Sashe 28
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
makoshinsa, ta juyo tana dubansa, ya rintse hannunta sosai acikin nasa yace, ya sunan wannan turaren da kikasa, tace bashi da suna. Yayi murmushi yace sunansa kenan bashi da suna. Ita ma murmushin tayi tace Allah ni bansan sunansa ba, ni dai Hajiya tasa musamman aka hado min shi a tudun wada. Wai amare akeyiwa da matan aure, wai en mata ba sa shi, ban dai san dalili ba. 34) Yayi murmushi, yace kinsn dalilin da yasa akce en mata basa sawa? Ta girgiza kai. Ya tada maotar suka fice daga gidan sai da suka hau titi sannan yace, in gaya miki dalilin? Tace gaya min mana idan ka sani. Yace wannan turaren duk wanda ya shaki kamshinsa, saboda dadinsa yana kashe wa mutum jiki ya tado sha'awa, sannan zakaji kana son akoda yaushe ka kasance da shi wannan ma'abocin sa wannan turaren, kinga idan mace zata sa sai tana tare da mijinta, idan wadda bata da miji ta sa akwai matsala kenan don fitina zata iya aukuwa ina ganin wannan ne dalilin. Amma yace ace turaren yana da suna ko? Tace Humra ne to amma wannan hadin ne na musamman sai en maiduguri ko dangoginsu, wanda ya jibance su, don ina jin akwai wasu sinadari ne da ake hada turaren da shi yasa dadin kamshinsa yayi yawa.( Duk mai bukatar turaren yana iya yin waya yaji inda zai samu). Sun iso kd cikin mintina da ba su wauce hamsin ba, kai tsaye suka wuce unguwar sarki nan ne gidan babban amininsa nasa yake shina usulinsa dan zaria ne amma a tudun wada. Dr. Bashir sunansa, likita ne a sibitin ido. Matarsa ma likitace a genera hospital 'y'yansu biyu mace da namiji. Gaskiya suna da kirki sun amshi aneesa hannu bibbiyu. Don acewarsu itace bakuwarsu shi Ishq dan gida ne. A yadda aneesa ta fahimta dama sun riga sun san da zuwansu. Kwarya2 liyafa aka shirya musu bayan sunci sun sha sunyi sallah, ne mzan suka dauke suka shiga cikin gari. 35) Gidaje 2 sukaje na wasu abokansu. Duk inda sukaje sai taji ana taya mijinta murna wai yayi dace mata er asali. Don suna falon gidan Dr. Bash taji Dr. Na yiwa Ishaq tsiya, gaskiyya Captain ka iya lalubo dangwalwa, wannan amarya taka ba makusa zaka dada danyancewa abinka. Suka tafa yace, ai da gani kaima kasan danya ce sosai, ni zan nunar da abina. Haka sukayi ta surutunsu na aminai ita dai barin falon tayi ta koma daki, saboda su suna barandar falon ne suna jiran su fito. Sun dawo gidan Dr. Bash anan yamma tayi musu lis! Har kusan magriba duk sai hankalin Aneesa ya tashi don bata son suyi tafiyar dare. Tayi masa flashin yasan mai take nufi amma sai yai kamar bai sani ba, can sai ta tura txt, don Allah ka bar hirar nan mu tafi dare fa yayi. Ko kwana zamuyi ne? Da gatse tafadi ko kwana zmuyi, kawai sai taga ya turo amsa, eh kwana zamuyi har an bamu masauki, kinyi min shiri ko? Gabanta ne ya fadi da taga sakonsa, duk ta rude har matar Dr. Ta tambayeta, naga duk kin damu ne kina ta duba agogo, inace kwana zakuyi? Tace, a'a yau zamu koma kuma naga yayi zamansa suna hira ga dare zaiyi. Tace idan ma dare yayi sai ku kwana, meye abin damuwa tare da kike da mijinki. Ita dai Aneesa shiru kawai tayi don ta riga ta gama tsurewa, kila ma plan dinsa kenan su kwna, ai kuwa zai sha fadan Hajiya. Waya yayo mata wai ya fito su tafi, suka fito musu rakiya, matar Dr. Ta hada mata kayan shafa masu tsada ta shake mata lede wasu kayan bacci masu kyau. Dr. Kuma dubu goma ya bata, banda sauran alkhairan da abokansa da matasnu skayi mata. Sun dauko hanya kenan taga yayi parkin a gefen hanya yayi kira wayarsa can suka soma magana da Hajiya yace, Hajiya kinga dare yayi mana ko? Tace ai da gangan ka bari dare yayi mukun, kun kusa isowako? Yace ina, ai gamu nan kd mun dauko hanya yanzu motar tayi mana lalata, shine zan shaida miki kada kiga munyi dare idan na samu motar ta gyaru zamu dawo komai dare, idan bata gyaru ba zamu kwana. 