Sashe 6
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya kusa gama gugar ma da takeyi, ta tsaya sororo. tana kallonsa yayi kamar bai san shi take kallo ba ai jo tayi yace,kin sa fa ni bawanki zan zama idan mukai aure, shiyasa ma tun yanzun zan fara bauta miki, ke er hutuce Tace tym din sallah yayi a gara kaje kayi, ya karasa goge wandon sannan Ya cire iron din ya mike tare da zuba mata ido, yace bari inje inyi sallah in dawo yau akwai latest labari ko ba kya son ji? tace idan na alheri ne ina so amma idan na yan matanka ne jami'a akara gaba da shi. Dariya ya kama yi sosai har da rike ciki ita kam kallonsa kawai takeyi, sai daya gama sannan yace, Ni wlh ban taba sani ana sona haka ba har da kishina, lallai zan zo in kama kaina kada tsautsayi ya sa a ga ina magana da wata ayi min bulala. Ficewa yayi ita kam ta bishi da harara tana cewa, kishi? lallai ashe zan wahala idan akanka zanyi kishi wanda yan matan jami'a ke rububi. Juyowa yayi yana gab da ficewa yace bari in dawo kema zan gaya miki yadda ake ta rububi akanki. Kafin ya dawo tayi sallah ta shirya cikin doguwar riga ta zauna tana cin abinci sannan ya dawo ta na ganin ya shigo tayi sauri mikewa taje ta kawo masa nasa, don tasan yana iya saka hannu yace sai sunci tare. Ita kanta yanzun a tsorace take saboda dan yinin da ya shigo yayi yayarsa tana iya jin haushi ko kaji wani zance ya fito. Gaba dayansu da yara suna tsakar gida ne sukaji sallamar mama tana ganinsa da fara'a tace aka sagir yau kaine a gidan? Ya risina da fara'a ya gaisheta. Yara kuma suka rungumeta suna mata oyoyo ita Aneesa ta isa ta amshi jaka mama tare da yi mata sannu da zuwa, dukansu daki suka bi Maman har da Aneesa suka bar sagir ya kelo yace, Mama ni zan wuce, tace au zaka tafi to ka gaida gida da su goggon da Hajiya. Aneesa ta danyi jim sannan ta biyo shi tsakar gidan sukayi sallama ya tafi. A daki mama take shaida mata yadda ya kasance a sibitin, tayi hoto sun tabbatar yanzun komai lfy tunda sungyara yaron kwanciya. Aneesa tayi murna da jin haka don bata son Mama ta samu matsala ko kadan. Aneesa sun fara shirye shiryen zana xams dinsu ta JSSce hakan ne ya sa ta zage damtse gurin karatu da bada himma zuwa wajen sch saboda dama ita mai himma cema shi yasa duk wani kuskure da zatayi mata sanadin hanata zuwa sch. Gashi a tym din cikin Mamanta ya tsufa, dole suka raba aikin gidan ita da Aysja ba don ayshan ya so ba, duk da dai itama ai wannan tym din tana tausayawa Maman wahala da take ciki. Ranar talata Aneesa ta dawo sch daidai gidan Hajiya ta hango motar Ishaq, kamar ta shiga ta gaishe shi, sai dai ta wuce abinta, don ta san in dai ba sauri yake ba zai shigo gaida Mama balle yadda ya san bata cika lfy ba shiyasa ko waya yayi sai ya tambayi lfiyarta, har kude ya aje musamman gurin Hajiyarsu wai da mama ta fara nakuda ayi maza direban Hajiya ya kaita asibiti don baya son ta haihi a gida kada asami matsala. Zata shiga gidansu kenan sukayi kicibis da diyar yayar Ishaq din. sukayi wa juna murmushi Aneesa tace kamar fa in shiga gidan Hajiya da naga motar Yaya sai dai na wuce$ Tace kuma shi ya aiko in kira ki Mama tace kina sch, amma ta san kina hanya. Aneesa taka hannunta mu koma ciki in cire Uniform dina sai muje. in kaji kira samu ne balle kirian irin na manya masu keta hazo kullum. Suka fashe dariya. Doguwar riga kawai ta saka da hijab ta so taci abinci sadiya ta hana wai taci a gidan ay,Alh ytiakt tayi sallah asch. A harabar gidan suka hangeshi yana ganawa da dafifn mutane, dattijai da matasa masu son ganin wanda duk xuwa sai yayi da gaske yake kwatar kansa a gurinsu, shima sai in sallah aka kira amma duk sai ya sallami kowa da bukatarsa da ya zo da ita, sannan yake shiga cikin gida, shi yasa matarsa bata bari suyi masauki a gidansu da hade dana Hajiya, sai dai su sauka ahotel. Amma idan shi kdai ne nan sashensa yake kwana, yafi son ga shi ga Hajiyarsa. Allah yayi Ishaq mai jama'a tun yana yaro. Kitchen din Hajiya Aneesa ta nufa ta shige ta debo abinci a plate sannan ta shiga falon, ta iske su zaune. Hajiya na ganin ta da palte a hannu tayi dariya taceN Hala dawowarki kenan taje ta taso ki agaba? Tace da kyar ta barni na cire uniform, ta hanani cin abinci wai yaya ishaq na kira na, kila kudi zai raba mana, ta bi ta dameni in taho yanzun. Hajiya tace kinji kyale wannan 'yar wautar cikinki ya dauka, In bakuyi sa'a ba kafin ya shigo gidan nan sai