Sashe 15
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amma yanzu ai da kunya ko? Yace meye abin kunya kefa 'yar gida ce a gidan mu tamkar su Haula, yanzu dai mu karasa ki gauda su Hajiya sai in kaiki a hala ta. Ta tsuntsire da dariya tace, au ashe kayi hala ban sani ba, daga mashin ashe mun koma hala. Yace lah? Baki san mashin din shine hala ta ba, ai wannan mashin dinmu shine halar samari. Ta sake dariya tace, kai sagir baka da dama. Gaskiyya ka rakani hanya kawai in hau mashin da ba son Aunty Basira ta aiko ni gurinta ba ta nan bane na tsaya jiranta da baka ganni ba. Yace, rabon zamu hadun ne ya sa hakan ta faru. Amma fa babu yadda za'ayi ina kallo ki hau bayan wani kato ya goya min ke alhalin gani kuma ina da mashin din nan. Don Allah zo muje da yanzun kin gaishesu ma munfito. Haka nan dai ya tilasta mata suka shiga gidansu. Da yake iyayensa masu mutnci ne suka dinga haba2 da ita. Ita kam, a darare ta dofana ta zauna, en matan gida ne suka gaisheta a wulankce, suna wani jin kai, ita dai duk ta kosa su bar gidan. Tana ji yana gaya musu, shima yanzun ya ganta an aikota gidan Alh. Isa tana tsaye tana jiran mashin shine ya cqQWe gara shi ya goyata a nashi mashin ya kaita gidan da wani kato ya dauketa, ko ba haka ba Hajiya? Yake tambyar mamansu Hanne, er tsohuwa tace, haka nan ne dana kana da gaskiyya. Suka yi ta dariya... 71) Sun fito daidai barandar gidan kenan. Sukaji hon din mita zata shigo, ya dubeta yace, ga alhajinmu nan ya dawo shima sai ku gaisa. Ta dafe kirji tace, gaskiyya ba zan iya ba kunyarsa nake ji sosai, don Allah ina zan boye idan ya shiga cikin gidan sai in wuce, ya janyo gefen hijb dinta yace, yace zo ki boye anan ai yanzun zai shige sai mu tafi. Da sauri ta bi bayansa ya tura kofar wani daki anan harabar gidan ta shiga, ta nemi gefen gado ta dan zauna a tsorace, sai ya da ya fita ne ta karewa dakin kallo ashe dakin sagir ne, sai ta tsorace, ita kam gara ma da ta tsaya ta gaida Alhajin ne da ya fiye mata, gashi sagir ya kutso ta dakinsa, kada kannensa suzo su ganta suce dama gurinsa ta zo ta fake da cewa an aiko ne gidan Alh. Isa. Alhajinsu na shigowa yayi fakin din motarsa. Sagir ya matsa ya gaishe shi ya amsa, yace sadiq ya dawo ne kuwa? Yace a'a bai dawo ba. Yace, ok to zo ka rakani nan gidan Mal. Ado ance bai jin dadi mu gaisheshi. Sagir ya dan kalli dakinsa yace to alh. Bari in dauko waya ta a daki. Ya shigo ya sami Aneesa a tsaye duk ta tsorace yace, bari in dan raka Alhaji dubiyar wani makocinmu ga gidan nan kusa yanzu zamu dawo. Tace sagir bari kawai in tafi kaga dare yayi Abbanmu ya dawo kada in jawa kaina laifi. Yace wlh ba dadewa zamuyi ba yi hkr. Ya fito ya ja kofar, Alh. yace ka rufe da key kaga ba kowa yau aharabar gidan, ko ka manta ranar da aka kwashe muku kaya ne. Ya kulle kofar da mukullin suka fita, su ka ci karo da kaninsa Sadiq shi dakinsu daya da hanne, ya mika masa key din tare da yi masa rada a kunne Akwai matata a dakin ka taya ta hira kafin mu dawo yanzu. Allah Allah sadiq yake ya bude yaga wacece, idan ta bashi fuska ma ya dan rage ahanya a gurinta, tunda dai yasan duk en matan da suke kawowa nan, en hutu ne. Basa kawo mai mutunci. Musamman shi sadiq da ya maida mace tamkar riga yau idan ya saka wannan gobe wata zai saka. Shi kam sagir da wuya kaga mace ya kawo sai dai irin marasa mutuncin nan sun su biyo shi en asha minti..... MIJIN ARO 1 **11 72) Yana bude kofa ya ci karo da Aneesa tayi tsuru2 a tsaye. Yayi murmushi yace, au dama kece, meye abin tsoro ki saki jikin mana ke da dakin mijinki. Tace haba dakin miji ai ba'a daura aure ba, tsautsayi ne ma yanzu ya shigo da ni dakinsa don wlh bansan dakinsa bane. Sadiq yayi wata munafukar dariya yace, Tsautsayi! To ai dama akan sami irin wannan tsautsauyin, balle irinku da kiris ya rage. Sai ya canza zancen nasa zuwa wata siga, hakan ya sa tayi shiru. Ya nuna mata gefen gado yace, ki zauna mana ai yanzu zai dawo. Ta ki zama, ya mika hannu yace muga file din hannunki na menene? Tace na Abbanmu ne aka bani inbashi. Ya matsa wai a dole sai ya amsa ya gani, da taga so yake ya hada jikinsa da na ta sai ta sakar masa. A gaugauce sagir ya shigo dakin yace, don Allah amarya yi hkr, ta so muje in kaiki gida, ai bamu dade b. Ita dai da sauri ta mike suka fito tana ta tsoron kada wani ganta bayan ganin da sadiq yayi mata gashi har ya neman yi musu