Sashe 49
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
mai dogon wando ya shigo da saurinsa don yasan ba lfy ba tunda yanzu ne ya bar gurinsu. Hajiya ta gaya masa asibiti za'aje Aneesa nakuda takeyi, ai bai jira an kira driver ba, shine ya tuka su ya kai su asibitin (PAL HOSPITAL) dake PZ dama anan ta cigaba da awonta. Suna zuwa aka wuce da ita dakin haihuwa su kuma su Hajiya suka zauna a reception dinsu suna jiran tsammani, tare da addu'o'I a bakunansu, suna rokon Allah ya sauke ta lfy. Cikin ikon Allah ba su wuce awa daya da rabi ba Allah ya sauketa lfy ta haifo en 2 lafiyayyu. Nurses din asibitin suka fito suka gaywa su Hajiya sannan suka ce a basu kayan sawan jariran. Ishaq ya tashi da sauri yaje ya dauko a ckin mota, cike yake da murna wannan karon ma Allah ya kuma yi masa baiwa da haihuwar en 2 har sau 3. Safeena tace ita ta gama haihuwa har tana saana juya mata mahaifa ba tare da saninsa ba, saboda tana ganin ita 'ya'ya hudu sun isheta a rayuwa ta manta akwai mutuwa sai gashi mutuwa ta rabata da en 2 kuma mazan da take tinkaho da su, shima da take ganin ta riga ta mallake shi ba zaiyi aure ba, yayi aurensa yau ga matar ta haifi masa en 2, haihuwa kuma yanzu aneesa ta fara a gidansa, ita kuma ta cuci kanta gashi nan tun aduniya ta soma ganin ishara. Amma idan suka barta anan ta daki matarsa wani abu ya faru da ita zai dauki mataki a kai gara tun wuri suyi shawar abinyi tun kafin ta aiwatar da abinda kullum take furtawa. Suma iyayen Safeena abin nata ya ishesu balle da aka zo aka gaya mata halin da aminiyarta take ciki ta sami mutuwar barin jiki bata iya ko da tashi ne komai sai dai ayi mata, a tym din da yake asibiti ma wai mijin na Haj. Nuratun aure zaiyi, habawa sai safeena ta dada haukacewa tana sirafwa Alh. Zagi tamkar ya gurin, su kansu masu bata labarin abin nata ya basu tsoro. A ciki wannan iyayen safeen suka koma da ita gida, amma su Yusra anan aka barsu saboda ga Hajiya, ita kanta Hajiya ta sami kusan wata biyu a buja, sai da taga Aneesa ta sami lfy sosai hankalinta ya kwanta ga cikinta yayi girma sosai tana zuwa sch, sannan suka barta ta koma zaria.********* ************************************** da kyar da jibin goshi Ishaq ya yarda Hajiya ta matsa ya maida mata Aneesa gidanta haihuwa, shi a cewarsa sai dai Hajiya ta dawo Abuja ta zauna, ita kuma tace ba zata dawo ba kuma Aneesa ba zata zauna ba tunda babu wani mai kula da ita a abuja. Tafiya ma Aneesa da kyar takeyi, saboda girman cikinta, balle cike ne na en biyu. Shi kuma Ishaq ya kallafa rai akan cikin nan tamkar yanzun za'a yo masa haihuwar fari balle da aka yi hoto akace duka en maza ne sai yana ganin tamkar Allah zai dawo masa da su Suhail ne da ya rasa, yara masu kama da shi gashi sun shhi ranshi kamar me. Tunda ya kawo Aneesa ya kasance duk sati yana zaria, tunda can gidan nasa ma ba kowa har yanzu safeena tana gidansu, su Yusea ma tare da su ya akwo Aneesan zaria, Allah ya sa atym en sun sami long vacation a sch sai hakan yayi masa dai2. 