Sashe 35
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne ke fizgarsa, komai nasa ya kwance idanunsa sun kankance sunyi ja, alamun ya shiga rudani, tun yana mata surutai tana amsa masa har ta kasa gane me yake fada, tanaji tana gani ya soma kokarin yadda zaiyi ya rabata da rigar jikinta, abin ya gagara saboda rigar ta matseta, ana haka sukaji ana kwankwasa kofar falonta, ita kadai ce ta jiyi kwankwasa kofar falonta, shi kam ya riga yayi nisa ta rada masa a kunne, Ya Ishaq ana kwankwasa kofa kila aunty safeena ce, ya ja wani dogon tsaki ya sake makaleta ya cusa fuskarsa a kirjinta yana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya, har sai da ya dan ji nutsuwa sannan yace taje ta bude kofar. Ta tashi jikinta a kasalance ta lalubi dan kwalinta ta tattara gashinta da ya hargitse ta tura cikin dankwalinta ta daura sannan ta je ta bude kofar. Safeena ta gani a bakin kofar ta bata hanua tace, shigo mana aunty, tace no dama na zo inga jikinki ne, da alamu ma kinji sauki. Idanun safeena karaf! Ya kai bisa silifas din Ishaq na fata zube a falon, ta dubi Aneesa tace Captain ya shigo ne? Gaban aneeesa sai ya da ya buga tas! Tas!! Tamakr wadda aka kama kwarto tace, eh yanzun ya shigo yana ciki tace ok yayi dai2. Sai kawai ta huya ta koma abinta, aneesa kam tsayawa tayi anan cike da zullumi da kyar ta ja kafa ta koma dakin. Ta iske Ishaq kwance bisa gadonta ya shige bargonta, ta zauna a gefen ta zuba uban tagumi, ya dan bude idonsa ya kalleta yace, ya akayi ne? Naga kinyi tagumi, tace ba komai Aunty ce ta zo duba jikina tana nemanka. Yayi murmushi yace shine kika zuba tagumi kamar aan ga mijin da banaki ba adakinki? Oya zo ki hau nan ki kwanta muyi bacci yau ko ofis ban zuwa jinyarki zanyi. Ya nuna mata yalwataccen kirjinsa wai ta kwanta, tayi shi a zaune ta kasa motsawa, ya dubeta yaga ta narkar da idanu tamkar zatayi kuka yayi dariya tare da yaye bargon da ya rufe yace, bari inje kiran auntyn naki yi hkr kada kiyi kuka dan nasan halinki. Ya mike ya shafi gfen fuskarta ya fice, ta bishi da kallon so da kauna tare da wani irin matsanancin begensa, ita kam sam idan suna tare da bata kaunar su rabu, amma ya zatayi tunda ta auri mijin da ba nata ba, ita kadai MIJIN ARO inji matarsa, kuma zahiri haka ne tunda gashi ma ya shalleka ya barta ya tafi gurin matarsa, kai lallai duk wanda ya auri mijin wata tabbas bai more rayuwar aure ba, don haka baka da wata sakewa. Yana zuwa dakinsa yaga bai ganta ba, hakan ya tabbatar masa tayi fushi kenan, don yaje dakin Aneesa, ikon Allah shi da matarsa babu halin ya rabeta sai jidali ya tashi. Ya kada kai yanufi dakinta ya iske tana sanyawa yara uniform ko kallo bai isheta ba ta cigaba da abinda takeyi, shima sai ya dauki uniform din yana taya su, yana yi yana wasa da yaran har aka gama shiryasu, direbansu yayi horn kowa ya suri lunch box dinsa suka sumbaci Ishaq da safeena haka sukeyi duk tyn din da zasu sch suka fice. Ishaq yana ganin fitarsu ya janyo jikinsa yana cewa, come on ma baby, me ya faru early in d mornin kike fushi? Ta galla masa harara tace pls kada ka ka kirana bbynka ka tashi ka koma inda bbynka take bani ba, tunda har ka gaama yayina. Nayi nada ina tsoron ranar da za'a wayi gari ka karkace zuwa gurin yarinyar can ashe ranar na kusa, duk abinda kakeyi ina kallonka fah, jiya cikin dare na dubaka baka makwancinmu, kuma baka toilet hakan ya tabbatar min gurinta kaje, wannan bai isheka ba yanzu ma kana dawowa masallaci ka je can ma ka tare, me kake son ka nuna min? Kada ka manta ni safeena ba irin matan nan nan bane za'ayi wa rawa kai don ayi sabon aure, in haka zaka bullo to nima zanyi maganin abin. Ya kamo ta ya soma lallashi, haba my Queen me zanyi na rawar kai, ina abin yake, yanzu don Allah me yarinyar can ta fiki da har zanyi rawar kai akanta, in banda albarkacin bata da lfy kuma bata da kowa, kema kinsan babu abinda zai kai kafata dakinta, ko kin taba ganin naje inda take? Don Allah ki kwantar da hankalinki babu mace da zata zarta ki a zuciyata balle har ta iya kwace miki ni, wane ita babu mai iya jimirin daukar dawainiyata sai ke. (Kunji kadan daga halin maza ko?) Haka yayi ta lallashinta da nuna mata babu tamkarta a gurinsa. A wannan ranar dukkansu suna gurin aaiki yayarsa Hannatu ta zo tamkat daga sama Aneesa taga zuwanta saboda tsananin murna taga na gida idon sani bata san tym din da tayi tsallen murna ta rungumeta ba tana murna ta manta sam yar mijinta ce. Ta jata dakinta tana tambayarta diyarta kuma kawarta sadiya, tace