Sashe 29
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rufe dakin ya zare key din ya cire rigar shaddar jikinsa ya cire wando ya zo ya haye gado. Duk tana ta satar kallonsa tabi ta rufe idanu da tafin hannunta. Ya dubeta yadda ta kankame jiki a tsorace dariya taso ta kufce masa yace, oya ke fa nake jira awa daya zuwa biyu na gama abinda zanyi sai mu tafi, in kuma ya kama mu dada kwanane sai mu kara. Jikinta ya dauki rawa yau ta shiga uku ko kasheta mutumin nan yake so yayi ne, in ba haka ba mai zaiyi mata a awa daya zuwa biyu. Ta rarrafa a hankali jikin gado tace, don Allah ya Ishaq kayi hkr wlh ba zan sake mA karya ba, na yarda idan muka koma gidan Hajiya duk abinda zakyi ba zan hanaka ba, amma a nan yaka ke son inyi, gashi ka ambaci awowi dan Allah kaji tausayina, ni fa yarinya ce, ya sake daure fuska kamar gaske yace, ke yarinya ce! Amma kika iya yiwa mijinki karya. Kawai ki taso ki zo kina dada ja min rai kada ki sa in kara tym. Jikinta na rawa kar2 ta tashi ta haye gadon, yace tashi zaki yi ki tube kayan nan tas, tun yanzu ma ki sani ba'a kwanciya da ni da kaya sai kace an daure goro. Ta tashi hawaye na zuba shar2 ta soma kwance zaninta ta ajiye ta cire rigarta duk yana kallonta fuskarsa a daure, shi yasa ta dada tsorata, sai sharar kwalla takeyi, yace iye yarinyar Hajiya ta sangarta ki da ywa shi yasa a gidanta kike ta gara ni don kinga tana goya miki baya, nan kuwa babu ita inyi yadda naga dama, babu mai kwatarki. Oya cire mini underwears dinan ki zo nan. Ta cire komai tas! Ta isa gefensa ta lafe a hankali ta rufe jikinta da bargo jiki na rawa. Ya laluba ya janyota ya mannata a kirjinsa, shi kanshi sai da wani abu ya tsirga masa, duk da dai baiyi niyya yi mata komai ba, amma sai ya latsata yadda yake so, ita dai hawaye kawai takeyi jira take yayi abinda zaiyi ta huta da luguendn da zuciyarta keyi, ga ajiyar zuciya dake zuwa mata. Gani tayi kawai ya tashi ya shige bayi yayo wanka abinsa, yana fitowa yaga idanunta kyar bisa kofar bayin ya yarfa mata ruwa a fuska yace, sarkin tsoro tashi kiyi wanka muyi brkfast mu bar ganin nan, bana son in bar hajiya da jinyarki ne nafi son inyi jinyarki a gidana sai ki shirya kema 40) Da sauri ta lalubi zaninta ta daura ta tashi ta shiga bayin tayo wanka ta fito ta gyara jikinta, ya miko mata bakar abaya da gyalenta yace tasa, ta amsa tasa, sannan yayi waya akayo musu odar abinda zasuci. Gidan Inna Binta suka fara biyawa, aneesa kunya takeji tana ta wani sim2 da fuska, duk Ishaq na lura da ita abin ma sai ya dinga bashi dariya, sai kace wata marar gaskiya. Sukayi sallama da ita suka bar garin kd suka shigo zaria gaban Aneesa ke ta faduwa, fargaba da kunyar yadda zata iya hada idanu da Hajiya kawai takeyi, ita a ganinta Hajiya zata ce da son ranta ta biyewa Ishaq suka kwana a kd ita a dole ga mai miji. Da suka isa gida yadda ta zata ba haka ta gani ba, dan kuwa ta dauka zata iske ran Hajiya a bace ne da abin da sukayi, amma sai ga sabanin haka, da murna Hajiya da ladidi suka tare su, Hajiya na tambaya ya su Binta da sauran jama'ar kd, ita dai amswa kawai takeyi tana yake hakora saboda ita gani takeyi ta tafka abin kunya. Aneesana bayi Hajiya ta rufe Ishaq da fada, Ishaq mw kake so ka maida ni ne? Cikin mutunci na jada auren nan ba musu da gardama ka amsa ashe dama sakayyar da zakayi min kenan, ka tsalleke can idan wanda kake so take ni ka barni a nan da er da mutane sai tyn da ka nishadu sannan zaka zo ganinta, abin ma yanzu ya girnana tunda har ka fara daukarta kuje wani gari ku kwana. Tunda ana tsohuwa ta sama ido, watau bari kayi magani na ka dau ka matarka ku ka tafi inda zaka fi sakewa kayi abinda kaga dama. To bari kaji in gaya maka naji kace yau zaka tafi to kafarka kafar matarka, tunda har kai kasan kana da hakki akanta to itama tana da hakki akanka, ku tafi can inda kowa zai ba dan uwansa kulawa babu mai tauye wa wani, ba wai na gaji da zama da Aneesa bane, na ma fi son ta kasance kusa da ni, to naga idan nace ta zauna nan zan tauye ta tunda sai kayi watanni yanzu kake zuwa gari nan, gara ku tafi tana kusa da kai, ni duk tym din Allah ya nufeka ka dinga zuwa kana ganina. Barin hado mata kayanta. MIJIN ARO 2***5 toh naga idan nace ta zauna a nan zan tauye ta tunda sai kayi watanni yanzu kake zuwa garin nan, gara ku tafi tana kusa da kai,ni duk lkcn da Allah ya nufeka ka dinga zuwa kana gani na.bari in hada mata kayanta. Ta tashi ta soma janyo akwatunan aneesa dake cikin(wardrobe)dinta tana ajewa ,yayi shr kawai yana kallon hajiya can ya gaza hkr