132) (To mata masu irin halin safeena wannan ya zama kalubale a gareku. Da masu ganin yara kaza sun ishesu a dunuya to kada su manta akwai mutuwa suna iya rasa yaran duka, su kuma masu ganin sun mallake miji ba zai sake aure ba kada su manta Allah yana iya karya kadarinsa tamkar yadda ya karya na safeena, shi yasa duk abinda zaka yi ka saka tsoron Allah tare da addu'ar Allah ya kare ka daga sharrin zuciya ya zabar maka duk abin da zai zamo alheri a rayuwarka, don wani abin kana tsananin sonsa to ba alheri a arayuwarka, wani abin kuma baka sonsa amma baka sani ba shine mafi alheri a rayuwarka, Allah ka kare mu, ka kiyaye mu da aikin da na sni, ameen). Ana gama shirya yaran aka fitiwa da hajiyasu, suka mikawa Ishaq daya itama suka mika mata daya, ta dube shu cike da murna tace, waje hassana cikinsu? Nurse din tace ai shi na mika miki, naki mijin kenan, wannan kuma ya nemi tashi matar a gida kin ganshi rago ne tunda ya zo duniya yake kuka. Sukayi dariya da yake nurse din bahaushiya ce. Ishaq baki har kunne ya matso yana leka yaron hannun Hajiya yace, kin gansu kamar su suhail, Allah mai kyauta da kari, tamkar hotuna na ina jaririri. Ita dai Hajuya addu'a takeyi tana tofawa yaron, shi ma sai yayi wa hannunsa, sannan suka musanya yaran tayi wa dayanshi ma yayi wa hussain don hajiya tace babu canjin suna, sunaan da suka zo da shi za'a kira su. 133) Sai misalin 12:30 Ishaq ya bar asibitin nan da kyar, sai da ya shiga yaga Aneesa bayan sun gyarata sun canza mata daki, da sassafe da kanshi ya shiga gidansu aneesa ya gayawa abbanta, su aisha kannenta sai tsallen murna sukeyi, sukace zasu bishi suga jariran, yace su bari ai da safen nan likita zai sallameta idan ta dawo sai su shigo su ganta. Da aysha kawai ya tafi da zai kaiwa su Hajiyan abinci da ruwan zafi. 'Ya'yan suna dakin da Aneesa ake agado daya aka kwantar da su abin sha'awa. Ishaq ya dauki daya ya rungume sam ba ya gajiya da kallon yaran kyawawa masu tsananin kama da juna, Allah yasa dayan na da digon tawada a gajen hancinsa, da zasu yi wuyar banbancewa. Likita na zuwa ya dudduba su ita da yaran ya tabbatar da lfyarsu, sannan ya basu sallama suka dawo gida. A yadda ya tsara Umman tudun wada(kakar aneesa) itace zata zo ta zauna don yiwa Aneesa wanka da kula da ita, Hajiya kuma tayiwa jarirai wanka, sai ladidi zata dinga sa ruwan wanka, amma da su Halima suka shigo matan baban sasa, sai Halima tace Umma tayi zamanta ya za'ayi suna raye kuma ga baki ga hanci su kasa xuwa yiwa Aneesa wanka, ita kam kullum zata shigo da safe da yamma tayi mata wanka, hanne ma da taji haka tunda yanzun Aneesa na auren maikudi ana lasa musu abin arziki sai tace ita zata dinga yiwa yaran, don dai Hajiya ba yadda zatayi ne, amma bata so Hanne tayiwa jikokinta wanka ba, yadda bata kaunar uwarsu kada wata rana ta shaka musu sabulu su mutu don taga halin imaninta ragagge ne. Ranar suna raguna 4 Ishaq ya yankawa yaransa kowa 2 manyan rahunwa kosassu. Mai jego ta shiga ta fita cikin tsadaaddun kaya saboda Ishaq saitin akwatuna yayi mata shakare da kaya, suma yaran kowa saiti abu tamkar barin iska, ita ma Hajiya settin akwati tayi wa Aneesa da yaran, daga gidansu Aneesa ma dangin uwarta da na ubanta sunyi rawar gani, kayan shakare suka kawo. Abban Aneesa ya bada garar abinci ta ban mamaki, dama yana da wannan burin tunda biki Hajiya ta hana shi yin komai shi yasa yanzun ya sayaawa ersa mutunci, ya aiko da buhunan kayan abinci, da jarkokin man gyada da manja da sauransu. Da aka nunawa Aneesa taji dadi sosai tunda bata taba zatan haka ba.