← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 51

Sashe 40

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

makara, ba zaki taba kamoni ba, koda a kullum zuma za'a jikaki ki kwana, tunda ba halitattarki bace kamas zai jiki, sai dai kiyi hkr, don naga yau sai rawar kai da rawar miji kike tayi ga wadda ta tsuma, wannan ai ya tozartaki ne ya wulakantaki, tunda har sai ya nemi shawarar yadda za'a taimaka mki ki zama mace sosai. Ina fatan yanzun kin gano banbancin da nake agurin mijinmu, saboda haka kada ki kara min wannan rawar kan, indai rawar jikine ai kina kallon yadda yake min ranar girkina to ba komai yake wa sai wannan ni'imataccen gurin da Allah ya mallaka masa, ke ko babu yadda za'yi mutum ya so abu mara dadi ai kin gane. Tana gama yiwa aneesa wannan tozarcin da wulakancin sai ta fice abinta cikin takama ta bar kicin din ita kan aneesa dama kukan hawaye takeyi, tana fita ta sake rushewa da kuka saboda babu wulakanci da ya wuce wannan tozarcin da wulakncin da akayi mata yanzun ace miji ya fallasa sirrin kwanciyar ku girin kishi har ya gaya mata yadda kake, kwarai duk ya nuna mata ashe shi abinda yaji ne bai gamsar da shi ba, shine tun daga ranar bai sake nemanta ba, wata so shine ya bata hadib zuma ta sha, lallai ta yarda hakan take ita kam ta hkr da zaman gidanshi wannan wulakancin yayi yawa gara ya maida ita gida zaria inda take da gata da masu lallashnta nan kuwa sai dai su taru shi da matarsa su wulakanta ta, sai dai ta shige daki tayi ta kukanta har ta hkr don idan zata kwana tana kuka babu wanda zaisan tanayi ballatana ya lallasheta. HAUSA Novels BOOK MIJIN ARO 2***10 Girkin da ta kasa karasawa kenan ta kashe gas din ta sauke miyar kayan lambu da tayi taji naman kajinta, sauke ruwan da zata dafa cous2 ta koma daki taci gaba da aikin kuka. Ita kuma safeena sarkin kisisina ta caba ado tana zaune a falo har ogan ya dawo gab da magriba, dakinsa ya wuce ya canza suit din jikinsa zuwa jallaabiya ya yo alwala yazo ya wuce mosque, da ya dawo ya wuce kai tsaye table ya iske babu komai ya zo inda safeena ke zaune, yace ba'ayi girki bane naga table wayam. Tace batayi ba tana daki aabinda amarci take ji ga yara tun dazun suke kukan yunwa sai tea na hada musu, Yasmin ma taki sha kasan bata damu da tea ba sai abinci. Nan da nan ya hasala jin cewa yara har suna kuka yunwa wannan ai wulakanci ne yarinyar nan zatayi masa tunda tasan yau ita ke da girki, ya dubi suhail a fusace yace, suhail je ka kira min auntyn ku. Suhail da gudu ya isa dakinta ya isketa bisa abin sallah ta idat amma har yanzun kuka takeyi, ya gaya mata sakon dadinsu kai kawai taa gyada masa, ya juya yaje ya gayawa Ishaq gata nan zuwa amma yaga tana sallah kuma tana kuka, safeena tayi karaf tace, idan bata da lfy ba sai ta fada baa ai da nayi girkin amma sai ta zauna a daki tana kuka mu ta barmu da yunwa. Ishaq yace ita ga shagwabbiya komai kuka, ba zata iya yin magana ba, ni ba zan dauki wannan ba. Ya zauna yana huci har fiye da 20mins Aneesa ba ta zo ba, ya tashi a hasale ya nufi dakinta har yanzun tana bisa sallaya tana ta addua tare da zubda hawaye, ya tsaya a kanta yace, aneesa me kike nufi ne na aiko a kiraki kinki zuwa, sannan me ye dalilin kin san kece da girki yau kika bar min yara da yunwa kika yin girkin? Shiru tayi tana shatato hawaye, ya ja tsaki, ni ban tambayeki kuka ba, ke tundaga shagwababbiya ce kinyi laifi ba dama ayi miki magana sai ki kamawa mutane kuka, to maza ki taso kiyi wa yara simple girki suce don ba zasu kwana da yaunwa ba, in kuka ba haka ba ranki zai baci agidannan. Ya juya a fusace ya fuce, yana fita ta mike saboda bata son Allah yayi fushi da ita, ta nufi kicin en mins kalilan ta dafa cous2 ta zo ta shirya musu atable, tana gamawa tazo ta wuce yace ina zaki? Dawo nan kici abinci. Cikin muryar kuka tace na koshi, me kika ci? Tayi shiru siafeena tace, kuka taci ta koshi ko? In ma ciwo kike ai ba kuka zaki shiga daki kinaan abyi ba, in kuma wani abu ne ke damunki ya saki kuka zaman aure ai dan hkr ne. Inbanda ke amarya ai er lele ce bata kuka, ko fada kayi mata da kashiga dakin? Yace fadan me zanyi mata ni dai na dai gaya mata ne bata kyauta ba da taki girki, ta bar yara da yunwa. Ta dubi aneesa da ke tsaye tana sharar kwalla tace, yi shiru ki daina kuka, 'ya'ya ai kema naki ne, wa ya sani ko kema kina makale da naki cikin, kila ma laulayi ne ke damunta take kuka daki, don Allah ka daina mata fada. Lallai wannan matar kisisinarta tayi yawa, sarai ta san