Sashe 24
Mijin Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace yanzun kina ina ne? Tace ina kicin din Hajiya ina dafa maka ruwan tea. Yace yauwa idan kin gama ki sa a flask ki kawo mini ina nan bangarena. Ta sauke ajiyar zuciya a tsorace tace, bazan iya zuwa ba, Hajiya cewa tayi idan na gama in nemi imrana ya kawo maka. Yace, kin manta yanzun ke matata ce? Ai kinga da can ban taba cewa ki kawo min wani abu nan ba, sai dai in ce ki aiko da shi, yanzun kuwa matata ce ke, ni ke da iko da ke. Har yanzun a tsorace take, kirjinta sai bugawa yake yi ganin haka kurum yau daga daura aure zai ce ta kawo masa abu bangarensa don dai ya sa ta dauki zunubi, sannan idan taje ga idanun en biki ace tun ba a kaita ba har ta fara kai kanta gurin miji. Sai tace, nasan kai ke da iko da ni yanzu amma kayi hkr tunda ba'a riga an kawoni ba, yanzu akwai idanun en biki basu watse ba, gaskiyya ina jin kunya, ga al'ada za'a ce nayi ba dai2 ba, amma ga addini na karanta na amsa kiranka shine dai2, kayi hkr ka yafeni yau kawai kaji? Ya danyi murmushi yace, nayi hkr ki ba Imrana ya kawo min. Ki dan soya min kwai kwada ya soyu, kin dai gane yadda nake so? Tace na gane, mu kwana lfya. Da ta kammala da kicin tana shiga Hajiya tace tasa lullubi a rakata gidan babanninta sun aiko ta zo za'ayi maya fada sai a dawo da ita gidan Hajiyan, tunda nan ne inda za'a fara kawo ta kafin a wauce da ita Abuja. Iyayenta maza da mata sunyi mata fada sosai, sannan aka kawota gidan hajiya. 16) Washegri da sassafe Ishaq ya kebe da Hajiya ya gaya mata matsalar da yake ciki da safeena na furincin ta na cewa sai dai ya bar Aneesa a zaria in ba haka ba idan ya kawota da shi da Aneesan ba za su sami kwanciyar hankali ba. Shine ya shaidawa Hajiya yanzun haka gida yake nemarwa Aneesa a Abuja da ya samu zai zo ya dauketa su tafi. Amma yanzun ta zauna tare Hajiyan. Haka en biki suka watse ba tare da an kai marya ba, Hajiya ta gaya musu Ishaq yace shine zai wuce da ita da kansa, duk mai son zuwa ya bari daga baya sai yaje, Aneesa kam! Abubuwan sun daure mata kai. Amma tunda Hajiya bata yi mata cikakken bayani akan abin da ya sa ba'a kaita abuja ba, itama sai tayi shiru, dama ita da son ranta ne tafi son ya gyara mata gurin anan gidan Hajiyan tayi zamanta, ko dama a falon Hajiya ne idan ta ware mata daki tace ta zauna tafi son haka akn zuwanta Abuja. Don bata son mai zata je ta tarar ba, saboda farin sanin da tayi wa safeena akan akidarta na rashin son kishiya ko da bata tata ce ba, balle kuma tatan. Da kunneta taji tana gaywa kawarta zata iya kashe kishiya idan akayi mata sai dai itama a akashe ta, ita kam, tana tsoron wannan furucin ko lfiyarta bata kaunar a taba balle a rayuwarta ita kam, ko zamata zariya yayi mata dadi. Tunda tayi wanka da safe tayi kwaliyyarta, sai kawai ta shiga dakin Hajiya ta haye gado tayi kwanciyarta bcci yayi awon gaba da ita. Shigowa Ishaq sau biyu tana baccinta bata sani ba, ya bi ya kura mata idanu saboda tayi masa kyau sosai, daga shigar da tayi har zuwa fuskarya wadda tayi haske sosai, babu komai a fuskar sumul bako dingon kurji, hoda ce kawai sai yaji tamkar ya lashe su daganinsu zasuyi dadi idan aka sumbace su, saboda ma'abotan taushi ne. Yayi saurin ficewa a dakin saboda zuciyarsa da ta soma harbawa. 17) Shigowa na uku, ya iske Hajiya a dakin, itama, duk tana lura da sintirin da yakeyi, Ya dubi Aneesa ya dubi Hajiya yace, yarinyar nan kuwa tayi brkfst kafin ta kwanta? Naga tun safe take bacci gashi har wajen 12pm? Tace ya za'ayi na barta bata karya ba ta kwanta, sai da tasha tea sannan ta kwanta. Ya sake cewa, Anya lfiyarta lau kuwa, baccin nan ai ya isa haka, tace haba Ishaq Yarinyar nan idan ta tashi mai zata maka wai? To ba mai tashinta sai an kira sallahr azhar shima wannan dan ya zama dole ne, irin gajiyar da tayi, ai dole ne tayi barci ma ishi. Tym din da ya dawo sallar azhar a falo ya iske Hajiya da ragowar baki, ya gaidasu sannan yace Hajiya zan sami maltina a fridge dinki kuwa? (Kuji fah wani zance, hahahaha Ishaq sannu.....) Tace akwai mana, jiya Aneesa tasa, yayi saurin isa dakin dan dama abinda yake nema kenan, ya rasa hanya yadda zai shiga kai tsaye ne za'a ce matarsa zai bi, tunda yasan tana cikin dakin. Shi yasa ya fake da neman maltina. Shi kam haka kurum tun jiya da aka daura auren ya ji ba ya gajiya da kallon