Sashe 17
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wannan shawara Hanne bata ce uffan ba, tayi shiru ne tana sakesaken ta hanyar da zata bullo da shirinta yadda zaiyi tasiri a zuciyar mahaifinsu ta gyara zama ta soma cewa, Alhaji ni dai ina da magana dangane da wnnan auren da ake son likawa kanina, yace ina jinki tace gaskiyya Alhaji wannan yarinyar tuntuni na gaya muku bata dace da sagir ba, ni dai a matsayina na er uwarsa na bashi shawara yaki dauka ni kuma ba zanso abinda zai cutar da shi ba. Mahaifiyarsu Hanne tayi caraf tace, kece dai kike ganin aibun yarinyar nan tunda ba kya kaunarta, amma mu ai banda abakinki babu wanda mukaji ya taba aibunta ta, in kuma da tana da wani mugun hali da anyo tattaki an gaya mana, wlh ki kiyayi kanki 'ya'ya mata ne kina da su..... MIJIN ARO 1**12 81) Hanne tace ni wlh gaskiyya ce nake fai in banda shi dan uwa nane, babu ruwa na da wanda zata aura ko cikin gidanmu waye bai san halin Aneesa ba, kwanakin baya fa zubarwar da yarinyar nan muna gani, a gidan nan. Babu irin sakarcin da yarinyar nan batayi, kwanaki fa sadiq yazo yake cemin har gidan nan take biyo sagir ko da yaushe, shine ma yace sai da ya fattataketa yace kada ya kara ganinta a dakinsu, tunda sagir din aurenta zaiyi ba shashanci ba ne a tsakaninsu, banda dakinsu sagir ma babu inda bata zuwa kuma ana zuwa ana gaya min. Haka kuruk kuma sai in kyale dan uwana ya auri shashar mace, ga shi tunda yana sonta bai zai taba ganin aibinta ba, gaskiyya alhaji wannan abin dubawane. Alhaji yayi alamar tunanin can sai yace, wannan maganar ba wai nayi na'am da ita bane. Amma zanyi bincike akai, kuma bai kamata koda za fasa auren ayi da irin wannan zance marar dadi ya fito daga garemu, ba musamman ma ke Hanne akwai zumunci tsakanin ku da su. Kada in kuma jin irin wannan zance daga gareki. Kema kina da 'ya'ya mata kuma ba zaki so ko da sunyi badaidai ba a zo ana yayatawa, balle idan basuyi ba, kinga ranki ba zaiyi dadi ba, kuma ki sani wlh duk abinda kayi wa dan wani za'ayiwa naka, walau khaitan ko sharran, Ina gargadinki da kiyiwa bakinki linzami. Idan dan wani yayi abu mara kyau to kayi masa addu'a shiriya don baka san me gaba zata haifar ba, kai dinnan baka isa ka shiryar da naka ba sai in Allah ne ya shirye su, saboda haka duk mu taru mu nemawa 'ya'yanmu da na sauran musulmi shiriyar Allah. Allah ya shiryar damu dukkanmu, ameen. 82) Shiru Hanne tai maganar mahaifinsu ta ratsata, tabbas! Zancensa dutse, to amma ita fa auren Aneesa da sagir din ne bata so, ita kuma ta rasa hanayr da zata tarwatsa auren shi yasa ta bullo ta wannan sigar, idan tayi nasara hana auren sai ta nemin Allah gafara. ( Ji wani shirme Allah ai baya gafarta laifin da kayi wa bawansa sai in bawansa ne ya yafe, to shima sai ya yafe maka). Duk wata hanya da Hanne zata bi sai da ta bi, tayi kutun2 ta hana auren sagir da aneesa! Balle tana ganin inda sagir ke aiki yana samu sosai har ya mallaki mitar kansa, shiyasa ta sha alwashin Aneesa ba zata aure shi ta huta ba, ita gata nan