Sashe 13
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga ta haihu da kanta. Amma idan haka bai yiwu ba dole aiki za'ayi mata, ki kira min babanku a wayar maman. Zan gaya masa halin da take ciki ne. Jikin Aneesa nan da nan ya shiga rawa, saboda jin irin halin da Mamanta tashiga. Ta kira lamabra Abban na su sai da ta kusa tsinkewa sannan taji ya dauka, sai ta mikawa Aunty nurse itace tayi masa bayanin komai, kuma tace ya kamata ya zo, ya kasance a gurin ko da za'a bukaci sa hannunsa idan ya kama ayi mata aiki. Yace yana nan zuwa idan ya gama da banki. Ciwo yayi wa Maman tsanani tace a kira mata Aneesa babu yadda za suyi, sai suka lullubeta sannan suka kira Aneesan, tana shigwa taga halin da Maman ke ciki sai ta soma kuka ta rike hannuwan Maman tamau. Mama tayi magana kyar, karama har yanzu Abbanku bai zo ba ko? Tace, na kira shi sun yi magana da Aunty nurse yace yana bank ne, amma zaizo, to yanzun na sake kira wai wayar akashe ta ke. Maman tayi murmushin nan nata wanda yawanci idan abu ya bata haushi a madadin ta nuna jin haushi, sai dai kaga tayi murmushi kawai, tace. Na so ya zo mu gana amma kila Allah ba zai ba shi iko ba, ni na san da wuya zan haifa abinda ke cikin nan nawa, kila Ajali na ne na kumsa, ko da bamu gana da Abbanku ba da sauran jama'ar gida duk ki gaya musu na yafe musu ni su yafeni. Allah ya sa na roki abbanku gafara yace ya gafarta mini, ki rokar min su Umma gafara, sannan ki cigaba da hkr da kannenki. Ku hada kanku.....(Crying) Allah yayi muku albarka ya kare ku a duk inda zaku kasance. Hawaye ya gangaro ta gefen idanun Maman, Aneesa kuka sosai takeyi, ta sa hannu ta goge wa maman hawayenta tace, Insha Allahu kina tare da mu mama, ba zaki mutu ki barmu ba, idan kika mutu waye gatanmu, waye zai kula da mu kamar ke, ba zaki mutu ba mama. Ta sake kankame hannun Maman tana kuka. Maman tace, kuyi hkr Allah shine gatanku, zai share muku hawaye fiye dani, rashi na ba zai nakasa rayuwarku ba, Allah zai kasance tare da ku.... 61) Aunty Nurse ta budo kofar dakin ta dubi Aneesa tace, haba aneesa ya zaki shigo ki kara tayar mata da hankali kina koke2 muna kokarin ganin jininta ya daidaita, amma zaki sa ya kara hawa. Aneesa tace maganar mutuwa take mini shi yasa nake kuka. Aunty Nurse ko mutuwar zatayi, tace sanin gaibu ai sai Allah. Ki kwantar da hankalinki Insha Allah ba zata mutu ba zata haihu lfy. Yanzu ki koma can gida ku taho da wani babba tunda mun sake kiran wayar babanku akashe take, gara wani cikin yar uwanku ya zo kusa, ba ke ya kamata kina tare da ita ba. Gidan kanwar maman shine mafi kusa da asibitin, don mai mashin Naira ashirin zuwa talatin zai kaita, shi yasa tayi shawara zuwa ta kirata tunda neman na gaggawa ne. Tana yin sallama a tsakar gida ta ganta tana yanka alayyahu, sallamar Aneesa kawai ta amsa tace, hala yaya Fatima ta haihu ne? Don wlh cikin satin nan kusan kullum sai nayi mafarki da ita, yau da na tashi nake gayawa Babansu, khalifa yace idan na gama abin da nake inje in ganta ko hankalina ya kwanta, yanzun haka azhar nayi da zan tafi. Aneesa tayi murmushin yake tace, bata haihu ba, amma tana asibiti ne zata haihu, shine akace in in gaya miki mu tafi, kila ma aiki za'ayi mata. Salati ta saka, hakan ne. Ya fito da uwar gidanta tace, Maman Nana me ya faru naji kina salati. Ta gaya mata abinda ya faru, ita ma ta jajanta sannan tace, yi ki shirya ki tafi barin in karasa girkin, miko min wayata gata nan da na tashi na barta, in kira baban halifa inshaida masa. Kuyi ku tafi ko me kenan ki kirani a waya nima da na kammala girkin zan biyo ku asibitin. Suna isa asibitin Aneesa ta nufi dakin da Maman take sai taji kofar a kulle, kuma ba ta jiyo salatin da tafi ta bar maman nayi ba, a zuciyarta sai tayi tunanin ko har sun tafi da ita dakin yin aikine. Ta kwankwasa ofis din Aunty Nurse ta shiga ta zauna ta ganta ta tallabi kuncinta da hannu biy2 da ganinta tana cikin damuwa sosai. 