surarta da fuskarta yana sin su zauna suna hira, shi fa komai nata birge shi yakeyi. Bisa capet ta sameta da flate din abinci agabanta, tana ci nan da nan gabanta ya zauna yace, sarkin barci kin tashi? Na shigo dakin nan yafi a kirga kina ta barci, lallai ke er gatan Hajiya ce, kina tashi kuma an kawo miki abinci ki ci ki sake kwanciya, Hajiya zata sa kiyi kiba, dubi naman da ake zuba miki a abinci ga Maltina, da dare kuma hajiya ta koya miki shan fura duk kiba suke sawa, ni kuma bana son mace mai kiba cikawa mutum gaban mota takeyi him... Idan kika yarda kikayi kiba, Allah idan zamu unguwa a seat din baya zaki dinga zama, safeena ma na yi mata warnin idan bata ragu ba, ta daina shiga gaban motata. Aneesa tayi dan murmushi tace, amma naga kaima kana shan furan nan da Maltina din kuma kana cin Nama sosai, Ya akayi baka yi kiba sosai ba? Yace, ina shan fura da rana, ku kuma da dare kuke sha sai ku kwanta, shiyasa zakuyi kiba, sannan ni Abuja duk weekend ina zuwa training, sannan inayin exercise, kullum da safe, don daki guda na ware na zuba kayan motsa jiki, kinga ai na shirya, fatata duk wani kitse da zai kwanta mini a jiki ya sani kiba. 18) Ku kuwa fa? Ba kwayin komi. Kullum kuna jibge sai dai kuci mai maiko ku kwanta ko Nama ne, mai kitse kuka fi so, ku debi kakiden kitse ku sa a abinci, ku ci, ba dole kyi kiba ba. Tace, Ni Allah bana son kibar bazan bari nayi ba, zan kiyaye wadannan abubuwan da kafada. Kada in wayi gari inji kayana sun gagare ni sawa. Yace da kin kyauta min kuwa. Ya sa cokalin da take ci. Ya dauki yankan nama daya a cikin abincinta yaci, yace nashiga falo naga an kai min abinci gaskiyya ba zanci shinkafa da miya ba. Ki shiga ki soya min chips idan kuna da nikakkiyyar gyada kiyi min kunu ya isheni har dare. Idan kin gama ki kawo min da kanki ba aike ba, ina so muyi hira ne don ina jin gobe zan wuce Abuja insha Allah zan dawo juma'a, ko asabar, kafin nan idan an sami gidan da nake neman miki sai mu wuce, nafi son kowa tana gidanta bana son fitina ni ma kuma hankalina zaifi kwanciya da hakan. Ya mike yace bari inje in dan kwanta ina jiranki. Idan kin gama. Tace kada kasa ran zuwana don kila Hajiya zata ce in bada akwao maka ne. Ni kuma bana son aga zakewata gurinka. Yace in dai Hajiya ce bata barinki zuwa gurin to ki shirya yau ma a can zata ce kije ki tayani kwana. Ta bude baki tana mamaki. Hajiyar ce zata ce haka? Lallai baka san Hajiya ba, ni ko tace inje ma ta san ba iya zuwa zanyi ba. Balle ma ba zatace ba. Yace au kinga ashe ba ita bace matsalat kema da matsalarki, wai ni yayanki da kike ji da shine yanzun ake guduna, kamar wani dodo, ba ke ba Hajiyar taki. Ita dai Aneesa shiru tayi har ya fice a dakin. 19) Hajiya na shigowa dakin ta gaya mata abin da yace tayi masa sannan ta wuce kicin din. Cikin kankanin tyn ta kammala masa duk abin ya bukata. Tana shirya kayan akan rire kenan Hajiya ta sameta a kicin din, sai tayi saurin cewa Hajiya, Ga abincin yaya Ishaq din wa zai kai masa? Tace ke yace ki kai masa, yanzu ya bugo min waya har da rokona wai dan Allah in kyaleki ki kawo masa, hira zaki taya shi, kuma yana son kuyi wasu maganganu da suka shafe ku, don gobe zai wuce Abuja. Kije ki kai masa ba zan hanaki ba tunda mijinki ne, amma ki sani ko da kiga ina kaffa2 dake. Ba komai nake gudu ba sai abinda zaije ya dawo, kinga yanzun kiri2 matarsa ta hana a kaiki gidansa. Shima saboda yana gudun rigima ya bi ra'ayinta, naji an amince kada akai ki can amma dole ya nema miki gida a can ya tafi da ke, don ba zai yiwu ba ya barki a nan, yayi tafiyarsa sai tym din da taga dama ta barshi ya zo ya ganki, shi yasa zan gaya miki duk wayonsa kada ki yarda ki bashi kanki, sai ya nema miki gida ya tafi da ke, idan ba haka ba, muddin kika sake ya barki da ciki a nan ya tafi can kyaleki zaiyi, kuma ke kika sani, ya barki da laulayi ni kuma ina jinya, shikenan haka zai bagarar da ke anan yana can da rabin ransa, don namiji idan ya nemi abu a gurin mace ya samu shikenan ya gama da ita, balle idan ta sami ciki, shi yasa nake son mu bari mu ga kamun ludayinsa in ya kama ki zauna anna ne sai agyara miki wancan flat din ki tare shi da ita kuma su ruke wannan da yake ciki. Amma ki bari mu kwatar miki enci don na fi son zaman ki a kusa da shi. Bari in kira sadiya yanzun ta shigo sai ta tayaki daukar wani abun, kin