da na en matan turus! A cikin daki babu mijin aure, in bayan sagir kaninta ne da tuni ta hada aurensa da Haulat to babu hali, saboda sun haramta ga junansu. Ta so ta hada shi da yar kanwar hajiyarsu, mahaifinsu yace sam! Kada ma ta soma, ba zai yiwu ba tunda ta kushe wancan auren ba ta isa ta jona shi da wata ba, duk wadda ya akawo yanzun ita zai aura, babu kuma wanda ya isa ya hana shi auren duk yarinyar da ya kawo ko wacce iri ce. Abban aneesa yaji ciwo sosai da Alhajin su Sagir yayo tattaki da kansa ya bashi hkr, dangane da fasawar auren yaran nasu, magana ta fahimtar juna yayi tsakanin su inda ya haisda masa ce wa dan uwansa ne ya ba sahgir 'yar sa, ahaka dai zancen auren ya sha ruwa wanda shi Sagir har kuka yayi wa Aneesa akan shi dai ita yake so, ba zai yarda ya auri wata ba, bai nuna mata hanne ce sanadi ba. Bai san ta fara jin komai a bakin 'ya'yan hanne ba, ita kam ta rasa irin wannan kiyayya da hanne ke mata ita da mahaifyarta, da uwarta take nunawa daga baya sai abin ya koma kanta, duk wani sharri da mugun alkaba- sai ta dora mata shi, ita ko tunani batayi abinfa da kayi wa dan wani na sharri watarana za'ayi wayi gari ya iya komawa kan danka idan ba abin alheri kayi sai kaga ya sameka kaima da zuri'arka. Shi yasa kullum muyi nufin kulla hairan kada mu nufi kowa da sharri gara ayi ma sharri da kayi ma wani. 83) Wannan lamari ya tashi hankalin Aneesa da duk wani masoyinta musamman Hajiya. Ita kanta Aneesan har ta rame don a daddafe ta iya gama zana jarabawarta saboda zuciyarta na cikin halin bakin ciki da damuwa, ga babban zullumi da take fada da shi wani furuci da mahaifinta ya kira yayi mata na cewa ta fitar da wani mijin kafin su zana jarabawarsu na Neco don da zaran ta kammala ba zai jira komai ba zai daura aurenta ga duk wanda Allah ya nufa, saboda ta bangarensa akwai mutanen da suke zuwa neman aurenta dana ya dakatar da sune saboda akwai wanda take so, ciki ma harda abokansa, kuma idan tym yayi koda abokinsa ne zao daura mata aure. Damuwa tayi wa Aneesa yawa lokacin tana kwance a doguwar kujera a falon hajiya, hajiya ta fito daga daki ta zo ta zauna a gefen Aneesa itama tayi shiru, tausayin Aneesa take sosai saboda irin abubiwan da ke kunnowa rayuarta kai! Ta dubeta tace, Aneesa bana son inga kinzo kin takura kanki da tunani. Duk abinda kika ga ya sami bawa daga Allah ne, dama da kaddararsa ce hakan kuma bawa ba wuce kaddararsa, yanzu kina ganin kafin ku gama jaravawa akwai wadda zaki fitarwa da mahaifinki amatsayin miji? Aneesa ta numfasa tace, babu wani a yanzu don na riga na kori kowa, amma ina rokon Allah kafin wa'adin nan ya cika ya kawo min nagari zan gabatar masa idan ban samu ba. Na amince duk wanda yabani zanyi biyayya inshaAllahu, albarkaxin biyayyan sai inga alheri. Hajiya tace ki kwantar da hankalinki, insha Allahu sai kin auri miji na gari fiye da sagir. Zasu ga sakayyar Alkhairin da Allah zai yi miki, sai sun sha mamaki indai ina raye ba za su ga naka sunki ba, da izinin Allah. Bayan tafiyar Aneesa wani tunani