tana gida da tare zamuzo, nima mun kawo diyar aminiyata ne da aka yiwa aure zan ma baki adress dinta ita ma nabata na nan gidan sai kuyi zumunci tunda Allah ya hadaku gari daya. Aneesa ta tashi take kicin ta hado mata abinci da abin sha ta kawo mata suka zauna suna ta hirar bayan saduwa, Yaya hannatu tace da banyi niyyar biyowa nan ba hajiya ta matsa wai sai na zo gani mata ke ita dai har yanzun hakalinta bai kwantaba da zamanki agidannan, amma idan tayi miki waya sai ki fadan mata komi lfy, baki da matsala bacin alhalin tasann ba zaki rasa matsalar ba boye mata kawai kikeyi, ni kaina gashi nazo naga duk kin rame, wlh da ganinki wani abu na damunki. Aneesa yai murmushi kawai tace, wlh kwana2 ciwo nayi kika ga na rame har asibiti sai da ya kaini amma sun ban magani. Jin haka yasa Hannu washe baki kilan an sami rabo ne tace, ayya ai babu wanda yasan baki da lfy ko hajiya bai gaywa ba tabbas da kingata tazo dubaki. Allah ya tabbatar mana da alkhairi, kice zanjewa Hajiya da albishir zata sami sabon miji. 72) Aneesa ta sunkuyar da kai cike da kunya tace, Allah bani da komai ciwo ne kurum ki kyale Hajiya kada ki tado ta tana fama da nata jikin. Nima yace idan ya dawo tafiyar da zaiyi zamu zo. Ita dai yaya Hannatu ji Aneesa kawai tayi, amma bata yarda da zancen wai bata da ciki ba, ga alamu nan ya nuna a jinta tayi fari tas! Jikinta yayi lukwi2 fatarta sai fdda annuri takeyi. Ta manta yanzu aneesa cikin hutu da sanyi Ac take dole ne komanta ya canza, don ba ta sami kwanciyar hankali da kulawar miji ba ki da ba za su gane ta ba. Ishaq ya dawo saboda Aneesa tayi masa waya, ta gaya masa zuwan yayarsa, ya zo suka gaisa sannan ya koma ofis, ita kuwa gimbiyar tasa da ta tashi nata gurin aikin kauyen birnin gwari suka wuce ita da aminiyarta saboda cewarta taga Ishaq ya soma rawar kai tana tsoron kada yarinyar nan mai shagwabar tsiya ta sace mata zuciyarsa, gara tun wuri ta dau mataki. Boka yaxe ke me kika fahimta tsakaninsu, duk da dai munyi yadda kwanciyar aure ba zata taba ratsa tsakaninsu ba, amma ga alamu ya zaku da lamarin yarinyar kuma ina da shawarar matakin da zamu dauka yanzu. Tace ko meye matakin na yarda ka dauka. Ya dauko wasu kullin magani guda2 ya bata fari da baki yace, kinga farin maganin nan ta yadda za'ayi yai ki kwaba shi da miyan bakinki ki tura a gabansa, zai narke ki tabbbatar da mijinki ya sadu dake a washe garin, da kuma wannan bakin zaki zuba shi a abun sha ki tabbata ita kishiyar taki kin bata tasa. To kuwa muddin ta sha wannan shikenan kun banbanta zta zama kamar ruwa ke kuma za ki zama tamkar zuma a gurinki mijinki, ko kin taba ganin an hada dandanon zuma da na ruwa sun daidaita? Ta girgiza kai ya saki dariya yace, to da zarar ya sadu da ita sai jita salam, daga ranan ba zai sake marmarin ba amma idan akayi yadda ba zai sadu da ita ba kwata2 shi da danginsa zasu gano dasa hannunki, amma yanzu babu mai gane ki shi kuma ba iya fadi zaiyi ba, koma ya fadi za'a dauka halilltarta ce haka suyi ta dibga mata hakukuwa don tayi ni'aima to ko gidan er skkoton da er nijar zata tare su gare ni'imarta bazata dawo ba. 73) Kuma ko ta dawo kinyi mata fintinkau saboda wanna da zaki turara a gabanki, ba ma ita ba ko yana neman mata bazai taba jin mace mai ni'ima irinki ba, dole duk inda ya tado da tsiminsa sai ya nemki. Ita da aminyarta sukayi murmushin nasa suka aje masa rafae dubu ashin sukayi godiya suka baro kungurmin dajin cike da farin ciki. Sai gab da magriba safeena ta iso gida batare da zullimn komai ba dama ta riga ta sharawa maigidanta karyar idan ta tashi ofis zasuje sunan abokiyar aikinsu data haihu. A falo ta iske Aneesa da Yaya hannatu wadda ta so wucewa zaria ya hana yace sai ta kwana. Da murnarta irin ta en bariki ta tari hannunta suka gaisa tare da taba hira sannan ta wuce dakinta, ranar dai kusan sha biyun dare suka kai a falon nan har da ishaq ana hira sannan kowa ya nufi makwancinsa, da kyar ya hannatu ta yarda zata kwana dakin aneesa don da tace ita a dakin baki ko yara zata kwana. Sunyi shirin kwanciya ne ta dubi Aneesa tace, kinga ni ki bar jin kunyata In kinsan yau ke kike da girki to ki kama hanya ki tafi gurin mijinki. Ni bana son sshiga rayuwar mutane babu ruwana ko ni kika zo kwana gidana zan barki in tafi, Aneesa tayi sunkwi da kai tana dan murmushi tace Allah bani bace da girki. Tace, hum! Yarinya ni fa na lura da wasu abubuwa a gidan nan, amma ba komai muna na kai kukan mu gurin Allah zai magance mana. a wannan daren safeena tayi amfani da kullin maganin