Sashe 3
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fatima saboda larurrta da ya sameta$ Da Ali ya dawo ya iske da halin da ake ciki. ya tasuaya mata matuka shi yasa da zai koma ya shawarci mahaifinsa da Yayansa akan zai tafi da matarsa gurin aikinsa, tunda sun ba shi gida, hakan kuwa akayi, ba su snara da marikiyarsa ba don hanawa za tayi shi yasa mahaifinsu yace suyi gam da bakinsu, sai ranar tafiya sannan suka shiga suka yi mata sallama. ai kuwa kuka ta saka wai ya nuna mata lyakarta din ba ita ta haifeshi ba. mhaifinsu shi ya kashe maganar da cewa da izinina zai tafi da matarsa din zaifi kulawa da lafiyarta acan. Tunda suka tafi Fatima bata zo zaria ba sai bayan da ta haifi Aneesa a Calaba, shi dai bai fasa zuwa duk karshen wata ba yana kawo musu abin da yake kawo musu ba kuma zuwan nasu bai hana marikiyarsa mitar ya guje su ba. da aka haifi Aneesa washegari a sako su a motar sa suka nufo Zaria don a kula da lafiyarta. iyayenta sun zo daukanta ba a basu ba sai da aka zo aka zauna da ita. 'ya'ya 3 Fati ta Haifa a Calaba sannan aka yo masa transfer zuwa zaria$ a tym din su Aneesa da kanneta basu cika jin hausa sosai ba sai yaren ibo da turanci da turanci saboda cudanya da sukayi dasu acan. shima nan ansha gori wai an gurbata tarbiyar 'ya'ya tunda basu iya yarensu sosai ba sai yaren wasu. zani ma basu iya daurawa ba dawowarsu aka koya musu.. Amma kuma bata lura ba bakinsu ya nuna da karatun addini gashi da sun ji kiran sallah suke zuwa suyi, ko da yake ta lura da haka fada ne ba zata yi ba, aibun su shi ya fi mata dadin fada, wanna bata rashin yiwa dan adam adalci bane. Su aneesa sun girma al'amura na canzawa, saboda kiyayyar da ake ma mahaifiyarsu ne sai ya koma kansu balle gasu tubarakallah masha Allah kyawawa irin uwarsu babu ma kamar Aneesa da ta dauko kyan uwarta dirin jiki kuma da fari na babanta, tunda shi farine , mahaifiyarsu kuma wankan tarwada, tym din tana Calaba cikin jin dadi da kwanciyar hankali sai ta zama kamr wata half cast. al'amuran sun cika gaba da canzawa har aka wayi gari irin soyayyar da mahaifinsu ke wa Fatima sai ta ragu, Rashin zaman lfy da kwanciyar hankali ya dinga wanzuwa a tsakanin ma'auratan wanda an rasa gano musabbabin hakan. ashe wanan hadin duk hadi ne daga marikiyarsa, da wasu 'yar surkulle da ake masa har kwakwalwarsa ta juye. idan a'amuran sun fara, Fatima ta taba zuwa ga mahaifanta ta fada sai sukace maza ta tashi ta koma dakin mijinta ko wace mace da ta gani hkrn zaman aure tae.. Shikenan sai ta daina zuwa gidan, sai tayi ta kuka tace ita ba yaji tayo ba, ta zo ne don su san halin da ake ciki ko za su kira shi don a daidaita matsalolin da ke knnuwa aurensu, saboda acan idan ta gayawa markiyarsa bata daukan abin da muhummanci, in kuma tayi magana to ita ake dorawa laifi ko da ita take da gaskiyya. duk da haka iyayenta da yake dattawan arziki ne sai basu goya mata baya ba suka ce ta tafi za su san abinyi. Gurin mutum daya awajen gidan nan take samun shawarwari da dukkan wani tallafi. in ka debe mutum2 a cikin gidan watau baban sasa da da maryarsa Halima, tun far kon aurenta aka yi mata uwar daki da ita Hajiya Asma'u wadda kowa ke kira Hajiya, babu alakar jini a tsakaninsu amma zaka ranste ya da kanwa ne. tunda ta girme ma Fatima. gamuwar jini ne kawai yasa Hajiya ke ji da su. Gidan da Hajiya take katafare ne na saurata kuma na tsofaffin masu kudi, karamci da mutnci da sanin kimar dan adam da addini sunyi zaman dirshan a zuciyar Hajiya da jama'ar gidan, musamman mai gidan kafin rasuwarsa, ita kadaice macen aurensa da yaranta4, mata3 namiji1. Duk wasu hidaman Aneesa da uwarsu da kanninta Hajiya bata gazawa da yi musu tamkar gudan jinita, donta so baban Aneesa ya bata amma yayi mirsisi ya hana duk da take. kayr fari shima ita yafi so cikin yarans, ya dai yarda ta je ta wuni, idan ma zata kwana a can Hajiya ta aiko ba yahanawa, shiyasa ta hkr da nacin yabataita. MIJIN ARO 1**4 Ranar litinin Mahifin Aneeesa bai barta taje sch ba, tana gida har ya fita zuwa gurin aiki, ta shirya kannenta suka tafi sch, yayi saura daga ita sai mamanta a gidan. Ta tashi ta gyara gidan tas tayi wanke wanke zatayi wankin yaran sai maman ta hanata tace, Bar wankin nan masa kiyi wanka in aike ki tudun wada gurin Ummata. Aneesa da hanzarinta taje ta yo wanka ta shirya duk da ita Allah bai yo ta mai son kyale kyalen mata ba, ita ko kwalli bata sawa daga vaselin sai farar hoda sukenan kayarn shafarta, har kanwarta mai bi mata ta fita iya kalailaita ita kam duk wannan baya