Sashe 48
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ya rasu twins ne dan uwansa ya rasu shima gadhi yau ya rasu dan Allah likita ka taimaka kayi iya kokarinka kada tayi bari da sassarfa likitan yabi bayan nurses din yana ba ushaq tabbacin zasuyi kokari in Allah ya yarda cikin ba zai zube ba..........A yadda ishaq yake a rude ya dauki wayarsa ya shaidawa haj rasuwar suhail sannan ya gaya mata halin da aneesa take ciki...itama a rude ta soma salati a innalillahi sannan tace direba zai kawota Abj komai dare...ishaq yace kiyi hakuri kinsan tafiyar are babu dadi ki bari da kin idar a sallar asuba sai ku tawo da kyar ya dinga lallashinta ya shawo kanta ta hakura sai gobe. 126) Dare babu dadi ki bari idan kun idar da sallar subahi sai ku taho. Da kyar ya dinga lallashinta ya shawo kanta ha hkr sai gobe. Yayi waya gidansu safeena ya sanar da iyayenta, amma yace gasu nan a sibiti yanzun zasu amshi gawai zuwa gida. Ya kira wasu muhimamman abokansa ya shaida musu, ashe ma safeena ta gayawa en gidansu suna asibiti, suna hanya ne kuma Ishaq ya gaya musu rasuwar suhail kafin ya iso dakin da take har sun riga shi isowa, a bakinsu taji rasuwar danta, habawa ai sai ta zauce ta kama surutai na fallasa da rashin hankali, wayyo na shiga 3 nayiwa kaina sanadin mutuwar dana gashi nasa an juya min mahaifa ba zan sake haihuwa ba, shikenan haka zan rayu da 'ya'ya 2 ba namiji a ciki, duk takamar in mallake gidan Ishaq ta tashi abanza tunda ga wata ya auro zata haihu wai ma yanzu ciki gareta zata haifi en 2, ina! Wane ke da haihuwar en 2 sai na salwantar da cikin nan boka yasa aljani ya sace mahaifar taki in ga tsiyar haihuwa, wlh za ki haihi agidan nan ba sai na kore ki, sai dai ki haihi a titi. Haka ta dinga wannan fallasar en uwanta na rirriketa suna rufe mata baki amma bata fasa ba, duk wanda ya shigo ya iske haukar da takeyi, kunnesa ya jiye masa wadannan mugan abubuwan da ta aikata da ma wadanda take shirin aikawata, Ishaq ya dubi en uwanta da sukayi tsaye chirko2, yace kinji ko? Ita da aminiyarta gidan boka sukaje mini da yara har birnin gwwari ban sani ba tayi markayra zata je duba ita aminiyartata bata da lfy shine, Allah ya aiko musu da wannan hatsarin ita ma kawar bata can emergency rai ahannun Allah. Yanzu don Allah aunty ina anfanin mutumin da ba zai barwa Allah lamarinsa ba, sai ya dangana da gurin boka? Yanzun idan suka mutu a wannan hanyar me zasu ce wa Allah? Kafin Aunty tayi magana safeena tayi karaf ta zabura tayo kansa zata shake shi tana cewa, wlh baka isa ka hanani zuwa gidan boka ba, tunda yace zai sa aljani ya sace mahaifar Aneesa ba zata haihu ba, wannan cikin da kake murna zubewa zaiyi, tunda nima nasaka aka juya mahaifa ba zan sake haihuwa ba kaima baka isa ka sake haihu ba sai a haifo ma shege a titi ba dai dan sunna ba. 127) Sakeni Aunty wlh sai na salwantar da cikin en 2 nan tunda nawa sun mutu. Ishaq da kyar ya kwaci kansa saboda shakar da tayi masa, ya fita yaje ya gaywa likita halin da ake ciki suka zo sukayi mata allurar bacci a haka enwata suka ce gara a maida ita gida tunda bata ji ciwo ba, aka sakata a mota suka tafi gida, shi kuma Ishaq da abokansa suka amshi gawar suhail din suka tafi gida da ita, sai da safe ne za'ayi jana'izarsa. A daren Ishaq ya koma sibitin yaa tarar ikon Allah likitocin sunyi kokarin tsayarwa da Aneesa jinin da ke xuba mata, amma ita daa likitocin sun sha wuya musamman ma ita da dinga suma. Suna gama mata komai sukayi mata allurai aka gangarota zuwa wani daki na musamman ita kadai ce a dakin. Tym din da Ishaq ya dawo tana barci sai wata nurse ce akujerar gefen gadon a zaune da littafinsu na nurses a hannu tana nazari. Yayi mata sannu tare da godiya tace, babu komai wannan aikinmu ne tsayawa tsayin daka akan mara lfy, dama Dr. Usman yace in zauna gurinta in kula da ita, kun tafi da yaron da yarasu, idan kun dawo to idan baka dawo ba in kwana da ita, ina ganin in ba damuwa kana iya komawa gidan zan kula da ita har zuwa gobe, yace nagode Allah ya biyaki, ki bari zan kwana da ita zuwa da safe sai kizo gurinta ni in koma gurin jana'izar yaron. Ya je ya leka Aneesa tanata baccinta lakadan. Ya koma gefen gadon ya zauna yana kallonta. Nurse dinan tayi masa sai da safe ta tafi. Tun wwajen asuba Aneesa ta farka idon Ishaq 2 ya ji salatinta ya dubeta yace, sannu Aneesa ya jikin yanzun me ke miki ciwo? Ta nuna masa kasan mararta, ya ce sannu Insha Allahu zaiyi miki sauki. 