← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 51

Sashe 19

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan danwa rikon sakainar kashi. Ishaq ya zayyane musu abinda ya kawo shi, suka taya shi murna. Ya kawo kudi dubu ashirin yace su kai na gaisuwar duk yadda akayi zai kira yaji, ya kawo dubu biyar2 ya ba su. Alh. Sani yace Madallah an gode Allah ya kara budi, munga kayan abinci direban ya kawo Allah shi albarka. A mota Ishaw tunani kawai yake yi, shi kam! Aransa bai jin son Aneesa ko kyas! Illa kaunarta da tausayi da suka gauraye da jininsa, shi dai umarnin duk abinda ya shafi Hajiya tace masa yake bi don ya faranta mata rai, tunda ya lura in har ya kuskurewa wani umarnin nata akan auren nan to zai daina ganin farin cikinta, shi kuma da ya daina ganin farin cikinta gara shi ya sallamar da nasa farin cikin tunda yasan yanzun rigima ce zata bullo a gidansa muddin ya gayawa Safeena zancen nan, don bai san ya zata dauki lamarin ba, tabbas! Ya san zayi ban kwana da zaman lfy a tsakanin, kaga kenan zaiyi bankwana da farin ciki, yana komawa ya gayawa Hajiya yadda sukayi, sannan yayi sallama da su ya wuce Abuja. Aneesa har zata tafi gida sai Hajiya ta kirata dakinta tace ta zauna zatayi magana da ita ne. Sun danyi shiru na en sakonni sanna Hajiya tace, Aneesa yanzu kina ganin akwai wani da zaki fitar nan da wata biyun da abbanki ya gindaya miki? Ta girgiza kai tace, Hajiya wa nake kulawa? Duk fah na gama korar samarin babu mai zuwa ko wa shakkata yakeyi, yanzu bani da zabi idan Allah kawo min wani to, idan bai kawo min ba haka zan hkr da duk wanda Abban ya zaba mini. 91) Hajiya tace kada ki damu ni nayi miki zabi, amma bansani ba, ko kice ba kya ra'ayin wanda na zabar miki. Tace Haba hajiya wlh ko kuturu ne kika zaba mini zan aura a yadda matsayinki yake a gurina, balle nasan duk wanda zaki zaba mini nagartacen ne wuya za'a same shi da wata mummunar illar duk yadda kika yi dani dayane. Hajiya ta numfasa tace, nayi miki miji kuma ba wani bane sai yayanki. Ta ware idanu tana al'ajabin sai tana jin tamkar kunnenta baiji sosai ba, ta tambayi Hajiya, Hajiya wane yayan nawa? Tace yayanki na nan gidan ina fatan ba zaki watsa min kasa a idanuna ba. Aneesa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace, Hajiya ban zan taba watsa miki kasa ba, amma ai yaya Ishaq ba tsaran aure na bane, ya fi karfin matsayi na, yayi min fintinkau, sannan matarsa tafi karfina, wayayyace ba irina ba ce, kuma da kunnena naji tana fadin yadda ta tsani kishiya, wai ko wani akace za'ayiwa haushi take ji, to balle ita, wlh ina tsoron wannan furucin nata. Hajiya tayi dan murmushi tace, kuruciya manya to Aneesa ai babu matar da zakiji ta furta tana son kishiya da bakinta, kuma ba wai kishiyar ita kanta ake tsoro ba, a'a makircin da zata shigo da shi gidan ake tsoro, wata bayannanen makirci wata boyayye na karkashin kasa, za'a yiwa wadda aka tarar har sai an fiddo ta gidan ta bar yaranta, wata kuma da alheri take shigowa, ta gidance zata ce sam bata yarda ki zauna ba zata shiga ta fita da makirci tabi karkashin kasa harda bin malamn tsibbu. Sai kin fita kin bar mata gidan, haka suke cewa wai gida nasu ne miji na su ne. To duk idan akayi hkr ke ta gidan kika tsare gaskiyya kikayi nufin idan ta zo zaki zauna lfy da ita, ki riketa da zuciyarki tsakani da Allah. To ko ta zo da mugun hali gidan da izinin Allah sai kyakkyawan kudurinki ya ruguza nata, idan kuma itace ta zo da nufin alheri ke ta gidan sharri a zuciyarki nan ma zaki ga Allah ya dorata bisa kanki, har ma ace daga zuwanta ta koreki. Alhalin zuciyarki ce babu kyau, amma duk idan zuciyar kowa ya tsarkake babu wani mai mugun kulli tsakaninsa da dan uwansa sai kiga zaman lfy ya wadata gidan. IJIN ARO **part 13 92) Ki kwantar da hankalinki da alheri a zuciyarki zaki shiga gidan. Ni ma da na hada auren ba da wata manufa na hada ba, fatana shine ya kasance alheri na kulla, in ma kinje gidan ki taddata da wani mugun kudiri a ranta, to ke kada ganin haka yasa ki canza alherin da ke xuciyarki, ya rikide mugun nufi, ki bar zuciyarki da alherinta Insha Allahu zaki ci ribar kyakkyawan kudurinki. Yanzu abu daya nake son inji daga gareki, kin amince ko baki amince ba? Kada kiyi shayin gaya minin gaskiyya kuma bana son ra'ayinmu ya sha banban a gaban mahaifinki don yau za'aje gidanku da maganar. Shiru kawai Aneesa tayi tana sauraron jawabin Hajiya. Ita kam! Gaskiya ta fada Ishaq yafi karfinta, don kuwa shi ajin farko ne a komai don hadadde ne na shiga gasa, ga kyau ga kudi ga tsabta da addini da taimakon addinin ga son 'yan