← Book details Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 51

Sashe 12

Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan murmushi tana latsa hannunta daya daya kumbura tace, babu abinda da ke damuna. Kawai Allah ne ya aiko min da wannan larurar. Ina nan ina addu'a kuma ku tayani. Ya tsurawa kafafunta idanu sun kumbura sintim sai sheki sukeyi. Ya numfasa yace, kafafun nan babu maganin da zasu sabesu? Haka ya zauna yana ta yiwa Mama magana ta kwantar da zuciya. Duk da ta boye masa damuwarta amma ai ya riga yasan komai, yasan irin zaman da sukeyi a gidan nan ita da yaranta, musamman Aneesa. Hajiya na gaya masa komai, kuma ya sha gayawa Maman duk wani abu idan ya taso na bukatarsu suje direct wurin Hajiya, kada su tambayi kowa, ita kuma Mama yau da gobe take dubwa shi ya sa wani tym din ko matsalar ta taso musu bata yarda Aneesa ta gayawa Hajiya, sai su hkr Allah ya kawo musu agaji. Da ishaq zai tafi ya bata dubu biyar, yace kuma idan wata bukata ta taso a gayawa Hajiya ko Aneesa ta gaya masa ta waya, ita ma Aneesa dubu 2 ya bata yace ta sayi kayan kwaliyya. A zuciyarta tayi dariya tace wai shi kullum ya bani kudi sai yace in sayi kayan kwaliyya, ko kuma so yake yaga tana kwaliyyar. Cikin Mama ya shiga watan haihuwa shiyasa, Aneesa ko makaranta ba kullum take zuwa ba, duk ranar da maman ta wayi gari ba karsashi. To bata zuwa, sai tayi zamanta tana lura da mamanta. 55) Ranar litinin Maman ta shirya ta tafi awo da yake asibitin kudi ne take xuwa, kuma babbar nurse din asibitin gidanta ba nisa tsakanin su da gidansu Mama, kuma tana da kirki har suna abin arziki da su Mama, yawanci ma idan Mama ta shirya da wuri tana aikowa mama ta zo tabi ta a motarta, su tafi asibitin. Yau ma mama na zuwa ta ganta waje jikin motarta tana jiran ta, suka yiwa juna murmushi. Ita ta soma gaida Mama. Maman jafar ina kwana? Ya jikin naki? Ta amsa da sauki, amman yau da ciwon mara na tashi kadan2, tace Allah ya sauwake bari mu karasa asibitin sai a duba ki, ina ganin ma haihuwa ce tunda EDD dinki har ya wuce, kila yau rike ki zamuyi. Tayi musrmushi tace, Allah yasa haihuwarce nima in huta, saboda yadda nake jin nauyin cikin nan kamar an dora min dutse, in bacin kunyi hoton kunce min daya ne, sai in ce ni nauyin mutum 2 nake ji. Allah dai ya raba ni da shi lfy, nurse din tace ameen maman jafar. A asibiti anyi wa mama awo suka ce insha Allahu zuwa gobe zata haihu. Amma idan ta kai gobe bata haihuwa ba, to da safe tayo shirin haihuwa ta zo asibitin. Su ka gaya mata adadin kudin da zata zo da shi. Da ta dawo gida, can sasan su Hanne ta shiga ta gaya ma Hanne yadda sukayi a asibitin. Amma ta iske Halima anyo mata waya kanwar babansu ba lfy ba lfy sosai acan kauyen sun tafi, kila gobe su dawo. Hanne tace idan Allah ya kaimu goben ba sai ku tafi da Aneesa ba, nu kuma ma biyo baya idan kin haihu. Dama maman ta gaya mata ne, ko zata ce zata rakata, tunda bata san ya haihuwar zata kasance ba, tabbas tasan da Halima na nan tare za su tafi ta rakata. Da abbansu aneesa ya dawo ta shiga dakinsa ta gaya masa, abinda akace a asibitin, sai ya kama fada, ni bani da kudi ahannuna yanzun da zan baki gobe kije asibiti, in banda janyowa mutum jidali, ya za'ayi haihiwa bata zo ba, suce aje asibiti. Ko ko su da kansu ne zasu janyo haihuwar da su sa mutum kashe kudi, to ni bani da su, sai na sama tym na amsa abank. 56) Mama ta sassauta murya tace ba wai kirkiro mini haihuwar za suyi ba, yau daman na gaya maka na tashi da ciwon mara shine, sukace haihuwa ce amma sai zuwa gobe, abinda yasa suka fi son in haihu a asibiti saboda sunce har yanzun kan yaron bai juyo kasa ba, akwai hadari. Ina fatan Allah ya kawo mini komai cikin sauki, ta mike da kyar ta bar masa dakin. Da daddare duk yaranta suna falonta. Suna kallo sun saka film din the message, ta tashi tsam daga cikin yaran ta shige dakinta ta kwanta. Ba barci zatayi ba, haka kurum ta ji tafi son zaman kadaici saboda hayaniyasu ta dameta. Aneesa da taji ta shiru a dakin sai ta biyo ta cikin dakin, ta zauna agefen gadon da Maman take, tace mama har kin kwanta ne? Tace Hayaniyar ce bana so shine, nazo na kwanta idona ma sam ba barci. Aneesa ta lura maman kamar tana cikin tsananin damuwa, saboda zahiririn abinda fuskarta ya bayyanar kenan. Tace mama hala zuwa asibitin goben ne ya dameki kike son saka zuciyarki cikin tunani. Tayi murmushinta da ta saba tace. Babu ko daya, saboda nasan duk abinda Allah ya hkunta shine zai faru akaina. Ni rayuwarku