36) Tace to tun kafin dare yayi sosai ka sako min Aneesa amota ta dawo gida dan ban shirya kwananta a kd ba. Yace Hajiya ya za'ayi in sakata a motar haya ita kadai, ga dare yayi gara in bar motar mu biyo motar haya tare. Tace wa zaka barwa motar? Yace ba wanda zan barwa zan barta ga Allah ne kawai, gara in rasa motar da wani abu ya sami er mutane. Tace to na yarda ku kwana acan amma yanzu ka dauki Aneesa ka kaita gidan innarka binta ta kwana can da safe sai kaje ka dauketa ku dawo gida. Yace, ban fa je na gaisheta ba. Kawai sai yanzu ta ganmu ai zata san ba don ita muka zo garin ba. Ki hkr kawai mu koma can gidan abokina mu kwana. Tace ban yarda da naka tsarin ba, nawa nake son kabi kalas! Kawai sai ta kashe wayar, ya dubi Aneesa ita kuma ta fahimci me yake nufi plan ya shirya wa Hajiya kawai. Ita ma Hajiya ta gane shi. Bata ce masa komai ba, shima baice mata ba ya juya kan motar suka koma gidan Inna binta, kanwar Hajiya. Suna isa ta tare su da murna ita da 'ya'yanta sai nan2 suke da Aneesa. Aka kawo musu abinci da abin sha sannan take sa masa, da daren nan ba dai gida zaku ba yanzu? Yace eh gidan zamu motar ta fara bada matsala ne naga kawai gara mu kwana idan aka dubata sai mu wuce. Aneesa ta shiga yin sallah ne ya gayawa Hajiya binta abinda Hajiya tace, Inna binta tayi murmushi tace to in banda abin yaya meye nata na zaba wa diyar tata wajen kwana tun da tana tare da mijinta. Ta dube shi kaga dauki matarka ku tafi inda zaka kwana, ni bana takurawa yara wlh, yace ki barta kawai Inna da safen sai in zo in dauketa tunda haka Hajiyan take so. 37) Ta dauki wayarta ta kira Hjiya tana ganin ita ce tace, su Ishaq sun zo gidanki yanzu haka? Tace eh gasu nan Aneesa ma na sallah. Yaya me ya sa miji da matarsa zaki ce ya kawo ta guri na ta kwana, ki barshi ya tafi da abarsa can inda zai kwana ai ba haramun bane, ko don bata tare ba? Tace ni wannan ba matsala bace, haba binta yaron nan me ya maida mutane ne tun fa da aka daura auren nan ya shallake ya bar yarinyar nan wata3 kenan yaki ya nema mata gida ya dauketa su tafi, tunda er ikon tasa tace ba za'a kawo mata Aneesa gidanta ba, kamar gidan ubanta, to ya bar yarinyar nan nufinsa sai tym din ya nishadu ne zaizo ya dauketa ya kaita duk inda yaga dama su kwana? Wlh yana ganinta da ciki ba zan sake ganinsa a zaria ba, kila sai ta haihu shi ya sa ni kuma na hana shi duk wani yankuri da yakeyi na ganin cimma burinsa, ki barni da shi tunda matarsa tafi karfinsa yaje su karata da ita, ya zama mijin tace sha2 kawai. Tace kiyi hkr Yaya kinsan lamarin nasa akwai bukatar addu'a muna nan munayi komai yana da iyakarsa kiyi hkr. Tace hkr ai ya zamar mini dole, ni dai ki aje mini 'yata ta kwana gidanki, idan ya matsu da lamarinta to ya dauketa zuwa gidansa. Ta juyo gurin Ishaq tace je kayi sallah ka zo ka dauki matarka ku tafi. Yace ta yarda ne? Tace eh kyaleta mu mun isa mu ja da abin da Allah ya halasta ne, tashi kaje sauke farali. Ita dai Aneesa bata san wainar da ake toyawa ba, ita dai sun gama cin abinci Inna binta tace tashi su tafi da safe ta dawo, nauyin Inna Binta kawai takeji shi yasa ta bishi. Hotel din Durba ya kaisu ya kama daki, ita dai kurma kwai ta zama tuni ya bude dakin ya matsa mata ta zauna gefen gado, har yayi wankansa ya fito anan ya sameta. Ya dube tym din ya fito yana goge gashinsa da tawul yace, kije kiyi wanka ko haka zaki kwanta? Tace masa, eh! Yace ok bari inyi sallah ke kinyi ne? Tace banayi. Yayi murmushi yana mata duban mamaki yace ba kyayi? Naga kuma kamar a gidan Inna Binta kinje kinyi sallah? Tace Abinci kawai naci. Ya kada kai yace shikenan ni bari inyi. Ganin tun a gidan Inna binta ta samu tayi magriba tayi Isha'I da shafa'I da wuturi shi yasa tace masa haka, idan ma kudurin da ya dauka akanta babba ne to gara tun yanzu ta warware masa shi. Yana idar da sallah ya canza kayan jikinsa zuwa na bacci, ita ma ya mika mata rigar bacci a lede yace, ki canza kayan jikinki naga kamar za su dameki. Tace baza su dameni ba. Ganin bata da niyyar matsowa ya sa ya dau filo ya yi kwanciyarsa nan bisa carpet ya rufa da bargo abinsa yace, gara ki kwanta ni bacci nakeji. Tana zaune har 12pm da dai taga baccinsa yayi nisa sai ta lallaba ta kwanta. Cikin dare sosai taji mutum ya nannade ta ajikinsa, ya rufe su cikin bargo tayi kokarin ta zille masa amma ta kasa saboda irin nannadetan da yayi. Farkadda shi da tayi yasa ya shiga wasanni da ita nan da nan idanunta suka raina fata, yace ba kince kina fashin sallah ba? Ai babu abinda zanyi miki da ya wuce wannan. Haka nan yabi ya dameta har akayi kiran sallar subahi., sannan ya kyaleta. Gani bacci ya fara dibanta sai lallubeta ya wuce masallacin hotel din. Tana farkawa taji ana sallah sai tayi sauri ta shiga bayin ta yai alwala tayi raka'atul fajr sannan ta salllaci subahi. Ta na tsakar shafa addu'a ne ya shigo wai ita dole sauri take ta gama kafin ya dawo. Yana ganinta yace Allah ya kamaki, kinga karyar da kikayi mini ita zata sa inyi miki abinda nake so. Oya shafa addu'a ki zo nan ki sameni. Mukulli yasa ya