ne. Ya darsu a zuciyar Hajiya wanda itace zata iya sanadin faruwar haka, wanda daddaden buri ne aranta saboda irin kaunar da ke tsakaninta da Fatima wannan shine abu na karshe da zatayi don ganin zuri'ar Fatima bata tozarta a doron kasa ba. 84) Wayarta ta sauka ta kira Ishaq, Yana ganin suanan HAJIYATA a screen din wayarsa sai yayi murmushi saboda abin da ya jibanci Hajiya ko ita kanta jinsa yake har cikin ransa, sabida sanin duk duniya baya da kwatankwacin Hajiyarsa, don har tsiya yayin sa ke masa idan yace Hajiyata, sai su harare shi suce, dadin Abin dai ba kai kadai bane balle kace Hajiyarka. Ya kanyi murmushi ne yace, ni dai nasan tawa ce, in kuma karya nayi sai atambaye ta gata nan, dariya kawai suke yi don sun san da an tambayeta cewa take yi shi kadai ne nata su ba nata bane. Yayi sallama tana amsawa yace, Hajiyata ina kwana? Ya jama'ar zariya, ya su Aneesa. Tayi murmushi, tace duk lfy kowa yake. A ranta dadi take ji idan ya tambayi Aneesa saboda irin kaunar da yake wa yarinyar da wuya ne suyi waya bai tambayeta ba, idan ma tana gidan sai yayi magana da ita. Ita kam, addu'a takeyi Allah ya dorar da wannan kauna har karshe rayuwarsu, Allah sa nufin da ke zuciyarta ya kai ga nasara. Tace, wannan hutun karshe makon zaka sami zuwa zaria kuwa? Yace indai kina son gani nane ai sai in aje komai in zo, ko gobe ne ko yau ne zan aje in amsa kiranki. Tayi murmushi ita kam, bata da haufi akan Ishaq. Saboda ladabinsa a gareta, tace ba zan shiga rayuwarka aikinka ba, ka bari kanar jum'a ko asabar kana iya zuwa ne maganar bana gaggawa bane. Dan halas din kuwa ranar asabar ya iso zaria kafin sallar azhar . Aneesa na gidan Hajiya, ita hajiyan ta sa tai masa lafiyayyen dambun cous2 wanda yaji hanta da joda da kayan lambu, kamshin duk karade gidan. Shi kanshi daga isowarsa kicin din ya shiga ya iske Aneesa da ladidi a kicin din. Ya dubi Aneesa, yace wannan irin kamshi haka, me kuke hadawa ne mai lagawadar kamshi haka, tun daga bakin titi nake jiyo kamshi? 85) ladidi tayi dariya ta nuna Aneesa tace ka ganta nan tunda aka ce zaka zo tace ita zata yi maka girki, ni ban ma san sunan abinda ta girka ba, gashi nan ya cika gida da kamshi. Ya dubi Aneesa yana murmushi yace, ai ni yanzu na yarda dai kanwata kin zama gwanar girki, bansan yadda za'a yi ba, kuma ga aurenki ya matso, idan kika tafi gidan miji, kilan can zan dinga yin waya ana sam mini na angon. Rufe fuska tayi saboda kunya. Shi kam dariya ya dinga mata yace, bari in sassauta belt da neck tie dina yanzu zan fara dibar girkin nan dama da yunwa na shigo zaria, sukayi dariya. Aneesa sai da ya fita a kicin din ta ba shi da kallo yau shigar suit yayi nasu ruwan kasa, sunyi masa kyau tamkar wani bature ga hadadden kamshi da ya baza musu a kicin din ya fice abinsa, kai Allah yayi haddaden gaye anan wurin inji aneesa a zuciyarta. Sai da Ishaq yaci yayi hani'an yaje sallah daga can ya kuma gana da jama'arsa ya shigo gida, ya nutsu sannan Hajiya ta nemi ganawa dashi a dakin baccinta suka nutsu saboda zancen