yace,hajiyata kiyi hkr wlh duk abin da kikaga yana faruwa nima bada son raina bane,kuma ba don in bata miki rai bane hakan ke faruwa,ki gafarta mini,ni kaina nafi son in tafi da ita kusa dani,to amma gidan daya kamata in aje ta din ne ban sami irin wanda nake so ba,umma insha Allah da an samu zanzo in tafi da ita.hajiya ta hasala tace ai nagaji da jin wannan tatsuniyar ni bance sai ka nemar mata gida ba don banga amfanin naka dankareren gidan ba da zaka aje ta anan ba tunda matarka yar gwal ta hana,to ba zai yiwu ba,nan cikin gidan ka zaka bata nata dakin itama ai matarka ce. Ya sassauta murya yace,nima nafi son ta zauna a gidana to amma rigima da fitintinu ne bana so,shiyasa nafi son kowa tana gidanta,sbd safeena zafin kishi ne da ita bana son ta matsawa yarinyar nan, gashi ita ba mai hayaniya bace,ni kuma kinga ba zama nake ba,sai inyi sati wani lkcn bana kasar nan,in ma ina nan ayyukan gabana basa bari na zama agidan,ki lallasheta yana bata uzurori sannan taa yarda amma sai da ta aje masa sharadi,na yarda na hkr bazata bika yanzun ba,amma na baka sati biyu zuwa uku,idan baka sami gidan ba, kazo ka dauketa ka ajiyeta agidan ka,in kuma baka zoba toni da kaina zan daukota in kawo ta,gidanka ai ba bakona bane,idan munzo sai a koremu. Ya dan sosa keya yace,haka ma bazai faruba. Wama ya isa ya kore ku, sai dai ku kori wani,insha Allah ma zanzo tun kafin kuzo da ire-iren wadannan dadin baki da lallashin ya lallaba hajiya. Ya cikasu da abubuwan alkhairai kamar yadda yasaba yafi. ganin ishaq ya kwna biyu a mahaifarsa zaria,yasa safeena ta tinzira taga idan bata tashi tsaye tayi da gsk ba hajiyarsa so take ta sake amshe danta tamkar da yake sintiri kusan duk sati a zaria,in ya dade ne yayi sati biyu,shi yasa ita da aminiyarta kuma uwar dakinta haj,nuratu suka dada fantsama gidajeb malamai da tsubbu da bokaye don su dabaibaye ishaq katakam a abuja ba cirawa ba motsawa,hakan kuwa akayi,sun sami sa,a Allah yayi masu talala sunyi nasara! Wannan karon ishaq sai da ya shafe kusan wata hudu rabonsa da zari,a kowa da irin shawarar da yake bayarwa game da aurensa da aneesa,wasu suce tunda an san bayin sa bane acigaba da addu,a har ranar da Allah zai karya kadarin abin.ita dai hajiya bata cewa kowa komai ba,nata shirye shiryen kawai takeyi,ita kudirin niyyar data gama zata zartar da abin da tayi niyya ne. Ranar juma,a da safe aneesa tayi wanka tana zaune tana shafa mai hajiya ta dubeta tace,idan kin gama shiryawa kije gidanku kiyiwa babanki da jama,ar gidanku sallama gobe zamu tafi abuja insha Allah duk ma wanda ya tambaye ki kice mijinki ne yayo waya in tafi dake don nasan yan tsegumi na nan dama sun sa ido suga ranar tafiyarki,to gobe Allah ya nufa a gidan mijinki zaki kwana.tayi saurin duban hajiya tace hajiya abuja! Yayi miki waya ne?tace sai yayi mini waya sannan zan zartar da abin da nayi niyya? Tace ni hajiya da kin kyale shi har lkcn da yazo,kada muje matarsa ta wulakanta mu,ko kuma ni ki barni suyi ta gallaza mini kinga bani da kowa can,ni dai ki barni nafi son zaman nan. Ta girgiza kai.ba zai yiwu bane zamanki a nan akwai zalunci,idan na kaiki ko bakida kowa akwai Allah gareshi muka dogara,shi zai kare mini ke 43/koda taje gidansu sallama su hanne sara kan tsegumi sai aka kama sana,ar harda tambayar bin kwakwafi tayi wa aneesa wai mijin nata yazo ne sai tace,baizo ba hajiya yayiwa waya wai mu tafi tare.hanne tayi murmushi tace,to Allah yasa dai wayar yayi, kada a kaiki ki wulakanta tunda matar cushe bata da wata daraja,shi yana can tare da wadda ya gani yace yana so ita kuma hajiya na lura so take tayi masa dolen dole yanzun ko mata ba,a musu auren dole har gara mace,da an kaita ta haihu kiyayya ke wucewa,namijin ko har ya,ya da jikoki sai kiyayyar ta shafesu. Ita kam! Aneesa tayi alkawarin a ranta tunda dai duk lkcn da ta shiga dakin hanne gaisheta sai ta gaya mata mgn son ranta na wulakanci to bazata sake shiga gaisheta ba daga bakin kofa zata dinga gaisheta ta wuce abinta,tunda abin ya zama cin fuska.direban hajiya ya kaita har tudun wada gidan kakanta su umma tayi musu sallama.umma ta dinga yi mata nasiha da yan shawarwari masu kyau na yadda zata kula da mijinta da yadda zata zauna da abokiyar zamanta cikin girmamawa da mutunta juna, ta rike musu ya,ya tamkar ita ta haife su kafin itama Allah ya bata nata. Ranar asabar tun kafin su tafi hajiya tayi sa,ar samun wayar ishaq din,don tun ranar alhamis da dare take ta kiransa bata samu ba.sai ranar asabar din da safe suna tsaka da shiryawa don sammako zasuyi shine ta