itace ta haddasa mata kuka bakincin amma don kinibibi sai tayi tamkar batasan abinda ke faruwa da ita ba. Wucewa dakin tayi ta barsu suna cigaba da zancen. Haka tayi wanka ta kwanta bata ci ba komai ba sai aikin kuka, adaren duk ta hada kayanta na tafiya zariya jira kawai takeyi gari ya waye ya kaita ko yasa akaita in ba haka ba tabi motar haya tatafi abinta. Can wajen 11pm Ishaq ya gama duk abubuwan da zaiyi har ya kwanta baiga Aneesa ba tazo dakinsa, yayi ta juyi shi kadai a gado rashinta akusa da shi ya dame shi, ko ba zaiyi komai da ita ba bashi dai burinsa kullun yaji ta manne ajikinsa, Allah yasa yaribyar ta iya wasanni da take koya mata, gata ma'abociyar sassanyar kamshi, sam jikinta da bakinta ba ya raboda kamshi, shi yasa baya gajiya da tsotson bakinta, matsalar dai daya ce, in banda wannan matsalar ta koina Aneesa ta gama kanainaaye zuciyarsa, yau kam yana fatan yasamu sauyi da ita don ya maga alamun za'a samu sauyi tunda tayi masa waya ta gaya masa abinda ke fita mata shi yasa yabi ya ko ta zo gare shi, amma gashi taki zuwa ko da yake yayi mata laifi kila sai yayi lallashin kafiny ya shawo kanta. Ya dauki wayar sa yayi ta kiranta tana kallon wayar ta ki dagawa sai mata dauki wayar ta tura kasan filo don kada kiran kada kiran ya dami kunneta da yaga taki dauka sai sauko daga gadonsa ya zura silifas dinsa masu taushi na bacci ya nufi dakinta. Kofar falonta abude amma na dakin baccinta a rufe gam, ya soma bugawa hankali yana kiran sunanta, ta dada shigewa cikin bargo tayi tankat bataji shi ba, yayi isa bugunsa taki budewa, ya koma dakinsa ya dauko bounch of key na gidan ya zo ya gwada har ya sami wanda ya bude koofar ya maida kofar ya kulle bayan ya shiga, ya isa inda take cikin bargo sai yajiyo shesshekar kukanta ya shige cikin bargon ya janyo ta jikinsa sosai yace, wai Aneesa har yanzun kukan ne? To kiyi hkr idan nine na bata miki rai, ko kuma anyi miki wani abu ne? Tayi shiru ya sake shigar da ita jikinsa sosai yace, to me ysa kika ki zuwa dakina? Kuma nakira kika daga wayata? Tayi shiru sai ajiyar hrt take ya lalubi bakinta da kamshinsa ke rikitashi ya manne da nasa ya soma sunbatarta cikin shaukin da wani irin matsanancin kidima tayi saurin datse hakoranta tana kokarin kwace jikinta cikin nasa ta kasa motsi sai dai mutsu2 yasa hannu ka kwance yar igiyar gaban rigarta ya tura kansa cikin kirjinta tana jin abinda ya soma yi mata da rawar jikinsa sai tasa masa kuka, yayi saurin saurarawa daga abinda yakeyi yace, Aneesa dan Allah kiyi min magana meke damunki kike kukan nan, inaji dai kinyi burin bakanta min rai ne a daran nan, don kinga na kwadaitu da ke ko? Nan ma shiru tayi shima shirun yayi da kyar ta gaya masa, ni gobe gidan Hajiya nake son ka mayar dani, naga ji da zaman nan, yace kin gaji da zaman nan? Me akayi miki ki gaya min insha Allahu zanyi maganin abin. A zuciyarta tace ji kamar gaske zaiyi min maganin matsalata alhalin duk shine silar komai, shine ya tona min asiri har akayi min gori da wulakanxi, ba sai na gaya masa ba ya riga ya san komai, tace ni dai kai maida ni gidan Hajiya gara in zauna a can, idan ma ka ga zaka sami zuwa ba kasa driver ya kaini. Yace yanzun ba zaki gaya min abin da akayi miki nayi alkawarin ba zan gayawa kowa ba. Ba kai ba ha hajiyan balle in hada ku, ni dai ka kaini inga iyayena da en uwana zanfi samun saukin kuncin da ke zuciyata. Yace shikenan gobe insha Allahu zan kaiki kiyi hkr ki daina kukan shine bana so, ta tashi ta shiga bayi ta wanke fuskarta ta dawo ta zauna a bakin gado, yana daga kwance ya miko mata hannunwansa yace come on zo ki kwanta, gobe sammako za muyi tunda kin tada min hankali. Tace ni bana jin bacci, yace au haka zamuyi da ke? To shikenan idan baki zo kin kwan ba babu inda zan kaiki. Tayi saurin taje nesa da shi ta kwanta, yayi mata nuni da kirjinsa yace ga matashinki nan zo ki hau ki kwanta. Ta rarrafo ahankali ta dora kanta bisa kirjinsa ta kwanta tana sauke numfashi kadan2. Ya kyaleta sai da yaji ta nustu sannan ya soma shafata ahankali, tana jinsa ta noke, tafi2 taji ya soma rabata da kayan jikinta, tun da ta gano me yake shirin yi mata sai ta soma masa kuka abinda baya so,ita kam tasha alwashin ba zata kara mallaka masa kanta ba. Tunda ya tozarta ta agurin matarsa, gara ya koma can din tafi ta komai, sai dai ba zata iya gaya masa haka ba, tana jin nauyinsa da ta gaya masa, ranshi ya baci da abinda take masa yace Aneesa ko gani keke zanyi miki irin na ranar nan?
Chapter 40 · 0% Book details