← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 51

Sashe 26

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dakin baccin Hajiyan. Ilai kuma a kwance ya sameta da littafin addu'o'in DU'A'UL MUSTAJABA amma tayi rigingine ta kifa shi a fuskar ta alamun baccin ta fara yi. Ya sa hannu ya cire littafin daga fuskar ta suka hada idanu, nata sun so mayin ja irin na mai bacci yace, har kin soma bacci ko ki zo ki tayani shirin kayana, to ni zan tafi ne. Tayi saurin tashi tace zaka tafi da safe haka? Na sha sai anyi sallar azhar? Yace zan tsaya yin wani abu a kaduna shi ya sa ki kula min da kanki Insha Allahu juma'a ko asabar zan dawo idan an sami gidanki sai mu wuce. Ta so muje ki rakani, yana mikar da ita sai hawaye shar2, ya ja ta jikinsa ya kwantar ya soma shafar gadon bayanta yace, meye na kuka kamar nace ba zan dawo ba, kullum dai sai kinyi mini asarar hawaye? Kiyi hkr da na dawo zamu wuce gidanmu mu kasance mu biyu muyi rayuwa mai dadi ko bakya so? Lamo tayi ajikinsa kwarai wannanrayuwar mai dadi tattare da tsantsar kulawa ya soma koya mata jiya zuwa yau, ita take wa kuka shikenan idan ya tafi zata shiga kadaici da kewa. Ita kam, gani takeyi yana bala'in kaunarta yana kulawa da duk lamarinta ashe da ba komai yake mata ba, sanadin aure gashi ta soma ganin kauna da kulawa fiye da na baya, ashe ayre haka yake da ni'imomi masu sa nishadi. In dai rayuwar aurensu ta dore a haka to tana ganin tafi kowa sa'a, sai dai bata da tabbacin dorewat hakan dan akwai manyan mata agabanta, amma duk da haka idan ta sami tata damar zayi zaman dirshan, Allah dai ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba zaiyi birgima son ransa. Ya ciro rafar en dari2 na dubu goma ya bata yace, ga wannan ki rike kafin na dawo ki duba wayarki na turo miki kudi, ko ban kiraki ba, ki kirani kinji babyna. Ya sumbaci kumatunta tabi ta rintse idanu, ita kam ta kosa ya kyaleta haka so yake ya tafi ya barta da kasala da kewarsa. Hajiya rafa en dari5 ya bata itama ya tura mata nata katin awaya. Aneesa dai na biye da sawunsa ji take kamar ta janyo shi ta rungume ta hana shi tafiya. Amma ina babu hali wata matar na can na jiransa, ga kuma aikinsa wanda ko nan da can ba sa so ya matsa saboda dinbin basira da hikimarsa. Aneesa ta yane jikinta da gyale suka karasa suka rakashi har jikin motarsa sai da ya tafi sannan suka dawo cikin gida, ita kanta Hajiya ji take tamkar kada ya tafi. Idanunta cike suke taf da kwalla, shi ya sa suna shigowa falo bata bari Hajiya taga fuskarta ba tayi saurin wucewa daki ta haye gado taci gaba da zubar da kwalla. Ita kam, da ta san haka zai kasance mata da tun farko bata soma sakin masa jikinta ba, gashi nan ya tafi ya barta da kewa. Gaskiyya Ishaq karshe ne gurin iya tarairayar mace ga komai nasa na da tsayawa a rai, kalamansa dabi'unsa da mu'amularsa, dole matarsa tayi kishinsa dan ya iya gudanar da komai yadda ba zakaji ya gundureka ba. Allah ya sota bata mallaka masa kanta ba da bata san yadda zatayi ba don bata san irin darasin da zai koya mata a nan fannin ba. Da kyar ta fito cin abinci bayan sallar azhar. 26) Tunda ya isa gida Abuja safeena ke tarairayar sa tamkar zata maida shi ciki. Shi kansa abin mamaki ya dinga bashi ganin da fushi suka rabu kuma ko a yau da sukayi waya haushinsa takeji, ba don komai ba sai don ya kai monday a zaria, ita gani take amarci ne yayi masa dadi har ya wuce ka'idar dawowarsa, bata san da Hajiya ta bashi damar amarcin da ba ta ganshi ya dawo a satin ba, saboda zai tsaya ne yayi amarcinsa mai tushe, kila ma sai Hajiya ta kore shi, tunda ya lura maryarsa tasa ba zai sha wuyar shawo kan abarsa ba, saboda komai na rayuwarta da sauki take daukarsa kuma cikin tsarin addini take yinsa. A wannan dare da safeena ta sha alwashi, sai da ta zautar da ishaq ta jiyar da shi ni'imar da bai taba ji ba ta hanyar surkullen da aka hada mata sai da ta mantar da shi duk wata diya mace da ke doron kasa don kuwa uwarsa ya so ya manta da ita, tunda da safe ya tashi ji yayi duk duniya babu kowa gabansa sai safeena, bayan tunanin zai iya farantawa kowa rai a duniya fiye da ita, ji yake tamkar ma ita ke kan ragamar rayuwarsa. Ya manta zaria sai dai idan wani daga can ne yayo masa waya yake tunowa ashe fa can mahaifarsa har yake tuno Hajiya da Aneesa. Sai dai ko ya tuno su baya jin kewarsu balle har yayi tunanin zaije ya gansu, sam babu wannan a ransa. Ita kam safeena duniya sabuwa miji ya zama mallakinta ita