← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 51

Sashe 11

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

biredi suci da miya, anan ma ta kai masa tsgeumi yayi ta fada wai munafinci ne... Mama sai dai ta shige kuryar daki tayi ta kuka don bata da wanda zata haywa, yayai mata maganin abin sai Allah shi yasa ta kai masa kukanta. Yawanci idan lamarin gidan ya ishi Aneesa, in dai mama bata da girki ranar sai ta gudu gidan Hajiya abinta tayi kwanciyarta ta huta, saboda gidan bata isa ta kwanta ta huta ba, abbansu na ganinta akwance zaice mazata tashi taje ta ya auntyn su aiki, to akan taya aikin watarana sai ta kai kararta tace tayi mata kaza ba daidai ba. Tana kwance bisa kujerar hajiya idanuwanta na bisa Tv da remote a hannunta tana latse latse daga karshe ta kamo tashar saudi qur'an, tana kallon yadda yara kanana ke kwararo karatun qur'ani cikin murya mai dadi ga tajweed sun fiddawa. Tana tallabe da goshinta tana sauraron amma idanunta a rufe, har hajiya ta fito daga dakin baccinta, tazo gefen Aneesan ta zauna tana cewa, jikine ko garin ne yau naji ki ba surutu ne balle dan girkin da ake mini, me ya faru? HAUSA Novels BOOK MIJIN ARO 1**9 50) Aneesa ta girgiza kai tace, ba komai ba dai naji dadi ne, tace me ke miki ciwo? Ni babu abinda ke min ciwo, haka nan dai naji jikina da garin ba sayi min dadi, Hajiya ta gyara zamanta tace, ruwa baya tsami banza amma ni nasan ba ya wuce matsalar gidanku wadda a kullum nuna miki nake yi hkr da addua zai iya yiwa mutum maganin duk wata matsala da ta sha karfinsa, bana so ki dinga sa damuwa da tunani a ranki sai ki ga kinga kankanuwarki ace jininki ya hau. Ko ita maman ku ba ki ga hkr take yi ba, duk da dai dama ita mai hkr ce, shi hkrn ai baya baci, kuma yana da ranarsa, ku cigaba da hkr wata rana sai labari Aneesa ta sauke ajiyar zuciya tace, shin wai hajiya idan akayi aure saurayi da budurwa, suna son juna dama kiyayya na biyo baya ne idan suka hayyafa? Hajiya tace, sam kiyayya bata biyi bayan zaman masoya, in dai sun gina soyayyatsu ne da tubali mai nagta, kuma suna son juna tsakani da Allah. Amma ko da tsakani da Allah ne suke son junan indai an samu wasu na shiga tsakani, in dai daya cikin masoyan ya bada kofar da za akawo cikas din abokin zamansa to tabbas zaki ga mummunar baraka, ta gifta tskaninsu ko da dayan shi bai bada kofa ta wajensa ba, sanna abu na 2 shine babbancin ra'ayi, in dai har za su dinga samun babbancin raayi na son zuciya bawai dalilin daya ya sabi Allah bane, to nan ma zasu dinga samun sabani wadda ba abinda zai biyo bayan sabanin sai kiyayya. Aneesa ta sake, Jefo mata wata tambayar, to Hajiya idan aka yiwa mutum kishiya dama dole sai daya ya cuci daya, shima mijin dole ya dinga babbanci yana wulakanta daya, ita wadda yake so sam ba zaiga nata laifin ba ko da tayi? Hajiya tace duk inda kika ga abokin zama 2 ko fiye sun hadu a inuwar mutum daya idan kika ga sun hada kai to daga namiji ne, idan ya kasance adali, in kuma kika ga ba hadin kai to ko dai baya adalci tsakaninsu ko kuma akwai matsala cikin matan. 51) Amma yawancin rashin zaman lfy kishiyoyi abu 2 ne rashin adakci daga wurin mijin ko kuma akwai masu shuga tsakani. Wadan da ba su da burin su ga ana zaman lfy. Akwai wasu kuma basu ma taka kara sun karya ba, zaki ga sun kawo matsalolon, kamar kowa ta dinga ganin auro ki akayi nima auro ni akayi. Babu ragayya tsakanin juna ko su singa wa juna gani2 da sauran su dai. Shi yasa duk rintsi ya kasance kai ka zauna da dan uwanka tsakani da Allah zuciya daya. To sai ki ga komai ya zo maka da sauki. Aneesa ta jinjina kai tace wadannan matsalokin kusan sune a gidanmu. Shi ya sa ni insha Allah ba zan auri saurayin da muke son juna ba, gara a aura mini wanda iyaye suka kawo sukace shi suke so, sannan bana son kishiya don ni dai gidan mu naga isharar zama da kishiyoyi matsala ce babba, wanda in bakayi sa'a ba ciwon xuciya sai ya kamaka ya kasheka abanza. Ni dai wlh ina tson kishiya, kada Allah ya hada ni da ita. Hajiya tayi dariya tace ki kwantar da hankalinki kishiya ba komai bace face alheri, duk sharrinta indai zuciyarki da tsarki sai kin gagareta, ke dai kiyi fatan ko da Allah zai hada ki da ita, to ya hada ki da tagari. Aneesa taxe ni dai nasan Maman kullum burinta alheri ne tunda Basira ta zo gidan nan bata taba fadar aibunta ba, ko mu muma bata barin mu fada. Ko da zatayi mana badaidai ba, mama ta dinga yi mana wa'azi da nasiha kenan akan hkr. Ta ya akayi basira ke cin Galaba akanta gurin Abbanmu, duk makircin da ta gaya masa yake dauka har ya dinga yiwa Maman cin mutunci ko da yaushe tace, idan kinga haka ta faru to jarabawa ce Allah keyi bawansa ya gani zai iya yin hkr, idan yayi hkrn sai ya ga sakyayyar alheri a tym din bai zata ba, idan kuma bawa ya kasa hkr to sai ya ciga ba da ganin ba badaidai ba arayuwarsa, ita mamanku hkrn da takeyi insha Allahi zai yi mata rana, ko mu dade ko mujima. 