uwa da taimaka musu, ita dai har yau ba taba ganin aibu ko wata illar tasa ba, komai yayi birgeta yakeyi sai take jin itama duk ranar da tayi arzikin kudi irinsa halayyarsa zata dinga kaman tawa, ita kam! Ba zata ce bata sonsa ba, saboda tun asali sun gidan tare ne kusan ma a inuwa daya suka rayu don tun tana tsumman goyo take karakaina a dakin mahaifiyarsa, shi yasa suka taso daga iyayensu har su kaunar junansu sukeyi, da abu ya sami daya nan da nan zaka ga sun taru sun kokawa juna idan na bakin ciki ne haka idan na farin ciki ne tare da yinsa, sau da yawa idan yayo waya zaizo zariya sai taji farin ciki, ya cika ta duk sai ta kosa ya zo ta ganshi, balle idan yace da 'ya'yansa zai zo, har mafarkin takeyi saboda yaransa kyawawa ne irinsu masu kwarjini kamarsa. Ita dai bata san dalilin da yasa take jinsa a ranta ba ashe akwai wani alheri da Allah zai kulla ne a tsakaninsu nan gaba, wai ita aneesa zata zamo matar captain Ishaq! 93) Shararren matukin jirgin saman da gwamnatin tarayya ke ji da shi saboda fasaharsa da baiwar da Allah yayi masa ta iya kirkire2 ba ma anan kasar ba har da kasar yaje yayi bama anan kasar kadi aka ji da shi ba har kasar da yake yayi karatun sa (Germany) sunyi alfahari da shi a matsayin dalibinsu da yake shiga cikin masu jajayen kunnuwa yana kirkire2, su dama nasara irin mutanen da suke so kenan masu baiwa shi yasa tym din suka fifita shi, suke ji da shi, da ya gama karatu suka nemi rike shi a wani kamfaninsu na kere2 jirage, da gida da albashi mai tsoka za su ba shi amma yace ba zai iya zama can ba gara ya dawo kasarsa cikin addininsa da ala'adarsa da en uwansa. Hajiya tace, Aneesa naji kinyi shiru, bana son in tauye miki hakkinki meye ra'ayinki. Ta sadda kai kasa saboda yanzun har ta fara kunyar Hajiya tace, na amince Hajiya, wlh ko yaya Ishaq ba na gari bane zan iya miki biyayya in aure shi balle halayyarsa da dabi'unsa zuwa mu'amularsa babu abin kushewa, amma hajiya shima ya amince? Naga fa yana son Aunty safeena sosai. Hajiya tayi murmushi, ya amince sannan don yana sonta shine ba zai kara aure ba? Ai duk wadda kika ga mijinta ya kara aure ba wai baya sonta ne, wani ra'ayinsa ne wani kuma koyi da Manzon Rahma (saw) ne, kalilan ne karawa don matansu ba su kyautata musu, duk irin son da yake mata zai iya yi miki fiye da nata, in dai kina kyautata masa don babu abin da Namiji ke son irin kyautatawa, kamar yin masa ladabi da biyayya da gudun bacin ransa don son abinda yake so in dai bai sabawa shari'a ba, da son en uwansa, idan kika rike wadannan to zaki kama namiji a hannunki. 94) A wannan rana magabatn Ishaq suka je gidansu Aneesam dama Hajiya ta fara sanar da Abbansu Aneesa. Su ka ba da kudin gaisuwa aka yanka musu sadaki dubu talatin amma baban sasa yace ko ranar daura aure ne suna iya kawowa. A cikin gidansu Aneesa tsegumi ne ya dinga tashi daga bangaren Hanne ta dinga yada habaici a tsakar gida. Oh! Allah mai iko wannan auren huce haushi kenan ko auren me? Allah ya raka taki gona bamu kwashi ragowa ba, ita ta kwasarwa danta, an cuce shi. Sai diyarta Haula tace, mama kika sani ko shima ragowarsa ce tunda dai dubi irin hidimar da yake mata ba dangin iya ba na baba, ga gidanshi da take zuwa wai hutu, kika san me suke yi a can Allah sarki matarsa duk anje an gane mata sirri ga shi za'a daure mata miji. Uwar tace, au dama me ne gaya muku kwanaki, daman ace daga hutu sai kunji wani abu ya bullo kinga kuwa ashe zancen aure ne zai biyo baya. Haka suka yi ta wannan tsegumin da sharrin don halima ta tanka musu, bata tanka ba, sai dai ta bari 'ya'yan Hanne sun fita sai ta same ta a kicin tace, wlh maman haula ki bar kushe da hassada saboda taki ne ga mai rabo, kin kushe Aneesa kinyi mata sharri sai ga shi Allah ya bata miji wanda ya fi kaninki shine kuma ke da 'ya'yanki kuke hassada, har uwar yarinyar nan ta bar duniya ba taba tanka wa sharrin da kike mata ba, ita da diyarta, hakan bai sa ki nadama ba yanzu ma bayan ranta bi ta da kulli yana cigaba, to yanzun kina hadawa da dan manya dan masu galihu ina tsoron ranar da wannan sharrin naki zaije kunnen uwar yaron nan in kina ganin Aneesa bata da gata shi dan gata ne, kuma shi wani ne, zasu iya daukar mataki akan irin wadannan sharri naki, ki tsaya kan Aneesa ko ki gyara bakinki kiyi masa linzami don Aneesa yanzun matar manya ce, idan kika ci gaba da mata bita da kulli mijinta zai dauki mataki akanki ke da 'ya'yanki, idan kunne yaji to gangan jiki ya tsira, Hanne ta tafa hannu tace, to kinibabbiya, kina iya zuwa ki gayawa Hajiya nayi wa danta sharri
Chapter 19 · 0% Book details