Sashe 51
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
shine yanzu yace babu ruwanshi. Sai dai in barta ta haihu ni ko ya za'ayi in barta abin kunyar ai sai yayi yawa, shine na dauketa na kaita aka zubar da cikin. Yanzungashi jinni ya yanke yana ta zuban mata, mun koma sibitn sunce sai an kara mata jini, ga uban kudi da suka fado mana, ni kuma nan bani da ko sisi kudin kenan na dauka na kai aka cire mata cikin. Wlh yau sumanta yafi 5 mu kadai adaki, yanzun na jira kawai nake in ga abinda Allah zaiyi akanta. Don Allah Aneesa ki taimakeni mijinki ya rufa min asiri ya biya kudin nan ayi mata karin jinin, jinin jikinta kila ya kusa karewa kada ta mutu a wannan halin. Aneesa tace ki kwantar hankalinki ba ma sai mijina ya ba ni ba, bari in kira driver ya kaimu asibitin zan biya kudin. Hanne ta durkushe gaban Aneesa tana kukan murna yau ita da sawa Aneesa Albarka. Aka dauki haula zuwa asibiti, kudi kare magana nan fa na aka hau yi mata karin jinni da ruwa, sanna likitoci sukayi kokarin tsayar da jinin$ cikin kwana 2 haula ta watstsake, Aneesa ta zauna ta dinga yi mata nasiha sai kuka kawai takeyi, duks ai kunya takeji. Yau ga wadda suke wa sharri suke wulakantawa Allah ya daukakata har ta taimake su tayi msu rana. Tun daga wannan tym din Hanne ta kiyayi duniya. Ta kiyayi yiwa yaran da ba nata ba sharri tunda gashi ya koma kan yaranta tsakaninta da Aneesa sai girmamawa da mutunta juna. Ita kuwa matar Ubansu Aneesa tun wani saki da yayi mata akan, kannin Aneesa ta je ta dawo sai ta shiga taitayinta, ta gane gaskiyya tasan zugata kawai hanne takeyi, gashi ta kusa kaita ta barota, don da aka sake ta sam Hanne bata nuna wata damuwa ba, kuma har bar gidan ta dawo bata lekata ba gidansu. Shi ya sa da ta dawo sai ta kiyayi hanne da yaranta, ta kama yaranta ta hada nasa ta rike su tsakaninta da Allah. 140) Tym din bikin sadiya yaran Aneesa sunyi farin jini kowa sha'awa suke bashi, duk atym Aneesa na makale da yaron ciki tasan da shi son ya shiga wata na 2 kuma bata gayawa Ishaq ba don tasan sai yabi yana gayawa Jama'a musamman Hajiya. Kafinsu Aneesa su koma abuja saida aka saka ranar Aysha saboda abokin Ishaq din ya matsu ayi auren don bai taba aure ba. A tym din Ishaq ya sayawa Aneesa mota sabuwa dal, sannan ya biya mata kujerar makka, ita da babanta yace tayi masa jagora shi zai zauna a gida ya kula da yara don safeena babu ruwanta da sabgarsu.************************************ ****************** Aneesa ta kammala degree dinta na farko a tym aurensu na da shekara biyar, tyn din diyarta na da shekara 1 fatima, wadda Ishaq ya sanya mata sunan maman aneesa suna kiranta zahra. Yarinyar babu inda bar Aneesa a kamanni, shi yasa ma babu jikan da Hajiya take ji da ita tankat zahra. Haka abban Aneesa kullum zancensa zahra sai mutane na ganin don taci sunan marigayiyar matarsa ne ya kallafa ransa akanta. Ranar wata asabar Ishaq daga yake kasar dubair daga can ya wuce da fasinjoji china satinsa guda sannan ya dawoam Aneesa ta basshi da yara suna ta bashi labarai, er lelensa zarha na kanwace bisa kirjinsa ta lafe hannunwanta guda2 na tsakiya suna cikin bakinta tana tsotsa. Aneesa Wanka tayi ta zuba wata fitted gown ta shadda dinkin ya kama kwankwasonta yayi mata kyau sosai, ta baza tutare ta fiti falon ta sameshi a kwance sai ya tashi zaune, Aneesa ta ruda shi ya dubi yarn yace, yusra dauki zahra ku tafi gurin Atine zanyi bacci ne kuyi wasa acan. Sukayi sukayi su dauketa sai ta sake lafewa a jikinsa. Ya dubi Aneesa ya kanne mata ido ya nuna mata zahra ta zo zata dauki zahran ta sake makalewa dole da kansa ya dauki zahran ya kaima atine, ita ce mai kula da harkokin yaran gidan dukknasu, yace ta kula da su zaiyi barci ne, ta amshi zahra ta goya suka nufi filin wasan yaran ita da sauran yara. Yana shigowa yake ya kwana bisa kirjin Aneesa yace, kwana 7 ina kewarki na dawo yara sun hanani sakat, tace wa zai hana ka sakat idan ba cingam dinka ba zahra. Ya dauko brief cas e dinsa ya soma ciro ambulan ya soma ciro da battoci na sarkoki yace zo kiga abinda sa aka yo muki a dubai kowa da sunansa, gwal ne kirar dubai an subuta sunanta da na safeena, sai na su yusra da na zahra da yafi na kowa tsaruwa, sai dai kudin su daya na da su Yasmin din. Ita nata da na safeena duk kudinsu daya har da zobuna da awarwaro gashi kirar tayi kyau sosai. Aneesa tana rike da su tace amma yayana kasha kudi sosai alhalin kasan muna gwala2 tunda ga kirar saudi, england, da dubai din, yace to in ba kashe muku kudi ba wa zan kashe mawa? Ko kuna da maiyi muku hidima ne bayan ni? Ta girgiza kai tace, bamudashi sai kai. Allah ya karabudu, yasa kayi mana hidima fiye da wannan nan gaba. Yace ameen, ya riko hannunta yace zo muje mu kwanta Allah da gaske barci nake ji kwanana 7 bana iya barci saboda ba sami dumi yadda nake so. Yana rike da hannunta suka haye sama, inda dakin barcinta yake, anan ne zai sami dumin da yake so...... KARSHE TAKU HAR KULLUM RAHMATU HASSAN ZARIA, TARE DA ADMIN DIN HAUSA NOVEL BOOKS SAI MUN HADU A WANI LITTAFIN.