62) Tana ganin Aneesa ta sauke hannuwanta daga tagumi tace, Aneesa kin dawo? Da wa kuka zo? Tace da kanwar mama ne. Abbanmu ya zo kuwa? Tace bai zo ba ina ta trying no amma har yanzu a kashe take. Muje inga ita kanwar Maman. Tace naji dakin da maman take a rufe, an tafi da ita dakin tiyatar ne? Tace eh an tafi da ita, muje takunnan inga ita kanwarta din. Kiran maman nana tayi office dinta, ban san me ta gaya mata ba, naga ta fito a rude tana kuka nayi saurin biyo bayanta nace, maman Nana me ya faru? Mama ta rasu ko? Ta ruko hannuna tace, Aneesa sai dai muyi hkr sunyi iya kokarinsu Allah bai ba su sa'a ba, don ba'a kai ga shiga da ita dakin tiyatar ba Allah yayi mata rasuwa, tunda sun jira Abbanku bai iso ba, yanzu kawai tafiya da ita zamuyi a motar aunty nurse. Aneesa jin numfashinta ta tayi yana neman daukewa, nan da nan jiri ya kwasheta ta tafi yuwww! Zata fadi maman Nana tayi yi saurin tallabota ta zaunar da ita bisa benci. Aneesa ta soma kuka tana surutai wadanda za su kaita ga sabon Allah. Maman Nana ta shiga yi mata fada, haba Aneesa kowa ma mutuwar nan ita yake jira ko kinfi Allah sonta ne da ya bamu aronta yau ya amshi abarsa. Ta zubo da hawaye tace, maman nana kin fi kowa sanin halin da muke ciki, mama na raye ma mun shiga halin garari balle ta kasa ta rufe idanunta. Tace mutum baya da wani gata sai Allah, shine gatanku babu mahalukin da zai zulunce ku sai Allah yayi maganinsa, ita dai tata ta kare. A bayan motar Aunty nurse aka saka gawar Mama tare da Maman nana da wata nurse, Aneesa da Aunty nurse suka zauna agaba. Sun baro asibitin da dan nisa ne Aneesa ta hango motar Abbansu ya taho asibitin, sai taji haushinsa ya kamata gani take ma rashin zuwansa akan lokaci shine yayi sanadin mutuwar mamansu, don da ya zo a tym da ake neme shi ya sa hannu, dan anyi mata aiki, amma don kada a dameshi da kira ma sai ya kashe wayarsa, ya kyaleta cikin azabar ciwo har tayi ajalinta..... IJIN ARO 1**10 63). Maman Nana tace, Aneesa waccan ba motar kamar ta abbanaku? Ta dan dubi motar da jajayen idanunta tace, ba ita ba ce. Maman nana ta gano haushin Abban nasu takeji shiya sa tace haka, sai tace ki kira wayarsa idan shine kice mun dawo gida ya dawo can ya same mu, kada ki gaya masa abinda, tayi murmushi irin na mamansu, murmushin bakin ciki tace, idan yaji abinda ya faru zai damu ne? Wannan mutuwar fa mu ta shafa. Maman nana tace ya isa irin wannan shirmen naki, kina nufin kin fishi sonta ne? Aneesa tayi en danne danenta na karya tace wayar sa ta ki shiga, tana kallonsa ya mike hanyar asibitin. A kofar gida suka iske baban sasa, maman nana ce ta karasa suka gaisa tayi masa bayanin abinda ya faru, iya rudewa ya rude ya kama salati da surinsa ya shiga cikin gidan ya sanar musu, nan da nan mutuwar tayi tambari a unguwar, dama Aneesa tayi waya tudun wada ta gaya wa su Umma, su Aneesa na isowa en uwan maman suka iso a motoci maza da mata. Abbansu Aneesa ma sai gashi ya dawo jikinsa a mace saboda jin mutuwar nagartacciyar matarsa. Aneesa bata taba tunanin abbansu zaiyi kuka don mama ta rasu ba, amma sai ta ganshi yana kukan hawaye wasu na korar wasu. Ba a bata tym ba aka shirya maman aka sallaceta aka kaita gidanta na gaskiyya. Aneesa tana can dakin maman kwance cikin bargo saboda zazzabi ne ya rufeta. Ta nemo layin Hajiya ta gaya mata, kuka taji Hajiyan nayi hadi da salati, daga nan ta kira Ishaq shima ta gaya masa, shima ji tayi ya saka salati yace, what Aneesa! Mama ta rasu? Kada ki gaya min shirme, ko dai babyn da ta haifa ta rasu? Ta sauke ajiya zuciya irin na wanda ya sha kuka, tace wlh mama ce ta rasu har an tafi kaita ba'a dawo ba. Ta wayar taji faduwar tasa wayar, hakan ne ya nuna mata shiga halin rudani. 64) Ta koma ta kwanta hawaye na ci gaba da bin kuncinta, tabbas ba ita kadai tayi rashin Mama ba, Ishaw ma yayi babban rashi saboda yadda yake ji da mama, tamkar hajiyarsa, wajen shawarwarinsa kuma tamkar yayar sa ta jini yake daukar shawararta saboda yace duk shawarar da ta ba shi idan ya bi ko da zuciyarsa ba so, daga baya yana ganin anfanin abin. Ita kanta Hajiyarsa cewa take shi da mama ba'a sanin cikinsu, kuma hakan ne. Don ko matsala ce da shi direct yake xuwa ya gayawa mama ya nemi shawararta haka za su kasa su rufe Hajiya bata sani ba, har sai anyi maganin matsalat, wani tym din ba idan ba dalili ba Hajiyar ba ta ma sani, don ko lokacin aurensa da safeena da aka sami matsala, da shawarwarin mama yayi ta anfani har Allah ya ba shi sa'ar auren safeena sai ga shi ashe da rabon 'ya'ya har an fara da biyu2, ba'a ma san me gaba zata haifar ba, shi yasa lamarin aure ba'a son mutum ya ja tunga da yawa, ko ayi ranka babu dadi. Da Hajiya da Ishaq kusan a tym daya suka iso Zaria, shi jirgi ya biyo zuwa kaduna, daga kd direban abokinsa ya dauko shi daga airpoart zuwa zaria, ita kuma safeena gobe driver zai taho da ita da yaran. Hajiya kuka ta dinga yi da hawayenta saboda rashin Mama da sukayi, haka ta dinga fadan kyawawan halayyanta wanda kowa ya sani, wasu