zaki iya gayawa hajiya bakijin kunya tace kunyar me zanji kaima ka iya gayawa matarka balle ni da abun ya shafa ai dole in gayawa hajiya dan taji danta na wulakanta ni. Dan Allah ki rufa wannan asirin kar ki gayamata dan ni zaki tozarta...tace bi kuma na cigaba da tozarta ba dan yanzu ka gayawa matarka tana mun tozarta balle nan gaba gara kawai na gauwa hajiya tasan abinyi...ya tallabe goshinsa yai shru...shi dai har ga Allah baya son ta gauawa hajiya sai dai kuma kila za asama masu mafita. 98) bai sake ce mata komai ba yaci gaba da shan furarsa har ya gama sannan yace kinga matsalata a ke ko? Dazu ma ina jin baki ci abincin da kika diba ba oya zuba furar ki sha.. Bata son tana musu dashi sai ta zuba furar rabin kofi ta sha da ta gama ta dube shi yana kishingide kamar zaiyi bacci tace yau din zaka koma? Yace inajin zan fasa sai hobe udan kika gayawa hajia sai naji feed back sannan zan tafi idan ma ta bani dama mu wuce tare ta fiyo da idanu waje tace in koma ina kaima kasan ba zai yuwu in bika ba sai nabi yan uwa na gaishe su wata na kusan biyar rambona da gida yace sai in zauna in jiraki kin yarda ko? Tace idan na yarda za a barka ka zauna ne waya kadai ta isheka yace waye zai min wayar tace kafini sani ya kyalkyale da daria yace lallai yarinyar nan kishinki yayi yawa naga ma har kina son kifi safeena tace idan na fita kuma ai sai a shiga min rokon Allah yayi ta dariya a ransa dadi yake ji ashe aneesa na sonsa har haka. Da yamma ta shiga gidansu ta gaishe su can tayi dare sai da taga Abbanta ta kawo dububgoma ta bashi tace yayi cefane cikin kudaden da ishaq yake bata wani lokacin shima da ya shigo zasu tafi sai da ya ba Abban 20k yayi ta sa musu albrk haka yabi sauran iyayen ta maza da matan gidan ya raba musu kudi sannan.sukai musu sai da safe suka tafi. Da dare tana kwance bisa kafet din tsakiar dakin hajia ita kuma hajian na gegenta suna ta hirar vayan saduwa can sai hajian ta tmbyeta Aneesa anya ba wani abu da ya faru kuka yo wannan tafiar baki ko yimun wayar zaku zo ba alhalin wancan zuwan da yayi cemun yai sai karshen wata zai kawoki har nace to ya baki isassun kudi ko ya miki siyayyar a zaki rabawa en uwanki sai.kuma naga kunzo.ko tsaraba babu kuma tjn zuwanki na lura akwai abinda ke damun zuciarki kina da magana aba kinki kin kasa fada ne in kin san akwai abubuwan.dake damunki ki gayamun inyi maganin abun tun kafin ya dauke ki ku koma dan yayarku da taje ta fara gayamun wasu abubuwa naso nazo da kaina sai dai na bari sai kinzo inji daga bakinki dan kuwa nasan ana can ana zaluntarku ba wata amanarki zai rike yada ya kamata ba tunda matarsa tafi karfinsa sai yadda tayi dashi dukanku hadaku zatayi tai ta muku milki son ranta dan na san halinta farin sani ...in zamanki zai yiwu ki koma can in ba zai yiwu ba gara ya barki anan kiyi zamanki. 99) hankalina zaifi kwancia dan tunda na baroki hankalina kacokan yana kanki hawayen da ya taru a idon Aneesa a take kokarin boyewa su suka zubo nan da nan hankalin hajia ya tashi tace aini nasan ba banza ba ta kai zomo kasuwa da magana a wannan zuwan naku na bazata...kinga bana son kukan nan gaya min meke faruwa don baki da uwar da ta wuce ni a yanzu gaya mun ta daga kafadar aneesan tana lallashinta ita kuma ta share hawayan fuskarta tace ki bari hajiya sai gobe kiyiwa yaya hannatu waya tazo ita zan gayawa sai ta gaya miki ni ba zan iya faa miki ba maganar da nauyi hajia tace ai bazan iya bari sai gobe ba bazan iya bacci ba tunda dare baiyi ba bari in kira ta waya in roki mijinta yasa a kawota yanzu..nan da nan hajia ta kira hannatu a waya ta gaya mata bukatarta sai ta shaida mata maigidan yana Abj amma bari ta kirashi ta gaya masa tana nan zuwa yanzu.. Ba afi rabin awa ba sai ga hannatu direbansu ya kawota bayan sun gaisa da hajiya sai hajian tace ga kanwarki nan ki bincikar min matsalolinta tace ke xata iya gayawa ni daam nasan yaron nan shi da matarsa sai sunci min amanar yarinyar nan shi yasa kullum cikin tunaninta nake hankalina yaki kwanciya. Hajiya ta fice ta bar musu dakin hannatu ta zauna cikin hikima irin ta manya ta nutsar da aneesa ta gaya mata matsalolinta har da cin mutuncin ta da safeena tayi mata a kjcin..Hannatu ta fita ta sami Hajia tai mata