an kusa magriba. Aneesa tace, ina ce yau zai koma naga ranar aiki ce gobe. Hajiya tace wani wani taro suka zo aviation nasu na matuka jirgin sama, gobe da safe ne taron a goben zai koma, Yanxun ma da aviation din zai tafi to jama'a sun hana shi tafiya. Aneesa tace ni na rasa yadda suke sanin Yaya ya shigo garin nan, kuma kowa ba zai zo haka ya tafi ba. Allah ya karawa Yaya budi, Hajiya tace ameen, to in bai taimakwa wanda baya da shi ba , yayi me? wanda ka bayar shine rabonka na lahira, wanda kaci kayi kiba idan ka mutu tsutsa ta burge shi, idan ma baka ci ba ka tara ma 'ya'ya da jikoki duk hakan take, y3ana ma Allah ya baka na kwarai ne za suyi maka ddu'a, shi ya sa nake ba shi kwarin guiwar ya taimakawa kowa ba 'yan uwa kadai ba. Yamma tayi sosai sannan Ishaq ya shigo gidan. Ya dubi Aneesa yace, Aneesa yaushe kika shigo, tun dazun nace sadiya ta kiraki. tace Yaya tun tym na shigo dan kana waje da jama'a ne, Kazo lfy? Ya su Suhail? Yayi murmushi suna nan fly kullum suna damuna wai su zaria wurin Hajiya ko suce Auntyn Zaria, sun ganeki sosai Yaran nan. Tace Allah sarki Yaya yaushe zaka kawo su? Yace ba su ne za su zo ba, kune zan turo driver ya dauke ku ke da Sadiya, kuna gama jarabawa kuje can kuyi mana hutu, suka kalli juna da Aneesa da sadiya su kayi murmushi, saboda duniya babu gidan da suke xuwan irin gidansa sannan babu yaran da suke so tamkar su lashe irin yaransa don Aneesa tym din suna jarirai har lasar Kyan kafafunsu takeyi ta tsotsi Jajayen labbansu, ita dai jinsu take tamkar ta su. ) Ya dubi Hajiya yace, Hajiya kinji ni shiru ko? ina gurin jama'a. Me zan samu inci anjima idan na dawo sallah? tace ban san me kake so ba, amma anyi birabuskon shinkafa miyar ganye ko tuwo kake so? Yace ayi min tuwon semo sai in ci da miyar, Yamma tayi da anyi min kubewa danya. Hajiya tace da ka sani ka gaya min a waya ko ka aiko amma, yanzun ladidi ta gaji sosai tun rana take tsaye a kicin$ Aneesa tace Yaya in yi maka girkin? N iya miya mai dadi har da tuwon, wanda kaci rannan a dakin Mama ma ni nayi shi fa. Yayi murmushi yace Kai Aneesa ni kam ban taba jin labarin kin iya girki ba, nasan dai kin iya wainar flour da shasshaka da meye ma dayan? Tayi saurin cewa Allah da gaske nake na iya girki ka tambayi Hajiya ma ko ita ina mata, kuma yayi dadi. Ya juya gun Hajiya dake sauraronsu tana mursmushi, Hajiya wai da gaske 'yarki ta iya girki? Kada tayi min in kasa ci ta sani neman restaurant a daren nan. Hajiya tace don iya girki 'ya ta iya, amma tun da ka fara ko kwanto to ba zan yarda ta yi maka ba don kada yau hannunta yayi gardama, kace dama bata iya ba. Yayi Murmushi yace, dama kawai bata iya ba, amma bari tayi min ai daga gwadawa jirgin sama ya tashi. duk sukayi dariya. Aneesa da murnarta ta nufi kicin saboda Allah yayi ta mai son girki ce, shi yasa a duk tym din da ta shigo gidan Hajiya bata da tashar kallon sai ta girke2, kuma duk abinda ta gani sai shiga kitchen din Hajiya ta gwada, don ta san Mamansu ba zata juri wannan shirmen ba, a cewar hajiyace mai bata dama tayi duk abinda take so, ko da babu abun girkin yanzun zata tada driver ko ladidi ta aike su su siyo. MIJIN ARO 1**6 28). Ishaq Yayi mamakin Yadda Aneesa har ta iya girki haka, don da ya ci tuwon cewa yayi Hajiya ta yi, Tayi murmushi tace kai ka san bana shiga kicin balle in yi, itan dai da ka raina iyawar ta ita tayi gashi har kana side hannu. Kafin ya bar zaria sai da ya shiga gidansu Aneesa ya sami Abban Aneesa ya nemi alfarmar tafiyarsu abuja hutu, Abban yace ba damuwa, gidansa ai tamkar gidan hajiya ne. Washe garin ranar da su Aneesa suka gama xams din su ne ishaq Ya turo driver ya tafi da su. Sau daya suka taba zuwa gidansa tun tym din haihuwar su Sultan shekaru 3 kenan sai, suka ga komai a gidan ya canza tamkar ba gidan da suka taba zuwa ba, gidan ya zama tamkar yaune aka bare shi a leda. saboda sabunta da kyalkyali, abinka ga gidan 'yan gayu. Kasancewar ranar asabar ne a gidan suka iske masu gidan suna falo su Suhail sun baza motacin da jiragen su suna wasa, Ihu da tsalle yaran da sukayi suka yo kan Aneesa dukansu, saboda ita suka fi sabawa da ita fiye da sadiya, kasancewar duk zuwan da za suyi zaria ko ba su iske Aneesa a gidan Hajiya ba, babansu yana shiga da su gidansu. Ita kuwa sadiya yawancin idan sunje basa ganinta tunda boardin takeyi. Kowa ya kwakwumeta sai ta dauke shu, da su biyun ta hada ta dauka,