52) Aneesa sun gama xams din 2nd term kenan, Ishaq yayi waya safeena ta haihu twins again. A ranaar aneesa tayi tsallen murna ita da hajiya aka rasa gane wa ya fi wani farin ciki. Ta dubi Hajiya tace, amma dai don Allah zakije abujan kiga 'ya biyun ko? Hajiya tace, me zanje nayi? Duk jama'ar da za suje basu isa ba sai na je? Tace Haba hajiya shima fa yaya Ishaq yana son yaga kinje gidansa, shi ba wani dan fari ba amma kin dau kunyar Maman su sadiya kin dora masa shima matarsa ai saita ga kamar ba kya sonsa ne? Tace indai sai naje gidansa ne zata ce ina sonsa tace, to kada tace, tunda ita tana sonsa ai shikkenan. Ana gobe suna jama'ar zaria ta isa abuja ciki har da Hajiya, wadda da kyar da sudin goshi taje, don kuwa saida Ishaq ya zo zaria yayi lallashi sannan taje, a cewarta bata ga dalilin zauwan nata ba, yara dai idan akayi arbain ai za su zo ta gansu. Yaran kuwa kyawaawa tamkar su Sultan ga shi suma sai ka sha wuya zaka iya banbance tsakaninsu. Su ma canza suna akayi. Hassana Yasmin, Hussaina kuma Yusra. Taron sunan ya kayatar, safeena ta kece raini cikin tsaddadun kaya ita da yaranta, ji take tamkar ta fi kowace mace sa'ar miji, koko ita kadai Ishaq ya mallaka a duniya, domin kuwa ya kashe mata kudi ita da gidanta kamar ba gobe, dama burinta kenan, kawayenta na jami'a su zo ga yadda take bushasha agidanta. Duk wanda ya zo taron nan sai da ya tafi da katuwar jaka shake da abin arziki mai dauke da hoton twins da nasu Suhail a kasa. 53) Aneeesa tana ajin kusa da na karshe ne a halin yanzun, ta zama cikakkiyar budurwa farace ita tas, irin farin nan mai haske, tana da tsayi amma bata da jiki, sai dai fasalinta mai kyau ne saboda kirar kalangu da Allah yayi mata ga yalwar gashi, kirjinta cikakke ne ta yadda zai dauki hankalin duk mutumin da zai tsura mata idanu. Shi ya sa ko da agida take ta faya sanya gyale, idan zata fita kuwa babban hjibi take sakawa. Agidan Hajiya kuwa tunda gidan na jama'a ne ko da yaushe bata rabo da Hajibinta. In dai za a aiki Aneesa to ta dinga cin kar da gaisuwar samari kenan. Da suka bata kula su. Sai suka kawo kansu gida, da yake Abbanta yayi nata kashedin kada ya ganta ta tsaya da wani namiki. Shi ya sa ko sun aiko bata fita, idan mutum ya gaji da nacin zuwa sai samawa kansa lfya. Mutum daya ne har yanzun suke tare da shi, shine Sagir shima albarkacin yana kamar dan gidan ne. Ba a jamza birki ba. Kuma natsattsa ne shi, yana gayawa Aneesa da zarar ta gama secondary zai aurar da ita ne. To ita abinda ke bata mamaki yace aurar da ita zaiyi, amma ya hanata tsayaea da kowa, to ko shine zai zabo mata mijin. Ko yana nufin Sagir kawai zai bata tunda da shi kadai ya kyaleta suna tsyawa. In dai kuwa haka ne, to ta yarda da zabinsa kasancewar tana son sagir din, komai nasa mai kyau ne, daga siffa har zuri'a mai kyau sannan mai ilimi ne duka biyun, yanzun haka ya tafi bautar kasa Abia state, a yadda ya sha gayawa Aneesa da ya dawo za afara maganar aurensu, tunda yana da tabbacin aiki a hanni da zarar ya dawo. Zasu iya samun matsayar aurensu ta bangaren Yayarsa Hanne saboda tun asali tana dawa da wannan soyayyar tasu, kullum aikinta kenan sukar aneesa a gurin sagir, shi kuma yana nuna mata ko meye halin Aneesa zai iya zama da ita, tunda yana sonta, can gidan su ma haka take sukar lamarin sai ya kasance gaba daya kannen sagir din sun tsani Aneesa saboda irin tarin batancin da takewa mata, iyayensu mata ne kawai su ke son wannan alaka ta Aneesa da Sagir. 54) Basura amaryar Abbansu ta haihu kusan shekarar yarinyar daya kenan. Ita kuma maman su Aneesa tana dauke da tsohon ciki, wanda girman cikin tamkar na en biyu ne, gashi tunda ta sami cikin take fama da lararu har cikin ya tsufa gashi ta kumbura. Har anyi mata gwaje2 sun tabbatar da tana dauke da ciwon hawan jini, wanda ya soma taba lafiyarta. Wannan lamarin ya tashi hankalin jama'a musamman iyayenta da abokan arziki irin su Hajiya. Ishaq kam da yaji a washe garin ya iso Zaria. Ya sami maman ya tsa ta gaba da tambayoyin shin me ke damunta take tunani haka har hawan jini ya kamata, gashi zuciyarta na neman harbuwa da ciwo. Tayi
Chapter 11 · 0% Book details