128) Tayi masa tambayr da yake ta zullumi... Ya Ishaq suhail ya mutu ko? Yace bai mutu ba yana nan da ransa, waya gaya miki ya mutu? Tace ina ji da likita na gaya maka, yace bakiji sosai bane, amma yana nan gashin jawo saura kiris ya rage cikin jikinki ya fita, haba Aneesa ko mutuwa yayi ashe ba zakiyi tawakalli ba irin na musulmin kwarai? Hawaye ya ziraro mata tace zanyi mana, Allah ai yafi mu sonsa idan ma amshi abinsa. Ya soma yi mata wa'azi sosai cikin hikima da dabara ya gaya mata rasuwar Suhail, tayi kuka sosai kuma bai hanata yin kukan ba saboda yasan irin shakuwar da sukayi da yaron, in dai yana gida baya zama gurin uwarsa yana can makale da Aneesa adkinta, in bacci takeyi tunda sarkin bacci ce shima zai kwanta a gefenta yayi baccin dole, sai gashi rana tsaka Allah ya raba wannan kaunar ai dole Aneesa tafi kowa rudewa. Yace mata kiyi hkr hajiyarki na nan isowa don tun jiya nayi mata waya idan ta zo zan kawo ta gurinki, ina jin ma idan likita ya zo anjima zance ya sallameki in dai babu matsala, gara ki koma gida nima hankalina zaifi kwanciya guri daya. Sai da su Hajiya suka iso misalin 8am akayi jana'izar suhai akaje aka suturta shi, kuna har wannan tym en safeena bata daina wadannan surutan fallasan da takeyi ba, don wasu ma gani suke tamkar ta sami tabuwar hankali ne don wannan abu bana lfy bane. A ranar da yamma aka sallam Aneesa suka dawo gida ita da Hajiya. Ishaq ya maida hankalinsa sosai wajen kula da lfiyar aneesa, sannan kuma ga Hajiya ya nata komawa zaria saboda kula da Aneesa, sannan bai san me zaije ya dawo a gidansa ba saboda rasuwar Suhail ta zautar da safeena, kullum yunkunrinta na a barta ne ta nakasa cikin Aneesa, shi yasa Hajiya tace ya bata Aneesa ta koma da ita gida zaria, shi kuma ya dage babu inda za'atfi da Aneesa sai dai ita safeena iyayenta su tafi da ita gida acigaba da yi mata magani, shi kam yayi alkwarin daga naira daya har miliyan ko nawa ne zai biya ayi mata magani. 130) Dakin dake dab da na Hajiya nan aka gyarawa Aneesa ta yaddaa zata dinga jin motsinta, kuma ko da haihuwa zata zo suna kusa da juna. Ranar asabar da wuri Ishaq ya iso zaria, su hajiya da ladidi da su yasmin duk suna falo suna kallon wni film din larabawa aa tashar OTV, aneesa ce kadai ke daki, tace wai bacci zatayi alhalin ciwon mara takeji kadan2 ta ki fade ne kada Hajiya tace su je asibiti. Su yusra da ihunsu suka makalkale daddyns, dukkansu ya rungume shu yana tambayarsu, ina auntyn ku? Sukace tana daki wai zatayi bacci ne. Ya zauna kujera gefen Hajiya yana gaishe ta, sannan yace, Aneesa lfy take daki ita kadai bata fito cikin mutane ba? Tace yanzu na fitoo gurinta tace min wai bacci take sonyi, amma na lura kamar akwai inda ke mata ciwo dauriya dai takeyi. Yace to ba sai aje asibiti ba, tunda sunce da taji ciwo akaita. Tace ciwon nakuda suke nufi nima idan naga shine ai ba zan barta a gidan ba. Ya mike ya nufi dakin, a kwance ya ganta shima cikin yana kwance gfe, tana ganinsa ta saki murmushi, dama tunaninsa takeyi. Su Yusra na biye da shi, ya so ya rungumeta ajikinsa ko yaji sanyi amma cingam dinsa idanunsa kyar. Sannu da zuwa sam banji shigiwarka gidan ba, yace ya zakije kin makale a daki ke kadai, me ke damunki ne? Ko haihuwar ta zo ne? Tace bata zo ba amma tana nuna alamu. Yace ai tuna EDD dinki ya yi zan zauna har Allah ya saukeki lfy don ko na tafi hankalina ba zai kwanta ba tunani na yana gareki. Ya dubi su Yusra ya mika musu ked in motarsa yace, kuje ki kaiwa ladidi a bude bayan motata a fito da kayan ciki har da tsarabar ku na nan. Suka amsa d gudu suka fita suna murna. 131) Suna fita ya ja Aneesa ya kwantar a kirjinsa yana sauke ajiyar zuciya yace, ni kinga tawa tsarabar nan yanzun ne zan sami kwanciyar hankali idan na jiki ajiki na, Allah dai ya sauke ki lfy ko na samu in dan rage abinda ke damuna, Abuja ba mai bani agaji anan kuma Hajiya ta kasa ta tsare balle a dan tallafa min a dinga rage min kewar da ke damuna. Murmushi kawai tayi ta riga tasan halin mijinta, to ya zatayi en 2 sun hanata hasala komai, fatanta ta rabu da cikin lfy sai taci gaba da yi masa yadda yake so, tunda hakan ne farin cikinsa. Sunyi hira sosai daga zuwansa har dare, da kyar suka rabu yaje ya kwanta don ma Hajiya ta koreshi ne tace ya kyale mata yarinya ta samu ta kwanta ta huta don tunda yazo ya hanata sakat. Ai kuwa yana tafiya ciwon da ta wuni tanaji kadan2 a mara yayi sallama, ya taho gadan2, Allah yasa dare baiyi ba wajen goma da rabi ne na dare, sai hajiya ta kira shi a waya tace masa ya zo, daga shi sai rigar bacci