gabanta, don dai Allah ya bata kyau dan asaline shiyasa ko tayi kwaliyya ko baatayi ba kullum fuskarta tas zaka ganta. Maman ta gaya mata sakon maganar kudi ce na komawa asibiti yin hoto, shi Abbansu yayi biris da lamarin Aneesa tace, Mama ko in ranto gurin Hajiya tunda wata ya kusa karewa idan aka yi biyan basukan anko nana ba sai ki bata ba? Amma Umma sai in ga kamar kina takurata ne, Maman tayi murmushin takaici tace, karama to ya zatayi,? Ni nasan abinda yasa ba kya son zuwa saboda kina ganin idan na aike ki amso kudi gurinta ranta na baci ba wai bata da shi bane yasa take bata rai ko bata son bayarwa. haushi halin ko in kula da babanki ya mini shi ke damunta tunda ta san duk abinda zan nema gurin Abbanku baya rasa bane. bayarwa ne ba zaiyi ba, kin ga kuwa dole uwa taji zafin ba a kyautatawa diyarta ba$ kta kuma Hajiya ko na ranta idan na mayar mata ba amsa takeyi ba, shi yasa bana son zuwa, tashi dai kije gurin umman, ki gaishesu.Ta mika mara Naira Hamsin kudin mota ta amsa ta saka hjiba dinta ta tafi. Tana zuwa dai2 gidan hajiya ta hangi motar dan Hajiya da ke aiki aAuja ya zo har zata wuce taji shai songaitwins da matarsa ke goyo.Alahyasaita ai tunda aka haifi Yaran take bala-n son su, lafiyayyu. farare kyawawa da su tamakar 'ya'yan turawa suke. Tun suna jarirai wani zuwa da sukayi suka kwana da za su tafi taje tayiwa Hajiya rada annne wai da su tafi da ita gidansu ta taya. Auntyn Abuja rainonsu, Hajiya ta dubeta Galala tace, saboda rainon su twins zaki bisu Abuja ki bari karatunki? Lallai wannan soyayya taki da yaran nan tayi girma, keMa Allah ya sa ki fara da twins din. tana jin hakan ta fyalle da gudu bata ma tsaya taga tafiyar en abujan ba. Rokon Allah ta dinga yi Allah ya sa taga aunty abujan aka zo, dan taga en 2 ai kuwa tana shiga taga yaran a cinyar kakarsu. Sallama kawai tayi a falon ta suri daya tana fadin Hajiya wannan waye na dauka Sultan ko Suhail? Hajiya tace kema kenan uwarsu baki gane su balle ni ina jin wannan ne Hassan. Aneesa tace yauwa ga sultan kenan. Ta juya ta soma gaida uwar yaran. dake zaune can doguwar kujera ta amsa mata da sakin fuska, albarkacin tana son yaranta kamar ta hadiye su, In baya ga haka ba kowa take wa fara'a a dangin mijin nata ba, shiya sa ba kowa ke shiri da ita ba. Hajiya kadai take shakka kuma ita kadai ke kiransu da sunansu na Asali Hassan da Hussain tunda aka haife su Hajiyan tace abar musu sunan su ita kuma uwar yaran ta. cewa mijinta wai kauyanci ne wannan sunan yayi common da yawa, tafi son sun unique shine ta zaba musu sultan da suhail, kuma haka kowa ke gaya musu. Akkala yanzun yaran sunyi shekra2 da haihuwa. Suhail shima ya taso daga cinyar Hajiya yana cewa Aunty nima. Ya mike hannunwansa wai shima ta dauke shi. Tayi dariya ta sauke sultan tace yi hkr da ma zan dauke ka ai. Mamansu ta danyi murmushi tace ya dauka yawo zaki tafi da sultan tunda ya ganki Da hijab, haka suke wannan kishin idan mai rainon su ta dauki daya shima dayan dole ta dauke shi. ta dauki Suhail din sai sultan ya fara kuka, haka nan ta hada su ta dauke su tana nishi saboda yaran kosassune. kujerar da maman su take ta akaisu ta zaunar da su tace, ku zauna anan bari in je in kawo muku chocolate zaku sha? Gaba dayansu suka amsa eh, ta zo gaba Hajiya tace, Hajiya bari naeTudu wada gidan Umma, Mama ta aike ni. Tace, to sai kin dawo ki gaida Umma, idan kin dawo ki biyo ta nan Yayanki na son ganinki. don tunda suka zo yace a kiraki, yaunxun kuma ya fita ganin abokin sa A GRA tace, bari nayi sauri in dawo. Tayi Rashin sa'a don bata sami Umman ba sunje dubiya asibiti, saboda haka dole ta zauna jiranta saobda muhimmancin sakon da zata amsa, tunda goben Maman zata koma asibitin. Har tayi azahar taci abincin ta dan kishingida sai wajen 2pm sannan Umman ta dawo$ Duka taji a gadon bayanta Umma nacewa, wacce raguwarce ke min minshari a daki, daga ci sai bacci, wannan ai sai ki firgita mtane da minsharinki. Ta tash tana sosa wajen, ni wlh kada ki karya min baya ki yiwa mijina sara, tunda kin san nafi karfin kwartakwashin mijinki. Haka suka yi ta barkwanci. Aneesa sai wajen 3pm ta bar tudun wada. abakin kasuwa ta tsaya ta sayi jakar Eclairs don ta kaiwa su Sultan da tayi musu alkawari. jikinta ne yayi sanyi tunda taga bata ga motar su a harabar gidan ba, ba dai sun tafu ba? kila sunje wani gurin ne ta san dai idan suka zo yawanci kwana sukeyi. Tana shiga Hajiya ke gaya mata sun tafi wai Yayanta ya dawo har can gidansu yaje akace bata dawo ba, kuma basu dade da tafiya ba. Taja