kadai, shi yasa take juyashi ta yadda ranta yaso, in dai yana gida to ba ya sabwa umarnin ta, ba ya da wani karsashi sai idan ya fita waje, amma da ya dawo gida ya zama mijin kan tace...... Sati daya na biyu ya wuce na uku suka wuce har aka soma kirga wata na daya na biyu zuwa na uku, babi Ishaq a zaria babu dalilinsa, tun hajiya da aneesa na kiransa da sauran en uwa yana ce musu gashi nan zuwa har aka hkr aka zubawa sarautar Allah idanu, aka dukufa rokon Allah ba dare ba rana. Aneesa tun tana boye kanta tayi kuka har hajiya ta gani halin damuwar da take ciki, saboda kallo. Daya zakayi mata ka gani tana cikin damuwa. Sai ya kasance duk tayi bankwana da wani farin ciki kullum tana daki akwance, idan Hajiya ta matsa mata sai ta fito falo to zata fito amma ba zata saka baki adukkan hirar da akeyi ba, tun Hajiya na lallashinta har ta koma fada dai daga baya ta koma mata nasiha. Ranar juma'a da hantsi tana zaune a falon Hajiya tana gyara kumbarta ne aisha kanwarta ta zo, sukan shigo tym 2 tym su gaisheta amma ba kullum ba, en kanana ma ko ba su zo zata aika su zo. Suna hira ne take tambayar Abbansu, sai Aysha ta gaya mata yau kwana biyu bai da lafiya ki gurin aiki baya zuwa. Aneesa tace, amma shine ba ki zo kin gaya min ba, ina garin nan baki ga hanci, ashe da wani garin nake ba za'a gaya mini ba. Aysha tace wlh tun jiya na so in shigo in gaya miki shi yace kada na gaya miki baya son kina fitowa tun da mijinki baya nan, yanxu ma da kyar ya yarda na zo na gaya miki yace wai ba sai kinzo ba ya yafe miki. Hajiya na shigowa falin Aneesa ta gaya mata, ita ma fada ta dinga yi daga karshe tace Aneesa ta tashi taje ta gaishe shi, ita ma tana nan shigowa anjima. Wannan shine zuwan Aneesa na farko gidansu tun bayana watannin uku da aurenta. Ta sake Hijab ta ba aysha Ledan da Hajiya ta zuba juice kala2 a ciki ta rike mata suka tafi. Ta shiga ta gaida Abbansu yana dakinsa, jikinma da sauki har suka danyi hira da shi akan ciwon, ya nuna mata magungunan da aka bashi a asibiti, da na gargajiya da aka masa yake sha, typhoid ce ke damunsa..... 28) Da zata tafi ta shiga dakin Baseera sukayi sallama ba yabo ba fallasa yadda tayi mata. Ta shiga sasansu Halima ko wacce na dakinta sun en share2. Dakin hanne ta fara shiga kamar abin arzikik suka gaisa, sai tace mata, oh tafiya Abuja dai bata yiwu ba? Tace, uhm! Ta sake cewa to daman zaman Abuja ai ba nayaku bayi bane, manyan mata ne en gaban goshi masu fada wa maza magana ta zauna darama! Irin wannan aure ai kanaji kana gani miji zaiyi maka fintinkau masu iya rikeshi su rike abinsu, ita ma Hajiyan ai gashi nan ta jawo wa kanta, da danta na zuwa ganinta amma yanzu yayi mata kanshi dan goma, anyi ba ayi ba, Allah dai ya kyauta ke kam, sai zaman hkr. Aneesa da taji ba zata iya kin wannan cin mutuncin ba sai kawai ta tashi ta shiga dakin Halima. Ganin yanayin fuskarta kawai ya sa Halima ta gane anyi mata halin da aka saba na zubar da girma, da nuna kiyayya. Lallashi da nasiha tayi ta mata tare da nuna mata cewa ta tsayu da addu'a domin babu abinda ya gagari Allah, taci gaba da yiwa mijinta addu'a, balle ma Allah yaba gaggawar amsa addu'a da akayi wa ba batare da saninsa ba. A ranar tunda Aneesa ta dawo gida sai tunaninta ya dada zurfafa, lallai ta yarda Abuja ba garin irin su bane na yaku bayi, to amma ai aure ya kaita matsayin da bata zata ba, tunda ba'ayi mata shamaki da mijinta ba da yanzun tana can suna more rayuwarsu, irin yadda ya fara gwada mata. Zazzabi ne mai zafe ya rufeta sai rawar sanyi takeyi, Hajiya duk hankalinta ya tashi, ta dauko panadol ta bata tashi ba ta dade ba da sha ba sai ta soma ami tun tanayida karfinta har ta zamo bata da karfi. Hajiya duk sai ta rude ta tasa ta gaba da tambayoyi don tana ganin anya ba ciki ya likawa yarinyar nan ya tafi ya barta ba, kila ma ashine ya sata bi tsangwami kanta take damuwa. Ta dan matsa dag da ita bayan aman ya lafa mata tace, Aneesa kin ganin al'adarki kuwa? Tace ina gani ko watan da ya wuce ma ai nayi. Tace eh zai yiwu ki dinga gani, tunda wasu suna da ciki suna al'ada, anya ba ciki gare ki ba? 29) Nifa binbinin da yaron nan ya dinga miki kafin ya tafi abin yayi ywa, dama nasan abin da yayi niyyar shukawa kenan. Aneesa tayi saurin dago idanunta tana duban Hajiya tace, wlh bani da ciki, ni ban yarda komai ya shiga tsakani na dashi ba har ya tafi. Hajiya tace to tashi ki gyara jikinki muje asibiti a dubaki. Nasan
Chapter 26 · 0% Book details