wata fassara. Tun a bakin titi Aneesa tace sagir ya sauketa. Ta karasa, shi kuma ya koma, sai yace sam, ba zai yiwu ba ya ajeta a bakin titi, to meye anfanin kawo ta din da yayi, ita kuma tsoro take ji kada agansu tare a dauka wani gurin suka je tare, tunda yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba. Allah ya taimaketa babu kowa a kofar gidan shi yasa yana tsayar da mashin din ta shiga gida da saurinta. Abinda take tsoro shi ne dai ya faru, saboda Abbansu ta gani atsakar gida da Basira suna tsaye, ya sakar mata harara yace, daga gidan ubanwa kike? Ta dubi Basira wadda ta dauke kanta tace, Aunty Basira ce ta aikeni... Yace yanxun daga inda aka akeki kike ko ya? 73 MA IS BLANK PAGE 74) Yace maza taje ta nemo masa file din sa, yanzun zai fita da shi office. Gidan Hajiya ta shiga tana ganinta tace lfy? Ina zaki da sassafe? Ta gayawa Hajiya abinda ya faru amma bata gaya mata gaskiyyar inda ta bar file din ba, saboda bata son Hajiya taji ta shiga dakin sagir don ba mutuncinta bane. Hajiya tace, ki tashi tunda yana jiranki, kiyi maza ki dauko masa, Allah yasa sun gani sun boye tunda kawar Basira ce, balle taji furucin da Abbanku yayi.... Aneesa ta miki tace, Hajiya dan bani wayarki in kirata inki, hajiya tace tana daki je ki dauka, bata fito ba a dakin ta kira numbar sagir ta tambaye shi ko yaga wani file da ta bari a akan stool din dakinsa, yace ya gani Amma ya dauka na sadiq ne, shi yanzu ya fita ta bari zai kawo mata gida. Tace, ai gani nan a hanya zanzo in amsa na abbanmu ne, yace yanzun zai fita da shi office. Yace to ki karasa gidan sadiq na nan. Ko kuma ki bari in kira shi sai ya kawo miki gida. Tayi saurin cewa ka barrshi kawai zanje in amsa. Allah ya taimaka harabar gidan babu kowa, dama tana tsoron kada wani dan gidan ya ganta, ta shiga 3. Abude din yake, tayi sallama ta shiga sadiq na zaune yana shafa mai da alama wanka ya fito, yana sanye da singlet da dogon wando. Ya dubeta yayi murmushi yace, daga ina haka? Na ganki a tsorace? Ya sagir din yayi sammakon fita gurin aiki, tace dama ba gurinsa na zo ba, file din nan na jiya da ka gani shi na manta na zo dauka, sagir yace ka bani. Yace file? Na dauka da shi kika fita? Ai kuwa ban ganshi ba, ta gintse fuska saboda ta lura yana son maida abin wasan yara, tace wlh anan na barshi shi sagir ma yace ya ganshi. Yace ok to dan zauna bari in sa riga sai ki tayani mu duba. Ta daure fuska sosai tace, gaskiyya ba zama na zo yi ba, daukan file kawai na zoyi Abbanmu na can na jirana, don Allah idan ka gani ka bani. Yace maida wukar na tsinta, idan na baki wani tukwici zaki bani? Taji sanyi aranta da yace ya gani, tace au sai na baka tukwici? To fadi nawa kake so? Yayi murmushi, ni ba kudi zaki bani ba, bari kiga tukwicin.... 75) Kawai sai taga ya ja kofar dakin yana juyowa taja da baya tace, sadiq me kake nufi da nine? Ni fa ba irin en iskan en matan nan da ka sani bane, in ma banda rashin mutunci irin naka, ka rasa wadda zaka yiwa irin wannan cin zarafin sai ni da muke shirin aure da danuwanka. Ai ko wani ka ga zaiyi min irin haka, a tunani na sai inda karfinka ya kare dole zaka kare min mutuncina, albarkacin danuwanka. Kaga bani file dina in fita a dakin nan. Ya murmusa, haba Aneesa shi dan uwan nawa ince jiya nan kika wuni gurinshi ya gama kwasar gararsa, to meye nima don zaki sammin ragowarsa. Hawaye ya gangaro a fuskarta tace, haka dan uwan naka ya gaya maka? To ni sagir a gurina mai mutunci ne tunda ko hannuna bai taba rikewa ba, balle mugun alkabain da kake ikiraran mun aikata. Ni kam! Na bar ka da Allah shi zaiyi mana hisabi da kai ranar gobe kiyama, yanzun ka bani file dina in tafi ko in yi maka ihu... Dariya ya kyalkyale da ita yace, kiyi ihu azo a ganki kin kawo kanki gurin maza, kinga jiya an ganki a gidan nan da sagir yau kuma kin kanki gurina, kinga sai ta tabbata jarabarki ta isa. Oya! Yi ihun ina jiranki. Ta soma kuka saboda tausayin kanta yau Allah ya hadata da macuci mara tsoron Allah kuma masharranci. Addu'a ta soma karantowa a ranta saboda Allah ya kareta daga sharrin da yake shirin kulla mata, wanda idan ya kulla mata shi bata da mai shaidarta sai Allah, tunda gata adakinsu, balle kuma idan zance yaje kunnen abbansu ta shiga uku, dama ya furta kalmar zargin wani abu tsakaninta da sagir, idan yaji haka kuma shi kenan zaice zarginsa ya zamo gaskiyya. Ta durkusa