ke da en kannenki kawai nake dubawa nan gaba sai inga tamkar, abbanku watarana zai ce ya ga za daukar dawainyarku. Aneesa tace, idan zaice ya gaza mama ba gaki ba, mu ko da ke kadai zamu iya rayuwa, idan yace shi ya gaza damu, ba ga shi kina er sana'ar zannuwa ba, kuma ba laifi kina dan samu, a ciki Allah zai dunga taimakonki kina rufa mana asiri wata rana sai labari. Ta sake yi murmushin tace hmmm! Karama kenan, tunani na kada wata rana a wayi garo ni in riga Abbanku mutuwa, ina nan ma ya ki yi muku abinda ya wajaba akansa ina ga bana nan. Tace don Allah ki bar fadin haka, muna nan da ke sai kin aurar da mu har yaron dake cikinki. Sai kinga 'ya'yansa, tace Allah yasa inga yaran naku. 57) Kinga kece Babba ki hada kanku, duk da Aysha butsararra ce nasan nan gaba zata yi hankali tasan ina ke mata ciwo, yanzun yarinta ce kawai ke kwasarta. Tace, yanzun mama goben ya zakiyi da kudin zuwa asibitin? Tunda Abbanmu yace baya da shi, tace Allah zai rufa aisiri ina ganin kiyi sammakon zuwa wurin Malama Maimuna ki gaya mata uzurin da ke gabana, sai ta juya min kafin ta hada kudin zunnuwan wannan wata sai ta cire a ciki. Anees atace, yauwa hakan za'ayi da har na soma tunanin gaya wa Hajiya, tunda Ya Ishaq yace idan matsala ta taso agaya mata ko ayi masa waya$ tace gaskiyya ba za a gaya mata ba, dawainiyar da takeyi ita da danta tayi yawa, sai kace sune masu alhakin larurar mu, haba ido ba mudu ba ne, amma yasan kima. Aneesa da mamanta sun kai fiye da karfe daya na dare suna hira da tattauna al'amuran rayuwar yau da gobe. Maman na jefo mata en nasihohi cikin hirar. Da ta fahimci Aneesa barci yayi awon gaba da ita sai ta tashi tayi alwala ta soma sallar nafila, da ta idan ta cigaba da adduointa, har sai da tayi raka'atul fajr da sallar subahi sannan ta bar abin sallar. Tabi duka yaran ta tashe su dan suma suyi. Aneesa tana idarwa ta fita ta hura wutar itace tasa wa maman ruwan wanka kansancewar babu wutar nepa. Bayan tayi wanka ta shirya tsaf! Sannan ta taka a hankali tayi sallama dakin Abbansu Aneesa, ya amsa mata, sai da ta nemi izinin shiga sannan ta shiga, suna zaune shi da Basira ta hada musu tea mai kauri ga bread a gefe suna sha, ita kuwa can da yaranta ya barsu da koko, idan ma tea za su ha sai dai su sha ruwan bunu, saboda ba zai ba su madara ba ba kuma gata nan ta ruwa da ta gari a dakinsa. Kai duniya ina zaki da mu? Lahira akwai aiki a gaban marasa shuka gskiyya. Haka ta fada a zuciyarta. 58) Hannun kujerar da ke gefenta ta zauna, sanna ta gaisheshi, da taga Basira bata da niyyar tanka mata sai ta soma gaisheta, sannan ta tanka mata. Mama ta dubi maigidan tace, ni nayi shiri zan tafi asibitin, don kuwa har yanzu ina jin ciwon marar, da wa zamu tafi? Ya wani dubeta yace, da wa zaku tafi da ya wuce Aneesa tunda naga ita ta hannun damanki, jiya wajen sha dayan dare na leko dakin na jiku kuna, kulle a uwar daki kuna shawarwari ke baki da abokin shawara sai Aneesa, idan tayi aure sai ki koma kiyi da aysha. Tayi murmushi tace, ko aure bai raba mu ba, mutuwa ma zata iya raba mu. Ta mike tsam, dama ta dauka zai ce Basira ta rakata ne, amma tunda ya fad haka ko insha Allahu da Aneesan zata je, don ko menene ya sameta itace zata fi tausaya mata. Tana shiga daki ta tarar da aneesa har dama musu koko, ta zuba na Mana a babban kofi tana juyawa da ludayi don ya huce. Aneesa tace mama ke da wa zakuje asibitin? Tace da ke ya ce zamuje. Tace da ni kuma mama? Ni ce zan rakaki haihuwa? To haka yace na dauka zai ce muje da Basira, shine na tambya shi, amma tunda haka ne ra'aryinsa sai muje da ke din, babu komi Allah yana tare damu. Aneesa cike da damuwa ko tace. Sai mu tafi din amma ko in gayawa Hajiya ne, ko inyi waya tudun wada. Tace ki kyale kowa bana son gaya musu hankalinsu ya tashi, musamman Umma tunda ita ba zuwa zatayi ba, sai dai ta turo wani ya zo, kinga sai abarta cikin tunani, gara dai idan Allah ya saukeni lfy sai agaya musu hakan yafi dadi. Ta mikawa Mama kokon tace, ya soma hucewa gara kisha, ni bari inyi sauri in yi wanka mu tafi. Mama ta amshi kokon tana kurba a hankali sam bata jin dadin bakinta sha dai kawai takeyi don kada ta zauna cikin ba komai. Da za su tafi ta leka dakinsa shima yana kokarin fitowa ne zaije gurin aiki, tace masa zamu tafi Allah ya hada fuskokinmu da alheri, idan nayi maka wani ka yafe ni, kasan haihuwa siradin mutuwa ce ban sani ba ko zan tsallake. 60) Tace eh bata haihu ba, amma muna iyakn kokarinmu mu
Chapter 12 · 0% Book details